Da yake jawabi jim kadan kafin tashinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin uba ga mutane da yawa, wanda karamcinsa da sadaukarwarsa ya wuce iyaka.

 

Gwamnan ya jaddada cewa, zuwan tawagar a Madina shaida ce ta matukar mutuntawa da jama’a da gwamnatin jihar Kano suke yi masa na gadon alkairai da ya bari kuma a matsayinsa na dattijon jihar.

 

Ana sa ran jana’izar da za a yi a birnin Madina, za ta samu halartar wakilan jiha da na tarayya, da ‘yan uwa, ‘yan kasuwa, malaman addinin Islama, da masoya daga sassan duniya baki daya, tare da yin addu’ar Allah ya jikansa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Farfado Da Karkarar Sin: Canjin Gaisuwa Daga “Shin Ka Ci Abinci?” Zuwa “Yaya Rayuwarka A Gari?”

Shin kun san, a lokacin da Sinawa suka hadu da juna, gaisuwar da suke yi ita ce, “Shin ka ci abinci?” Wannan gaisuwa mai sauki tana nuna damuwar mutanen dake rayuwa bisa aikin noma, wato ma’ana, tambaya ce a kan ko ana da isasshen abinci?

A halin yanzu, wannan gaisuwa mai cike da nuna damuwa, tana samun sauyi mai ban sha’awa a yankunan karkarar kasar Sin. Dai Yihui, wadda ba ta wuce shekaru 30 da haihuwa ba, ta koma garinta na lardin Jiangsu, domin kula da gandun noma na iyalinta, inda ta yi kokarin kara yawan amfanin gona da kashi 35 bisa dari ta hanyar amfani da injunan noma na fasahar zamani, sai dai kuma mazauna garin sun canza gaisuwar gargajiya da ake yi daga “Shin kin ci abinci” zuwa “Yaya rayuwarki a garin?” Wannan gaisuwa ta nuna yadda irin gagaruman sauye-sauye da tsarin farfado da karkara a dukkan fannoni da ake kawo wa jama’ar kasar Sin.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Lawal Ya Ziyarci Yankunan Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Wa Hari A Zamfara
  • ’Yansanda Sun Kama Mutum 2 Da Bindigogi Da Alburusai A Filato
  • Farfado Da Karkarar Sin: Canjin Gaisuwa Daga “Shin Ka Ci Abinci?” Zuwa “Yaya Rayuwarka A Gari?”
  • Gwamna Namadi Ya Yaba Wa Kungiyar NBA Bisa Inganta Manufofi Da Ka’idojin Aikin Lauya
  • Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita
  • EFCC Ta Bayar Da Belin Tambuwal, Ta Yi Allah-wadai Da Zargin Da Jam’iyar ADC Ta Yi
  • ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Kashe Wani Mutum Da Jikkata Wasu Da Dama A Sokoto
  • Gwamnatin Kano Za Ta Horar Da Tubabbun ‘Yandaba 718 Sana’o’i 
  • Jiragen saman NAF Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 592, Sun Lalata Kayayyakin Yaki 372
  • Shettima Ya Jagoranci Tawagar Gwamnatin Tarayya Don Yi Wa Iyalan Ogbeh Ta’aziyya