Faransa Tace Za’a Maida Takunkuman Tattalin Arziki Kan Kasar Iran Idan Taki Yarda Da Yarjeniyar da Trump Yake
Published: 29th, June 2025 GMT
Gwamnatin kasar Faransa ta nawa JMI barazana kan cewa idan bata amince da yarjeniyan da Amurka take so ba to za’a sake dawo da takunkuman MDD a kanta.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Noel Barrot yana fadar haka, ya kuma kara da cewa idan Iran ta ki ta rattaba hannu kan yarjeniyar da gwamnatin shugaba Trump yake so kan shirinta na makamashin Nukliya ba, abinda muke buklata kawai shi ne mu aika da wasika kan a dawoda takunkuman tattalin arziki kan kasar Iran, wadanda suka hada da na makamai, kudade, da kuma fasaha wadanda aka dagesu shekaru 10 da suka gabata.
Bayanda Amurka ta fice daga yarjeniyar JCPOA a shekara 2018 kasashen turai Faransa Burtaniya da Jamus suma sun ki su cika alkawulanda suka hau kansu a yarjeniyar donn goyon bayan Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
PLA Ta Kori Jirgin Ruwan Yakin Amurka Daga Yankin Ruwan Kasar Sin A Kusa Da Huangyan Dao
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp