Aminiya:
2025-08-15@11:09:05 GMT

Isra’ila na neman ƙulla hulɗa da Siriya da Lebanon

Published: 1st, July 2025 GMT

Isra’ila ta bayyana shirin ƙulla hulɗa ta diflomasiyya da ƙasashen Siriya da Lebanon da suka daɗe ba sa ga maciji da juna a yankin Gabas ta Tsakiya.

Wannan na zuwa ne bayan samun lafawar rikici tsakanin Isra’ila da Iran.

Kasar Isra’ila ta ce za ta ƙulla hulɗa da ƙasashen da suka daɗe suna zaman doya da man ja, amma ta ce babu batun tattauna makomar tuddan Golan da ta ƙwace daga hannun Siriya.

Zan yi takara a Zaɓen 2027 — Peter Obi An sanya dokar hana fita a Kaduna

Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Gideon Saar wanda ya bayyana hakan a wannan Litinin din ya ce ƙasarsa tana da yaƙini kan karya lagon ƙasar Iran lokacin fito na fito na tsawon kwanaki 12 da suka yi a bayan nan.

Dangane da hakan ne Isra’ilan ke cewa za ta ƙara ƙulla hulɗa ta diflomasiyya da ƙasashen yankin.

A shekara ta 2020 Isra’ila da ƙulla hulda da kasashe da dama na Laraba na Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain gami da Maroko da ke zama karo na farko, bayan wadda Isra’ila ta ƙulla da Jordan a shekarar 1994, da kuma wadda aka fara yi da Masar a shekarar 1979.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Isra ila Siriya ƙulla hulɗa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojojin Mamayar Isra’ila Suna Ci Gaba Da Kashe Kansu Bayan Yakin Gaza
  • Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa
  • An zabi sabuwar firaminista a Luthuania
  • Hizbullahi Ta Yaba Wa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Irin Gudumawarta Ga Lebanon Da Gwagwarmaya
  • Larijani a Beirut: Iran A Shirye take ta taimaka ma Lebanon
  • Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Jaddada Kasancewar Iran Tare Da Kasar Lebanon Koda Yaushe
  • Iran: Janar Hatami ya karbi bakuncin babban hafsan hafsoshin sojin Afirka ta kudu
  • Sin Na Goyon Bayan Duk Wani Mataki Na Warware Batun Ukraine Ta Hanyar Lumana
  • Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
  • Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila