An Kaddamar Da Aikin Hadin-Gwiwar Kafafen Yada Labaran Sin Da Kasashen Waje Wajen Watsa Labarai Game Da Jihar Xizang Ta Kasar Sin
Published: 29th, June 2025 GMT
Jiya Jumma’a 27 ga watan Yuni ne, aka kaddamar da wani aikin hadin-gwiwar kafafen yada labaran kasar Sin da kasashen waje daban-daban, mai taken “Ziyara a jihar Xizang don tunkarar zamanantarwa” dake karkashin jagorancin cibiyar watsa labarai ta harsunan Asiya da Afirka ta babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, da ofishin fadakar da al’umma na kwamitin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin reshen jihar Xizang mai cin gashin kai ta kasar, da gidan rediyo da talabijin na jihar, da kamfanin zirga-zirgar jiragen kasa na Qinghai-Xizang na kasar Sin, inda aka gayyaci manyan ’yan jaridu gami da shahararrun masu amfani da shafukan sada zumunta na intanet guda 20, don watsa labarai game da jihar ta Xizang.
A makwanni biyu masu zuwa, ’yan jaridun Sin da kasashen waje za su yi tattaki zuwa Lhasa, Xigaze, Nyingchi, da kuma Ngari dake jihar Xizang, don daukar shirye-shirye masu taken “ziyara a kasar Sin”, da zummar nuna manyan sauye-sauye da babban ci gaba da aka samu a jihar cikin shekaru 60 da suka gabata. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: jihar Xizang a kasar Sin
এছাড়াও পড়ুন:
Rashin Amincewa Da Kasashen Yamma Yana Haifar Da Sabon Tunani Kan Huldar Kasa Da Kasa
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau?
A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai a cikin babbar shawarar inganta jagorancin duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a watan jiya.
Yayin da ake kawo karshen tsohon zamanin da kasashen yammacin duniya ke taka rawa a matsayin masu ba da umarni a duniya, kasashe masu tasowa, ciki har da kasashen Afirka da kasar Sin, za su kara kawo ci gaba mai inganci, da adalci, da daidaito ga duniya, yayin da suke kokarin aiwatar da wasu sabbin tunani, gami da raya su a kai a kai. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA