HausaTv:
2025-07-03@01:39:22 GMT

Aragchi: Iran Ba zata Taba Daina Tace Makamashin Uranium A Cikin Gida Ba

Published: 2nd, July 2025 GMT

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran kuma na zaman lafiya ya zama abin alfakhari ga mutanen kasar da daukaka. Don haka gwamnati mutanen kasar ba zasu taba yarda a barshi ba.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da tashar talabijin ta CBS news na kasar Amurka dangane da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar a cikin watan yuni da ya gabata.

Hare-haren  da aka kaiwa kasar a dai-dai lokacinda take tattaunawa da Amurka.

A wani bangare a maganars Aragchi ya bayyana cewa baya ganin Iran zata farfado da tattaunawa da kasar Amurka nan kusa.

Ya ce: Idan har zamu sake shiga tattaunawa da Amurka sai mun tabbatar da cewa Amurka ba zata kuma kai mana hare-hare a dai-dai lokacinda muke tattaunawa ba.

Ya kara da cewa, tare da wannan tunanin muna ganin sake zama da Amurka kan teburin tattauna ba nan kusa ba. Daga karshe ya ce: a duk sanda muka ga dama ta samu, bama rufe kofar tattaunawa da kowa .

Da aka tamabaye shi dangane da shirin makamashin Nukliya na kasar bayan bom da aka jefa masu. Ministan ya ce: Ai ba’a kauda shirin nukliya da bom. Ko babu shi kwata-kwata zamu sake gina wani daga farko. Sannan idan sun baci ne muna iya sake gyaransu sai mu ci gaba.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: tattaunawa da

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Ba Za A Iya Kawar Da Fasahar Nukiliya Da Karfi Ba

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a iya kawar da fasahar nukiliya ta hanyar harin bam ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Ba za a iya kawar da fasaha da kimiyyar da ake bukata don inganta sinadarin Uranium ta hanyar kai hare-haren bama-bamai ba.

A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta CBS, Araqchi ya yi tsokaci kan ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na cewa ana iya komawa tattaunawa da Iran a cikin wannan mako: Araqchi yana mai mayar da martini da cewa: “Ba ya jin za a dawo da tattaunawar cikin gaggawa.”

Ya kara da cewa: “Kafin yanke shawarar komawa kan tattaunawar, dole ne Iran ta fara tabbatar da cewa Amurka ba za ta sake kai wa kasarta harin soji ba yayin tattaunawar.”

Ya ce: Ya yi imani tare da wannan la’akari, cewa har yanzu Iran tana bukatar karin lokaci, amma kofofin diflomasiyya ba za su taba rufewa ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Aragchi: Hare-Haren HKI Ya Kara Rashin Zaman Lafoya A Yankin Yammacin Asiya
  • Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare
  • Amurka Ta Dakatar Da Tura Makamai Zuwa Kasar Ukraine Saboda Kada A Sami Karancinsu A Gida
  • Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU
  • Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Ba Za A Iya Kawar Da Fasahar Nukiliya Da Karfi Ba
  • Iran Ta Ce Babu Batun Tattaunawa Duk Tare Da Amurkawa Sun Ce Za’a Yi
  • Iran Ta Ce: Ba Za Ta Koma Zaman Tattaunawa Da Amurka Ba Sai A Kan Wasu Sharudda
  • Iran Tana Tababa da Ayyukan Hukumar Makamashin Nukl’ila Ta MDD Wato IAEA A  Halin Yanzu
  • Lebanon Ta Nuna Damuwarta Da Yiyuwar Yan Ta’adda Daga Siriya Su Kawo Hare-Hare Cikin Kasar