Aminiya:
2025-08-13@19:22:25 GMT

Monaco ta dauki Paul Pogba

Published: 29th, June 2025 GMT

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Monaco ta ƙulla yarjejeniyar kaka biyu da tsohon ɗan wasan Manchester United da kuma Juventus, Paul Pogba.

Pogba mai shekara 32 ya koma a matakin wanda bai da kwantiragi tun daga watan Nuwamba, bayan da Juventus ta soke yarjejeniyar da ke tsakaninsu.

Nijeriya ce kasa ta 12 mafi talauci a duniya — IMF Yadda na hannun daman ’Yar’Adua ya yi tuggun hana ni zama shugaban ƙasa — Jonathan 

A watan Maris ɗin bara ne aka dakatar da Pogba shekara huɗu, sakamakon zargin shan abubuwan ƙara kuzarin jiki.

Amma yanzu zai koma taka leda bayan da aka rage hukuncin zuwa wata, sakamakon ɗaukaka kara a watan Oktoba.

Ya fara taka leda a Manchester United daga nan ya koma Juventus a 2012.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda ɗan shekara 70 ya rasu a gobarar tankokin gas a Zariya

Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna.

Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin.

Dattijon ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa na zuwa gona, lokacin da wasu tankokin dakon gas biyu suka kama da wuta bayan su gogi juna.

Mai auran babban ’yar marigayi Malam Abdullahi Magaji, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, akan rasuwar marigayin.

ya ce, “A jiya da safe marigayin yana kan babur ne a kan hanyarsa na zuwa gona, sai waɗannan motocin ɗakon man gas ɗin suka kama da wuta kuma suka yi ƙara.

“To a lokacin da yake ƙokarin tsira da rai ne wani shi ma da yake kan babur garin gudu sai ya kwashe shi a inda kafin a kai shi asibitin ya rasu,” in ji shi.

Marigayi ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya shida kuma tuni aka yi jana’izarsa a gidansa da ke Babbale cikin birnin Zariya.

Bayanai na ƙara fitowa dangane da wadanda suka rasu a sanadiyar hatsarin tankokin dakon gas ɗin da ya auku a garin Zariya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Iraki Ta Ce: Yarjejeniyar Da Ta Kulla Da Iran Zai Amfani Dukkan Kasashen Yankin
  • An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe
  • Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
  • An kama ɗan shekara 18 kan zargin fashi da makami a Gombe
  • Yadda ɗan shekara 70 ya rasu a gobarar tankokin gas a Zariya
  • Iran da Iraki sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro
  • Masar ta yi gargadin cewa a shirye take ta dauki duk wani mataki na kare muradunta
  • Sashen Masana’antun Kirar Motoci Na kasar Sin Ya Samu Gi Gaba A Watan Yuli
  • Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe
  • Ƴansanda Sun Kama Makashin Wani Ɗan Jarida A Abuja Bayan Shekara Ɗaya