2025-11-27@22:00:01 GMT
إجمالي نتائج البحث: 12
«sauraron jin ra ayoyin»:
Babban abin lura a nan shi ne irin alfanun da Nijeriya za ta samu tare da sauran kasashen Afrika daga wannan bikin baje koli. Na farko dai Nijeriya da sauran kasashen Afirka za su kara kaimi wajen noman irin waɗannan amfanin gona domin fitar da su zuwa Sin, hakan kuwa zai kara samar da aikin yi ga dubban ‘yan Nijeriya, abin da zai habaka kudaden shiga ga kasa. Alfanu na biyu kuma shi ne fadada damar ingantawa da kara daga darajar irin wadannan amfanin gona da Nijeriya ke samarwa. Sannan kuma akwai batun bunkasa dangantakar cinikayya tsakanin Sin da Nijeriya da ma sauran kasashen Afirka. Sabo da haka wannan irin lamari na bude kofar cudanya tsakanin Sin da sauran kasashen...
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da taron sauraron ra’ayoyi jama’a kan shirye-shiryen tsara kasafin kuɗin shekarar 2026 a wani yunƙuri na jaddada ƙudirinta na gudanar da mulki cikin gaskiya da haɗin kai. Da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Gwamnan Jihar, Dakta Manassah Daniel Jatau, ya bayyana cewa wannan mataki na nuna jajircewar Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya wajen tabbatar da cewa ra’ayoyin jama’a na taka muhimmiyar rawa a tsara kasafin kuɗi da aiwatar da shi. Za a rataye wanda ya kashe ɗan uwansa a Ekiti Gobara ta tashi a babban kanti a Abuja Ya ce tattaunawar ta bai wa gwamnati damar haɗa kai da sarakunan gargajiya, mata, matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki, domin bayar da...
Kungiyar gwagwarmyar ta Hamas ta yi maraba da matakin da kotun kasa da kasa ta ICJ ta dauka na karyata ikirarin da HkI ta yi kan hukumar bada agaji ga falsdinawa yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya . Gwamnatin Sahyuniya ta yi ikirarin karya kan hukumar ta UNRWA inda kafafen yada labarai na kasashen turai suka yayata ba tare da wani bincike ba kan gaskiyar lamarin, inda kotun ta ICJ ta majalisar dinkin duniya ta mayar da martani kan ikirarin karya da isra’ila ta yi kuma ta kare hukumar UNRWA ta bayyana irin ayyukan jinkai da take yi da gudanarwa ga alummar falasdinu. Babban kotun duniya ta umarci isra’ila da ta bada dama a shiga da kayayyakin agaji zuwa...
Kafafen watsa labarun HKI sun nakalto cewa kamfanin jirgin saman kasar Oman, wato “Oman Air” ya cire sunan Isra’ila daga cikin taswirarsa yam aye gurbinta da Falasdinu, domin nunawa domin abinda yake faruwa. Tashar talbijin din “almayadin’ ce ta nakalto labarin daga kafafen watsa labarun HKI akan matakin na kasar Oman. Ana ganin matakin na Oman a matsayin mayar da martani akan kisan kiyashin da HKI take tafkawa akan al’ummar Falasdinu, musamman a Gaza. A baya ma’aikatar harkokin wajen kasar Oman ta yi kira ga kasashen duniya da su yi aiki da nauyin da ya rataya a wuyansu, domin kawo karshen laifukan da HKI take tafkawa akan al’ummar Falasdinu, da kuma buke kafar da za a shigar da kayan abinci...
Jaridar Telegraph: Makaman Iran Masu Linzami Sun Sauka Kai Tsaye Akan Cibiyoyin Sojan Isra’ila Guda 5
A wani rahoton musamman da jaridar ” Telegraph” ta Birtaniya ta buga, ta amabci cewa; makamai masu linzami da Iran ta harba wa Isra’ila sun sauka kai tsaye akan wasu muhimman cibiyoyin soja. Jaridar ta kara da cewa; Mahukuntan Isra’ila ba su bayyana wa duniya wadannan wuraren da makamai masu linzamin su ka fadawa ba, saboda aiki da dokar soja ta Sakaye labaran wuraren da aka kai wa hare-hare. Rahoton jaridar ya ce, ya sami bayanai ne daga hotunan tauraron dan’adam na jamiar Jahar Oregon da suka saba yin aiki da irin wadannan bayana da suke tarawa domin gano barnar da aka yi a wuraren yaki. Rahoton ya ci gaba da cewa cibiyoyin sojan da Iran ta kai wa harin,...
A yau Asabar ne kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na lura da yanayin bala’u a doron kasa, wanda ake sa ran zai rika samar da bayanai ga kasar Sin dangane da aukuwar bala’u daga indallahi, ta aikewa da sakwanni tsakanin sararin samaniya zuwa doron duniya. An harba tauraron dan Adam din mai suna Zhangheng 1-02, ta amfani da rokar Long March-2D, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, da karfe 4 saura mintuna 4 agogon Beijing, ya kuma shiga da’irarsa ba tare da wata matsala ba, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta tabbatar. Kazalika, CNSA ta ce, wannan aiki muhimmin mataki ne...
Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya fitar da bayani a yau juma’a da a ciki ya yi wa ‘yan sahayoniya alkawalin fuskantar ukuba mai tsanani. Bayanin na jagora ya kunshi cewa: Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai Ya Ku Al’ummar Iran Masu Girma Da safiyar yau, ‘yan sahayoniya sun miko hannuwansu da suke jike da jini, domin tafka laifuka a cikin kasarmu. Sun kuma sake bayyana hakikanin dabi’arsu mummuna fiye da kowane lokaci a baya, su ka kai wa gidajen fararen hula hari. A dalilin haka, wannan haramtacciyar kasar ta saurari sakamako mai tsanani. Su kuma sani cewa; Sojojin Jamhuriyar musulunci masu karfi ba za su kyale su ba da yardar Allah....
MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida. Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39. Sanarwar ta MDD ta ci gaba...
A wani bangare na daban kuwa, dole ne ’yan siyasar Turai su yi tunani cewa, jama’arsu sun dauki irin wannan mataki ne ba ma kawai bisa bukatunsu na sayayya ba, har ma ya kasance mataki ne na nuna adawa da babakeren Amurka, da bukatunsu na dogaro da kansu a bangaren manyan tsare-tsare. Huldar Amurka da Turai ta wannan fuskar ta yi hannun riga da ainihin ma’anar zumunci, inda lamarin ya yi rauni matuka, kuma tabbas matukar Turai ba ta nemi dogaro da kanta ba, za ta yi asara daga barazana da kalubalen da Amurka take haifarwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin. Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na...
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa. Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20 da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...