Ƙoƙarin Ƙungiyoyin Afrika A Gasar Kofin Duniya
Published: 28th, June 2025 GMT
Nasarar da kungiya ta samu a matakin rukuni za a ba ta Dala miliyan biyu, canjaras kuma miliyan daya, wadda ta cinye kofin kuma za ta samu ladan Dala miliyan 40. Ganin yadda kungiyoyin Turai suka mamaye gasar, Afirka na fatan samun karin dama a nan gaba, ma’ana a Karara nahiyar Afirka yawan kungiyoyin da za su dinga wakiltar ta.
Wasu na fatan kungiyoyin Afirka da ke cikin gasar za su ja hankalin duniya zuwa nahiyar ko da kuwa gasarta ta zakaru ba ta iya yin hakan ba, da kuma kawo musu kudi idan aka kwatanta da takwarorinsu.
Sabuwar gasar African Footbal League da hukumar CAF ta kaddamar a 2023 ba a sake yin ta ba, duk da irin rigingimun da aka yi lokacin da aka fara ta, mai tawaga hudu wadda kungiyar Sundowns ta lashe.
Kungiyar Pretoria da shugaban hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF, Patrice Motsepe ya mallaka, ta kafa kanta a matsayin jagora a harkar kwallon kafar Afirka – ita ta lashe kofunan gasar Afirka ta Kudu tara na baya-bayan nan.
Sundowns za su kara da Ulsan HD da Borussia Dortmund da Fluminense a Rukunin F, abin da wani magoyi kwallon kafa ya ce zai taimaka wajen nasararta a gasar ta Club World Cup.
Lokacin gudanar da gasar Club World Cup ya shafi harkokin wasa a Afirka, ta yadda sai da aka matsar da lokacin gudanar da gasar Kofin kasashen Afirka wato AFCON 2025 daga watannin Yuni da Yuli zuwa karshen shekarar ta 2025. Tuni kungiyar kwararrun ‘yankwallo ta duniya ta shigar da kara a shekarar da ta gabata kan abin da suka kira “nuna karfin iko” da FIFA ta yi wajen fadada gasar, amma kuma duk da haka ba a dakata ba.
Danwasan Nijeriya na AC Milan Samuel Chikwueze ya ce kungiyarsa ba za ta buga gasar ba, amma duk da haka yawan wasannin da za su buga sun yi yawa. ‘Yan wasan dai sun yi korafin cewa lokaci daya da ‘yanwasa za su huta shi ne daidai lokacin da suka saka gasar. ‘Yan wasan sun bayyana cewa abu ne mai wahala buga wasanni masu yawa domin mutum zai gajiyar da kafufuwansa da tunaninsa ta yadda ma ba zai ji dadin buga wasan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Duniya Ƙwallon Ƙafa
এছাড়াও পড়ুন:
Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa
Mahukuntan kasar Afirka Ta Kudu sun sanar da cewa, ya zuwa yanzu ba a sami wani dalili na musabbabin mutuwar jakadan kasar Nathi Mthethwa A Afransa ba.
Jami’an tsaron kasar Faransa suna aiki tare da takwarorinsu na kasar Afirka Ta Kudu da su ka isa kasar domin gano musabbabin mutuwar jakadan.
An ga gawar jakadan na kasar na Afirka Ta Kudu a kasar Faransa,Mthethwa a Hotel din Hyatt Regency dake birnin Paris. Alamu sun nuna cewa ya bude kofar dakinsa dake hawa na 22 ya fado kasa, ba tare da wata alama dake nuni da cewa turo shi aka yi baa.
Gabanin faruwar lamarin jakadan ya aike da sako na waya ga maidakinsa da a ciki ya bayyana mata shirinsa na kisan kai.
Kasar Afirka Ta Kudu ta aike da jami’an bincike su biyar zuwa Faransa domin su yi aiki da takwarorinsu na kasar akan binciko hakikanin abinda ya faru.
Mthethwa ya zama jakada ne tun a 2023, bayan da a can baya a kasarsa ya rike mukamai da dama a fagagen al’adu da wasanni.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hamas Ta yi Watsi Da Yunkurin Balair Na Yiyuwar Shiga Gwamnatin Gaza. October 11, 2025 Cuba Ta Bayyana Bada Kyautar Noble Ga ‘Yar Kasar Veunzuelas machado A Matsayin Abin Kunya. October 11, 2025 Kasar Indunusiya Ta Hana Tawagar wasan Jiminastik din Isra’ila Visar Shiga Kasarta October 11, 2025 Ammar Hakim Ya Gargadi Kasashen Yamma Da su Kiyayi Tsoma Baki A Harkokin Cikin Gidan Kasar. October 11, 2025 Sarkin Morocco Ya yi Magana Tun Bayan Barkewar Zanga-zanga A Kasar . October 11, 2025 Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa October 11, 2025 Bayan Yakin Kwanaki 12, Kifar Da Gwamnatin JMI Ya Fita Daga Zabin Makiya: Aref October 11, 2025 Iran Ta Bukaci HKI Ta Aiwatar Da Yarjeniya Da Gaza Kamar Yadda Take October 11, 2025 HKI Ta Kashe Mutane 19 A Gaza Duk Tare Da Tsagaita Wuta October 11, 2025 Iran Tana Goyon Bayan Duk Wani Shirin Zaman Lafiya Da Ya Hada Da Kawo Karshen Kisan Kiyashi A Gaza October 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci