Kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ya ce kasarsa na adawa da duk wata yarjejeniyar yafe haraji da Amurka za ta kulla da wata kasa, wadda ka iya illata moriyar Sin, tare da baiwa kasar da aka kulla yarjejeniyar damar samun yafiyar haraji daga Amurka.

Kakakin wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, lokacin da yake amsa tambayar da manema labarai suka yi masa, dangane da tattaunawar cinikayya da Amurka ta yi tare da wasu kasashe, ya ce, idan an samu aukuwar irin wannan yanayi, kasar Sin ba za nade hannu ba, za ta dauki matakai na martani domin kare halastattun hakkoki da moriyarta.

Jami’in ya kara da cewa, tun watan Afrilun da ya gabata, Amurka ke ta ingiza matakan kakaba harajin ramuwar gayya kan abokan cinikayyarta. wanda hakan mataki ne na nuna fin karfi da ya yi matukar keta tsarin gudanar da hada-hadar cinikayya na duniya, ya kuma haifar da cikas ga tsarin gudanar hada-hadar cinikayya tsakanin sassan kasa da kasa, kuma Sin ta sha nanata rashin amincewarta da hakan.

Daga nan sai jami’in ya ce, ta hanyar kare manufofinta, da matsayarta ne kadai kasa za ta cimma nasarar kare hakkokinta na halas. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa

 

‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.

 

Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.

 

Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe Laraba wakilan masu sassaucin ra’ayi na jam’iyyar Socialist za su gana da Firaminista Lecournun mai murabus.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Ko Afirka Za Ta Samu Kujerar Dindindin A Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya? October 12, 2025 Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  October 12, 2025 Rahotonni Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya October 11, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
  • Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice  
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh
  • An Yi Girgizar Kasa Mai Daraja 5 A Ma’aunin Richter  A Kasar Habasha
  • Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
  • Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa
  • Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa
  • Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara