Sojoji Sun Kashe Shugaban Ƴan Ta’adda Mai Dada
Published: 30th, June 2025 GMT
Sojojin Nijeriya sun kashe wani shugaban ‘yan ta’adda Mai Dada a yankin Maru na jihar Zamfara yayin wani farmaki na musamman.
Babban hafsan Soja Manjo Janar Markus Kangye ya bayyana cewa an kama wasu waɗanda ake zargin suna kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki, tare da aika wasu masu basu bayanai a jihohin Borno, Kaduna da Edo.
A Borno, Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da ƙwato makamai da harsasai da dama, yayin da aka kama wanda ake zargin jigilar kayayyakin ga ‘yan ta’adda a Monguno.
An kuma ƙwato bindigogi da harsasai a jihohin Kaduna da Filato, yayin da aka kama wasu ƴan fashi a Edo da Bayelsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Army yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Ta’adda Sun Kashe Jama’a A Kauyukan Sakkwato
Wani sabon rikici ya barke a jihar Sokoto inda ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Marnouna da ke karamar hukumar Wurno, inda suka kashe akalla mutum daya tare da yin awon gaba da wasu da ba a tantance adadinsu ba a lokacin da ake sallar isha.
Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Sokoto, Alhaji Isah Sadik Achida, wanda ya fito daga yankin ya tabbatar da faruwar harin inda ya jaddada cewa maharan sun kuma kashe shugaban kungiyar masu sayar da babura na yankin a yayin farmakin.
Achida ya ci gaba da cewa, kwana biyu kacal kafin harin masallacin, ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyuka biyu da ke makwabtaka da su, Gidan Taru da Kwargaba, inda suka yi garkuwa da wasu mazauna garin tare da jaddada cewa ‘yan bindigar sun kuma kashe wani dan uwa tare da kama iyalansa baki daya.
A cewar shugaban jam’iyyar APC, ‘yan ta’addan na kokarin kafa sansani a yankin domin fadada ayyukansu.
Achida ya tabbatar wa mazauna jihar cewa gwamnatin jihar da jami’an tsaro suna bakin kokarinsu domin yakar matsalar.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa’i, ya tabbatar wa gidan rediyon Najeriya faruwar lamarin inda ya ce a yanzu ‘yan fashin na kai hare-hare a lokutan damina domin kai hare-haren ba tare da an gano su ba.
NASIR MALALI