Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce; Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ta Kasar Kan Hukumar IAEA Dole Ne Aiki Da Ita
Published: 30th, June 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta kasar ta dakatar da hadin gwiwa da hukumar IAEA dole ne aiki da ita
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Ismail Baqa’i ya bayyana a wani taron manema labarai cewa: Dole ne hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ta yi aiki nesa da batun siyasa, yana mai nuni da cewa: Dokar Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran kan dakatar da hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar ta IAEA, dole ne yin aiki da ita.
A zaman taron manema labaransa na mako-mako kan taron tunawa da juyayin shahadan Imam Husaini (a.s), Baqa’i ya ce: “A gare su makokin Ashura ba wai kawai zaman makoki ne na wani lamari mai raɗaɗi ba, a’a, abin tunawa ne na al’adu da wayewar al’ummar Iran na rayuwa ta mutuntaka.” Wato kiyaye mutuncin dan’adam, da rashin yarda da mulkin kama karya ta kowace fuska.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu. “A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, ni da mataimakin shugaban kwamitin tattaunawa na gwamnatin tarayya, mun tattauna da ASUU, zan iya gaya muku a yau, a zahiri, an biya kusan dukkan bukatun ASUU, don haka ban ga dalilin da ya sa ASUU ta fara yajin aikin ba.” In ji Ministan ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Hukumar Hisbah Ta Kama Wasu Matasa Da Suka Yi Aure Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Kano October 13, 2025
Ra'ayi Riga Labarin Xinjiang A Zane: Aikin Yawon Shakatawa Na Kara Samar Da Arziki Ga Al’ummar Xinjiang October 13, 2025
Labarai Ba Gudu Ba Ja-da-baya Kan Ci Gaba Da Kwaskwarima Ga Tsarin Haƙar Ma’adanai – Minista October 13, 2025