Muhsin Rizai: Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Bayar Da Umarni Da Jagorantar Yakin “Wa’adussadiq 3”
Published: 3rd, July 2025 GMT
Tsohon kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran Muhsin Rizai ya bayyana cewa; Jagoran juyin musulunci Ayatullah sayyid Ali Khamnei ne ya jagoranci da kuma bayar da umarnin yakin “Wa’adussadiq 3” akan HKI.
Dr. Muhsin Rizai wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama shahidai da aka yi a jiya Laraba a babban masallacin juma’a na Tehran ya kara da cewa; A karon farko jagoran juyin musulunci ne ya rika bayar da umarni da kuma jagorantar yadda yaki da HKI ya kasance.
Dr. Muhsin Rizai wanda shi ne kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran a lokacin kallafaffen yaki da Iraki, ya kuma ce; An yi aiki tare a tsakanin babbar shalkwatar soja ta “Khatamul-Anbiya” da kuma babbar cibiyar Dakarun kare juyin musulunci, inda jagoran ne ya rika bayar da umarni a matsayinsa na babban kwamandan dukkanin rundunonin tsaron kasa, akan yadda yakin ya rika tafiya. “
Da yake Magana akan sake kawo wa Iran hari da ‘yan sahayoniya za su yi, Dr.Muhsin Rizai wanda a halin yanzu memba ne a cikin majalisar fayyace maslahar tsarin musulunci ya ce; Idan hakan ta faru, to martanin da Iran za ta mayar zai fi na baya tsananin da zai fi karfin a iya kwatanta shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kalibof Yace: Iran Zata Maida Martani Mai Tsanani Kan HKI Idan Ta Sake Bude Yaki da Iran
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran Muhammad Bakir Qalibof ya bayyana cewa HKI zata gamu da maida martani mafi tsanani idan ta seke farfado da yaki da JMI, sannan sai sun yi nadamar fara yakin kamar yaki da kwanaki 12.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Qalibof yana fadar haka a jiya Laraba a lokacinda yake gabatar da jawabi a taron tunawa da kuma yin addu’a ga shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kawowa kasar.
Ya ce HKI ba zata jurewa yaki mai tsawon lokaci ba, saboda Iran ta fi karfinsu, sannan wannan ne yasa gwamnatin Amurka ta shiga yakin, inda ta takaita da kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin nukliyar kasar a fordo da Natanz da kuma Esfahan.
Daga karshe shugaban majalisar dokokin kasar ta Iran ya bayyana cewa duk wata karawa da HKI zata kasance mai murkusheta ne , ta yadda ba zata sake tashi ba.