Aminiya:
2025-07-03@20:58:53 GMT

’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar Tinubu – Amaechi

Published: 3rd, July 2025 GMT

Tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya ce wahalhalu sun yi yawa a Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, wanda har ya sa mutane suka fara fatan dawowar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Yayin da yake magana a birnin Abuja, Amaechi ya ce Najeriya ta taɓarɓare matuƙa, inda ya ce sauyin gwamnati ne kawai zai magance matsaloli.

Gwamnatin Yobe ta rufe kasuwanni 3 saboda matsalar tsaro Ɗan wasan Liverpool, Diogo Jota, ya mutu a hatsarin mota

“Farashi kayayyaki ya tashi sosai. Mutane ba za su iya siyan abinci ba. Babu kuɗi. Komai ya lalace,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa rayuwa ta yi tsanani har mutane sun fara tunawa da zamanin Buhari da muradin dawowarsa kan mulki.

“Yanzu mutane na so Buhari ya dawo. A Najeriya, kowace sabuwar gwamnati tana ƙara muni fiye da ta baya. Wannan shi ne dalilin da ya sa mutane ke ci gaba da tunanin gwamnatin da ta gabata,” in ji shi.

Amaechi ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar APC a daren ranar Talata, inda yanzu ya koma jam’iyyar haɗaka ta ADC.

Ya ce tuni ya daina shiga harkokin jam’iyyar APC tun da daɗewa.

“Na fice daga APC jiya da daddare. Ban halarci taro ko guda ɗaha ba. Na taɓa gargaɗinsu, kuma na rubuta musu kada su sake gayyatata. Ba za ka zauna cikin ƙungiyar da yawancinsu suke satar dukiya ba, kai kuma ka yi shiru,” in ji shi.

Da aka tambaye shi me ya sa yake sukar gwamnatin da ya taɓa yi wa aiki, Amaechi ya ce matsalar Najeriya ba kawai shugabanci ba ne, sai an gyara tsarin gaba ɗaya.

Ya ce akwai bukatar fara shiri, ba kawai kafa jam’iyya ba, wanda zai haɗa ‘yan Najeriya su ƙwato ƙasarsu da hannunsu.

Amaechi ya kuma ce bai taɓa ganin Tinubu a matsayin mutum wanda ya cancanci ya mulki Najeriya ba.

“Na taɓa cewa Tinubu ba shi da ɗabi’u shugabanci. Har yanzu ra’ayina kenan,” in ji shi.

Ya soki yadda gwamnati ke tafiyar da tattalin arziƙi, musamman faɗuwar darajar Naira.

“Lokacin Buhari, dala tana kusa da Naira 460 ko Naira 500. Yanzu ta kai Naira 1580. Wannan ya fi kashi 100,” in ji shi.

Da aka tambaye shi ko wannan matsala ta Naira wata dabara ce ta gwamnati, Amaechi musanta hakan.

Ya ce, “Ko dabara ce ko akasin haka, duk wata gwamnati da ba ta damu da rayuwar mutane ba, ba za a ce dabara ce mai kyau ba.”

Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shi ma ya fice daga jam’iyyar APC, inda ya bu sahun Amaechi wajen komawa jam’iyyar ADC.

Ficewarsu da wasu manyan jiga-jigan siyasa na nuni da juyin juya hali kafin babban zaɓen 2027, yayin da jam’iyyar ADC ke neman zama sabuwar babbar jam’iyyar adawa a ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Buhari Haɗaka

এছাড়াও পড়ুন:

An Kashe Kusan Mutane 1500 Kan Sabanin Mazhaba A Kasar Siriya A Wata Guda

Mummunan kisan kiyashi kan ‘yan darikar Alawiyyan Siriya, kuma wadanda aka yi wa kisan gilla a kasar a watan Maris sun kai mutane 1,479

A cikin binciken da ya yi na baya-bayan nan, kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cikakkun bayanai na kisan gillar da aka yi tsakanin ranakun 7 zuwa 9 ga watan Maris din wannan shekara ta 2025, inda aka kai wa ‘yan darikar Alawiyya hare-hare a yankin gabar tekun Siriya. Binciken ya tabbatar da mutuwar Alawiyawa 1,479 da bacewar wasu da dama a wurare daban-daban guda 40, lamarin da ke nuni da karuwar tashe-tashen hankula da daukar fansa kan tsirarun mabiya mazhabobin Musulunci a kasar ta Siriya.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya wallafa binciken nasa ne bisa shaidar fiye da iyalai 200 da abin ya shafa, da kuma hirarraki da jami’an tsaro 40 da mayakan da kuma shugabannin yankin.

Yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton mutuwar mutane 111, inda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar da cewa adadin ya fi haka. Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syrian Network for Human Rights ta watsa rahoton cewa, an kashe mutane 1,334, da suka hada da yara 60 da mata 84, kuma dakarun gwamnati ne ke da alhakin mutuwar mutane 889.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Harin Filato: Remi Tinubu ta ba da gudummawar Naira biliya 1
  • ’Yan Najeriya sun fara begen Buhari saboda azabar TIinubu – Amaechi
  • 2027: David Mark zai kai mu ga nasara — ADC
  • Atiku, Obi, El-Rufai, Amaechi Da Wasu Sun Halarci Taron ADC Na jam’iyyar Haɗaka
  • David Mark ya fice daga PDP, ya shiga haɗaka don ƙalubalantar Tinubu
  • Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu
  • An Kashe Kusan Mutane 1500 Kan Sabanin Mazhaba A Kasar Siriya A Wata Guda
  • Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 
  • Togo: An Kashe Mutane 7 A Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati