HausaTv:
2025-07-02@02:44:32 GMT

An Kashe Kusan Mutane 1500 Kan Sabanin Mazhaba A Kasar Siriya A Wata Guda

Published: 1st, July 2025 GMT

Mummunan kisan kiyashi kan ‘yan darikar Alawiyyan Siriya, kuma wadanda aka yi wa kisan gilla a kasar a watan Maris sun kai mutane 1,479

A cikin binciken da ya yi na baya-bayan nan, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cikakkun bayanai na kisan gillar da aka yi tsakanin ranakun 7 zuwa 9 ga watan Maris din wannan shekara ta 2025, inda aka kai wa ‘yan darikar Alawiyya hare-hare a yankin gabar tekun Siriya.

Binciken ya tabbatar da mutuwar Alawiyawa 1,479 da bacewar wasu da dama a wurare daban-daban guda 40, lamarin da ke nuni da karuwar tashe-tashen hankula da daukar fansa kan tsirarun mabiya mazhabobin Musulunci a kasar ta Siriya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya wallafa binciken nasa ne bisa shaidar fiye da iyalai 200 da abin ya shafa, da kuma hirarraki da jami’an tsaro 40 da mayakan da kuma shugabannin yankin.

Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton mutuwar mutane 111, inda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar da cewa adadin ya fi haka. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syrian Network for Human Rights ta watsa rahoton cewa, an kashe mutane 1,334, da suka hada da yara 60 da mata 84, kuma dakarun gwamnati ne ke da alhakin mutuwar mutane 889.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 22 ga watan Yulin wannan shekara domin sauraron bukatar ba da belin da Tukur Mamu, da ake zargi da daukar nauyin ta’addanci Mai shari’a Mohammed Umar ya tsayar da ranar ne biyo bayan dage shari’ar da lauyan Manu, Johnson Usman, SAN, ya nema, domin ba shi damar yin nazari tare da ba da amsa da ya dace kan karar da lauyan gwamnatin tarayya, David Kaswe ya shigar a kansa. A cikin bukatar da Mamu ya gabatar a jiya Litinin 30 ga watan Mayu, ya nemi a bayar da belinsa dsaboda yanayin rashin lafiyarsa. Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya Ya nemi Gwamnatin Tarayya ta ba shi izini a kai shi asibiti don yin aikin tiyata kamar yadda likitoci a kasar Masar da na Najeriya suka ba da shawarar. Tun a ranar 21 ga Maris na shekarar 2023 ne dai gwamnatin tarayya ta gurfanar da Mamu a gaban kuliya bisa zarginsa da taimakawa ta’addanci a kasar nan. Ana masa tuhume-tuhume guda 10 da ke da alaka da ta’addanci amma ya musanta duka zarge-zargen.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Malaman Sunna A Kasar Iran Sun Bayyana Gwagwarmaya Da HKI Wajibi Ne A Sharia
  • Kotu za ta duba yiwuwar ba da belin Tukur Mamu a ranar 22 ga watan Yuli
  • NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya
  • Togo: An Kashe Mutane 7 A Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
  • An Kashe ‘Yan Kungiyar Shabab 19  A Kasar Somaliya
  • Sin Ta Yi Watsi Da Bangaren Rahoton SAGO Mai Nasaba Da Binciken Tushen Cutar COVID-19
  • Lebanon Ta Nuna Damuwarta Da Yiyuwar Yan Ta’adda Daga Siriya Su Kawo Hare-Hare Cikin Kasar
  • Babbar Mota Ta Afka Cikin Kasuwa A Taraba, Mutane Da Yawa Sun Mutu
  • Kalibof Ya Mayarwa Shugaban Kasar Amurka Martani Kan Mummunan Kalamansa