Indomie Ta Kaddamar da gangamin “Ingantaccen Abinci Domin Nasara” Don Daukaka Abinci Mai Gina Jiki da Murnar samun Nasara
Published: 28th, June 2025 GMT
Indomie , shahararriyar kampanin taliyar indomie a Najeriya, ta sanar da kaddamar da sabon gangamin ta mai taken Ingantaccen Abinci Domin Nasara. Wannan gangamin yana jaddada rawar da abinci mai gina jiki kamar Indomie ke takawa wajen ciyar da
nasarar iyalai da Karin lafiyar su a Arewacin Najeriya.
Shekaru da dama kenan da aka san taliyar Indomie da inganci, daɗi da arha a gidajen ‘yan Najeriya.
An ƙaddamar da gangamin ne a ranar 6 ga Yuni, 2025, Munaso mu kara jaddada
jajircewar Indomie wajen tallafawa iyaye mata da iyalai ta hanyar samar da abinci mai daɗi, mai sauƙin samuwa, Wanda yake cike da sinadaran gina jiki kuma ke inganta girma, kuzahri da cimma burin rayuwa.
Kunshe a cikin tallar na talabijin akwai labarin Binta. yarinya daga arewacin Najeriya
wacce burinta na zama likita ya samo asali ne ta hanyar soyayyarta da abinci mai gina jiki Wanda mahaifiyarta ke ba ta. Za’a iya kallon faifan tallar a Manhajar YouTube, labarin rayuwar Binta da yake jaddada muhimmanci abinci Mai Gina jiki da goyon bayan Ahali.
Tallar ya bada labarin rayuwar Binta ya kuma maida hankali Akan tasirin abinci Mai kyau wajen tallafawa iyali. Da labarin yayi nisa, mun gano Binta tun daga ƙuruciya zuwa
shigarta makarantar koyon aikin likitanci. Hakan ya nuna yadda abinci mai kyau da
goyon bayan Ahali ke taka muhimmiyar rawa wajen cin nasara. Binta ta girma da cin abinci Mai Gina jiki tun farko wato Taliyar Indomie.
Indomie tun da dadewa tana da yakini cewa ciyarwa ba wai ga kawai jiki ba ne. Muna ciyar da mafarkai da makomar kowanne yaro gaba. Shi ya sa muka ƙirƙiri Indomie AI
Career Generator, wata Manhaja ta musamman da ke taimaka wa yara su hangi manyan burinsu ta hanyar hotuna masu kayatarwa da ƙarfafa gwiwa.
Ta ziyartar https://nasarada.indomie.ng kawai, iyaye za su bi wasu matakai masu sauki domin su samar da hotunan yaransu a matsayin likita, lauya, injiniya, da dai sauransu. Wannan wata hanya ce daga gare mu domin kusanta su da mafarkinsu, sanya nasara ta zama mai yuwa, da kuma nuna wa kowane yaro cewa makomarsu tana da amfani, ana iya hangenta, kuma tana dab dasu.
Dauke Da Muhimman Sinadaran Gina Jiki TaliyarIndomie na dauke sinadarai masu matuƙar amfani ga jiki, kamar su: calcium, iron, protein, Vitamin B da Vitamin A. Duka suna taimakawa wajen girma, bunƙasa kwakwalwa da kuma lafiya mai ɗorewa. Wannan ya saka Indomie ya zama abinci
daddadar abinci mai sauƙin shiryawa, Wanda ya hada kayayyakin bukata da akeso a kowani kalar abinci.
“Muna alfahari na kaddamar da gangamin ‘Nasara Da Indomie’ wanda ke murnar rawar da abinci mai gina jiki ke takawa wajen gina kyakkyawar Rayuwa anan gaba,” in ji Jamiu Abdulrasheed, jami’in tallace tallace a Manhajar zamani na
Indomie “Wannan girmamawa ce ga sadaukarwar da iyaye mata ke yi wajen ciyar da iyalansu da abinci mai amfani, da kuma nuna yadda Indomie ke haɗa daɗin ɗanɗano da gina jiki domin tallafawa nasara.”
An ƙarfafe masu kallo da su duba wannan labari mai saka kaimi na Ingantaccen Abinci Domin Nasara a shafukan sada zumunta: @IndomieArewa a Manhajar Facebook da
@indomie_arewa a Manhajar Instagram.
Indomie Nigeria zata cigaba da jajircewa wajen samar da hanyoyin abinci masu gina jiki ga iyalai da kuma tallafawa hanyarsu ga cinma nasara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ingantaccen Abinci Domin Nasara
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Karamar Hukumar Dutse Sun Bukaci Gwamnatin Jigawa Ta Yashe Madatsar Ruwa Ta Warwade
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin.
Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata.
Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum.
Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran bukatun yau da kullum.
Yace ana samun ribar kimanin naira dubu goma zuwa ashirin a kowace rana daga siyar da kifin ga matafiya da kuma baki masu kai ziyara garin.
A don haka, Umar yayi kira ga gwamnatin jihar Jigawa da ta yi yashen madatsar ruwan saboda a samu karin kifaye da kuma ruwa da za a iya amfani da shi domin noman rani.
Shi ma a yayin tattaunawa da Dagacin Warwade, Malam Musa Ado, ya ce madatsar ruwan tana samar da ayyukan yi ga matasan yankin, tare da hana tafiya zuwa cirani a sauran yankunan kasar nan da sunan yin sana’o’i.
Ya ce matasan yankin suna gudanar da sana’ar kamun kifi da kuma nomar rani da ta damina.
Sai dai kuma, Malam Musa ya koka kan rashin samar da injinan noman rani da kuma Malaman gona kamar yadda ake yi a gwamnatocin baya.
Kazalika, yace a ‘yan kwanakin baya gwamnatin jihar Jigawa ta kai ziyara kauyen inda ta sanar da cewar Bankin duniya zai samar da wasu kudade ta hannun gwamnatin tarayya wanda za’a baiwa gwamnatocin jihohi domin yashewa tare da gina burtuloli da hanyoyin noman rani.
Bisa haka ne dagacin yayi kira ga gwamnatin jihar da ta fara yin garambawul a madatsar ruwan domin a baiwa mazauna yankunan damar amfani da shi.
A shekarun baya dai, gwamnatin jihar Jigawan ta samar da irin kifaye guda dubu Dari uku domin inganta samar da kifi a yankin.
Usman Mohammed Zaria