2025-09-21@01:06:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6213

«ganga miliyan»:

    Al’ummar Jihar Sakkwato na cike da fargaba da alhini bayan da wasu mazauna kauyuka da dama suka rasu a hatsarin kwale-kwale a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Lamarin ya faru ne lokacin da jama’a ke tserewa daga wani sabon harin da ‘yan ta’addan Lakurawa suka kai, inda kwale-kwalen da ke dauke da mutane fiye da kima ya kife. Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Abubakar Rufa’i, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga wakilin Rediyon Najeriya a jihar. ASP Abubakar ya ce har yanzu ba a tantance adadin mutanen da suka shiga kwale-kwalen ba, yana mai jaddada cewa ana ci bincike da aikin ceto. Wani shaidan gani da ido, wanda bai...
    A gun liyafar murnar cika shekaru 76, da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin da ofishin jakadancin Sin dake Birtaniya ya shirya a jiya Jumma’a 19 ga wata, an gabatar da wani fim mai taken Shen Zhou 13, fim din kasar Sin na farko da aka dauka kai-tsaye a sararin samaniya kuma bisa fasahar 8K, wadda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar wato CMG ya tsara. Wannan ne karo na farko da aka gabatar da fim din a kasashen waje. Al’ummun kasar Birtaniya daga bangarori daban daban, da jami’an diflomasiyyar kasa da kasa dake Birtaniya, gami da Sinawa dake zaune a kasar sama da 400, sun halarci liyafar. Wasu ’yan saman jannati uku na kumbon Shenzhou-13, wato Zhai Zhigang,...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta kashe ’yan ta’addan Boko Haram 32, a wani farmaki da ta kai garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno. Rahoton ya bayyana cewa farmakin ya auku ne a ranar 18 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10:15 na safe. Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato Wannan na zuwa ne bayan ’yan ta’addan sun kai hari hedikwatar ’yan sanda da ke Banki. A lokacin kai farmaki , sojoji biyu sun rasa rayukansu, haka kuma wani ƙaramin yaro mai shekara tara, Ismail Abubakar, ya rasu. Har ila yau, maharan sun ƙone motocin soja uku. Bayan kai...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce matsayin Sin dangane da batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma tana jaddada aniyar gwamnatin kasar na martaba hakkokin kamfanoni yadda ya makata. Ma’aikatar ta ce Sin na maraba da matakin gudanar da shawarwari da kamfanoni bisa doron dokokin kasuwa, ta yadda za a iya kaiwa ga shawo kan matsaloli daidai da dokokin kasar Sin, da ka’idoji, da daidaita moriyar dukkanin sassa masu takaddama. Ma’aikatar ta ce Sin na fatan Amurka za ta dauki makamancin wannan tafarki, ta cika alkawuran da ta dauka, da samar da wata kafa ta adalci, marar nuna wariya, kuma ta bunkasa muhallin kasuwanci ga kamfanonin kasar Sin, ciki har da kamfanin TikTok, ta yadda zai ci gaba da...
      Kamfanin dillancin labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, lamarin wanda ya faru ne a lokacin da ake gudanar da aikin a ƙarshen mako a masana’antar, ya yi sanadin mutuwar ma’aikata biyu ciki har da wani jami’in soji da ke aiki tare da jikkata wasu huɗu.   “Na ji wani babban ƙara har sai da ya girgiza gine-ginen da ke kewayen DICON. Mutane na ta gudu daga wurin, amma muna tunanin fashewar bam ne, amma daga baya mun gano cewa daga masana’anta ne,” inji wani mazaunin da ya nemi a sakaya sunansa.   Shaidun gani da ido sun ce fashewar na da nasaba da samar da hoda mai matukar muhimmanci wajen ƙera hodar harsashi ga sojojin Nijeriya. Daga...
    A kwanan nan ne aka rufe taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO a takaice, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin, inda shugaban kasar, Xi Jinping ya gabatar da shawarar tsarin inganta jagorancin duniya. Wakiliyar babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG, ta zanta da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, wanda ya halarci taron, inda ya ce, ana amfani da ma’aunai biyu a halin yanzu a duk duniya. A cikin shawarar tsarin inganta jagorancin duniya da shugaba Xi Jinping ya gabatar, akwai wani muhimmin bangare na gudanar da harkokin duniya bisa dokokin kasa da kasa, wato ya kamata a mutunta ka’idoji. Masoud Pezeshkian, ya ce bai kamata a aiwatar da ma’aunai biyu a...
    Venezuela ta yi Allah-wadai da Amurka kan abinda ta danganta da yakin da ba ta shelanta ba a yankin Caribbean, ta kuma bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta binciki sabon harin da Amurka ta kai kan wani jirgin ruwa, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane uku.. Shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa sojojin Amurka sun kai hari na uku kan wani jirgin ruwa da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi. Ya fitar da wani sabon faifan bidiyo da ke nuna abin da ya yi ikirarin harin da Amurka ta kai da ya kashe ‘yan ta’adda uku.. Wadannan hare-haren da jiragen yakin Amurka F-35 suka kai, rahotanni sun ce sun kashe akalla mutane 17 a cikin ‘yan makonnin nan....
    A shekarar 2025 a gundumar Qiemo dake jihar Xinjiang ta kasar Sin, wasu sabbin sassan dausayi da ake iya nomawa sun bayyana a cikin makeken yankin hamada. A ’yan shekarun nan, an gyara yankin rairayi zuwa gonaki, wadanda fadinsu ya zarce murabba’in kilomita 40 a gundumar Qiemo. A cikin sama da shekaru 10, an yi kokarin raya wasu sassan dausayi da ake iya nomawa a cikin yankin hamada dake jihar Xinjiang, inda fadin gonakin da ake noman hatsi ya karu zuwa murabba’in kilomita dubu 8 ko fiye, al’amarin da ya sa Xinjiang ta zama jihar da ta fi samun karuwar hatsi da ake nomawa a duk fadin kasar Sin. Wani babban manomi dake wurin, mai suna Liu Yong, ya ce...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
    Sama da mako uku da suka gabata, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da wani magidanci da matarsa mai juna biyu da kuma ’yarsu a unguwar Kanada da ke Ƙofar Ƙaura a garin Katsina. Masu garkuwar sun fara neman a biya su naira miliyan 100 kafin su sako su, amma daga baya aka daidaita da su a kan naira miliyan 50. Mahaifin Halimatu, Alhaji Ali Turare, ya tabbatar da biyan kuɗin kafin a sako ’yarsa da mijinta da jikarsa. “Bayan kwana uku da biyan kuɗin ne suka kira mu ta waya, suka ce an sako su, a je a karɓe su a Gurbin Ɓaure. Yanzu haka duk suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi. Sai dai har zuwa lokacin...
      Ya ce Morocco, ta sha alwashin zurfafa hadin gwiwa tare da Sin, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, da fadada musaya a fannoni irinsu yawon bude ido, da ilimi, da al’adu, da ci gaba da yayata kawance bisa matsayin koli tsakanin kasashen biyu. A daya bangaren kuma, Morocco na maraba, da kuma goyon bayan shawarar inganta tsarin shugabancin duniya da Sin ta gabatar. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mutum tara sun rasu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya auku a ƙauyen Zalla Bango, da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, a Jihar Sakkwato. Wani mazaunin yankin ya ce hatsarin ya faru ne bayan sallar Magariba a ranar Alhamis, lokacin da jirgin da ya ɗauki mata, maza da yara, domin tsallaka ruwa saboda hanyar mota ta yanke sakamakon ambaliya. Wata mata ta haifi ’ya’ya huɗu a Bauchi Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi Yayin da yake tafiya, jirgin ya bugi wata ƙaramar gada ta nutse a ruwa, lamarin da ya jawo mutuwar mutum tara, yayin da wasu suka samu rauni. Rahotanni sun ce ba a san adadin mutanen da ke cikin jirgin ba saboda ya...
    Wata mata ta haifi jarirai huɗu — maza biyu da mata biyu — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Kiwon Lafiya (FUHSTHA) da ke Azare, a ranar Alhamis, 18 ga Satumba, 2025. Sakataren yaɗa labarai na asibitin, Abdu Mohammed, ya shaida wa Aminiya cewa Malama Hauwa ta haifi yaran ne ta hanyar tiyata, kuma tana ci gaba da jinya tare da ’yan huɗun. A washegarin haihuwar, Hajiya Halima Garba, matar shugaban asibitin (CMD), ta ziyarci mai jegon tare da mijinta da manyan ma’aikatan asibitin. Ta taya iyalan murna tare da addu’ar samun lafiya cikin gaggawa. ’Yan bindiga sun kashe basarake, sun tarwatsa mutane a Sakkwato Kwalara ta kashe mutane 58, wasu sun kamu a Bauchi Kamar yadda ta...
    A baya, ƙasashe biyu kawai na Afirka ba sa shigo da man fetur, amma abin takaici, yanzu sun koma shigo da kaya. Wannan yana da illa ga Afirka,” in ji shi. Dangote ya bayyana cewa aikin masana’antar ya kasance mai haɗari sosai. Ya ce ya samu gargaɗi sau da dama daga masana harkokin mai, masu zuba jari, da jami’an gwamnati na cikin gida da waje, waɗanda suka yi jayayya cewa irin wannan aikin masana’antar mai girma manyan ƙasashe ne kaɗai ke iya yi, ya amince cewa da aikin ya gaza, zai rasa dukiyoyinsa ga masu ba da rance. “Yanke shawarar gina masana’antar ba abu ne mai sauƙi ba. Idan ya gaza, masu ba da rance za su daka wawa a...
    A nasa bangare kuwa, shugaba Trump cewa ya yi alakar Amurka da Sin ita ce mafi muhimmancin dangantaka a duniya, yana mai cewa aiki tare tsakanin kasashen biyu ka iya haifar da manyan abubuwa da za su ingiza zaman lafiya da daidaito a duniya. Daga nan sai ya yi fatan wanzar da babbar dangantaka mai armashi ta dogon lokaci tsakanin kasarsa da Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba. Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba Jonathan, ya yi wannan jawabi ne a taron shekara-shekara na Tattaunawar Gidauniyar Goodluck Jonathan da aka gudanar a Birnin Accra, na Ƙasar Ghana. Ya ce mutanen Afirka na son a yi amfani da ƙuri’unsu don su samu shugabanni da za su inganta ilimi,...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin Lakurawa ne, sun kai hari ƙauyen Sayinna, da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sakkwato. Sun kashe Hakimin ƙauyen, Malam Murtala Sa’adu, tare da wani mutum mai suna Ibrahim Mai-Kuɗi. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba Mai bai wa shugaban Ƙaramar Hukumar Tangaza shawara, Alhaji Gazali Raka ne, ya tabbatar da harin. Ya ce maharan sun kashe hakimin ne saboda yana taimaka wa ’yan sa-kai wajen tsaro a yankin. An ce maharan sun shiga ƙauyen ne da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar Alhamis, inda suka dinga harbi a ko ina. Bayan sun kashe mutanen biyu, sai...
    Duk da cewa, Nijeriya ce kan gaba wajen kiwon dabbobi a nahiyar Afirka, amma har yanzu, mahukunta a ƙasar sun gaza gudanar da wani kyakkyawan tsari da kuma samar da kayan aiki wajen samar da kashin na dabbobi, inda rashin hakan ke ci gaba da haifar da damuwa ga waɗanda ke fannin a faɗin ƙasar. “Nijeriya za ta iya samun daloli masu yawa a kasuwar ta duniya”, a cewar Chuka Mordi Babban Jamie’s kamafanin Ellah Lakes kuma wanda ya kasance ɗaya daga cikin masu goyon bayan ganin ana fitar da kashin dabbobin zuwa kasuwannin duniya, domin yin hada- hadar kasuwancinsa. “Kashin dabbobin ya kasance ɗaya daga cikin hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga, musamman wajen sarrafa kashin dabbobin zuwa takin zamani,...
    Kimiyyar sadarwa ta kawo sauƙin rayuwa a harkokin kasuwanci da mu’amalar kuɗi ta banki. Yawaitar amfani da wayar hannu wajen yin hada-hadar banki a Nijeriya ya sa mutane da dama ke tura kuɗi cikin sauƙi. A shekarar 2024 kaɗai, rahoton Hukumar Biyan Hada-hadar Banki ta Ƙasa (NIBSS) ya nuna cewa darajar kudin da aka tura ta hanyar waya ta kai Naira tiriliyan 41.5, lamarin da ya nuna ƙaruwar kaso 74 cikin 100 daga shekarar da ta gabata. Sai dai kuma hakan na iya kawo matsala, musamman idan aka yi kuskure aika kuɗi zuwa wani asusu daban. Wannan na faruwa sosai, musamman idan aka rubuta lambar asusu ko sunan mai asusu ba daidai ba. Shin me ya kamata mutum ya fara...
    An bukaci gwamnatin jihar Kwara da ta gaggauta shiga tsakani kan rufe kasuwar Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi domin ceto harkokin kasuwanci daga durkushewa.   Shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Shehu Garba ne ya yi wannan roko a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Ilorin.   Sanarwar ta ce shirin rufe kasuwannin Kara da ke yankin Kwara ta Kudu da shugaban karamar hukumar ya yi ba tare da sanin sarakunan gargajiya da shugabanni da masu gudanar da aiki ba, bai dace ba.   Ya bayyana cewa kafin daukar irin wadannan shawarwarin da shugaban karamar hukumar ya yi ya kamata a yi shawarwari da yawa don tafiyar da...
    Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauya sunan ma’aikatar harkokin mata, yara da nakasassu a hukumance zuwa “Ma’aikatar harkokin mata, yara da masu bukata ta musamman.”   Wannan dabarar yanke shawara, ga kwamishiniyar harkokin mata Ambasada Hajiya Amina Sani Abdullahi, ta nuna irin kwakkwaran kudurin gwamnati na inganta mutunci, hada kai, da daidaito ga dukkan ‘yan kasa musamman masu bukata ta musamman.   A cewarta, sake suna ya yi daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya ta hanyar maye gurbin tsoffin kalmomin da za su iya ɓata lokaci da mutane-harshen farko wanda ke mutunta haƙƙin ɗan adam da kuma kiyaye ƙa’idodin adalci na zamantakewa.   “Wannan canjin ya wuce alama yana nuna dabi’un mu a matsayin...
    Dubban ’yan Nijeriya ne ke zaune a ƙasar Saudiyya ba tare da takardun izinin zama ba, musamman a biranen Makkah da Madina. Rayuwarsu cike take da fargaba da rashin tabbas, a yayin da suke yin ayyukan hannu ko ƙananan sana’o’i ba tare da wata kariya ta doka ba. A yayin aiki Hajjin shekarar nan ta 2025, wakilimmu ya samu yin hira da wasu ’yan Nijeriya da ke zaune a can — waɗanda aka fi sani da Takari — inda suka bayyana masa yanayin rayuwarsu sa iliminsu da tsarin matsuguninsu da yanayin aikinsu da rayuwar ’ya’yansu da wasu ƙalubale na fargabar kame da rushe gidajenau, da ma ra’ayinsu kan komawa Nijeriya da sauransu. Ameera, wata ’yar Najeriya da ke zaune...
    Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kwamitin sulhun Majalisar ya rasa damar tattaunawa da fahimtar juna a yau Jakadan kasar Iran kuma wakilin din-din-din a Majalisar Dinkin Duniya Amir Sa’ed Irawani, ya yi tsokaci kan rashin amincewa da daftarin kudiri na ci gaba da dage takunkumin da aka kakabawa Iran a taron kolin na yau, sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Turai. Irawani ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhun a jiya Juma’a cewa: Kwamitin sulhun ya yi watsi da damar tattaunawa da fahimtar juna, yayin da Rasha da China bisa gaskiya suka gabatar da wani madaidaicin kudiri na tsawaita kudurin Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2231 da kiyaye tsarin diflomasiyya. Ya ce: “Maimakon amincewa da...
    1- Musayar yawu ta hanyar sumbatar juna- Ma’ana, ta hanyar sumbatar juna a tsakanin ma’aurata, idan guda daga cikinsu na ɗauke da cutar, nan da nan ɗayan shi ma zai kamu da cutar. 2- Gaurayewar jini ko haɗuwar jini- Haɗuwar jini, misali; idan wani ya yi amfani da reza ya yanke, ɗayan ya yi amfani da ita, zai iya kamuwa da cutar, ko kuma wani abu maikama da haka. 3- Ɓangaren saduwa a tsakanin ma’aurata- A wajen saduwa tsakanin mata da miji, ta hanyar haɗuwa maniyyi ko maziyyi da sauran makamantansu, wannan cuta za ta samu hanyar shigewa nan take da ɗaya daga cikinsu na ɗauke da ita. Don haka, waɗannan hanyoyi da aka ambata dukkanninsu na iya faruwa a...
    Firaministan kasar Sin Li Qiang, zai halarci babban taron mahawara na MDD karo na 80 a birnin New York na kasar Amurka, tsakanin ranakun 22 zuwa 26 ga watan Satumban nan. A cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, firaminista Li, zai kuma halarci wasu ayyuka da Sin za ta shirya, ciki har da taron manyan jami’ai dangane da shawarar bunkasa ci gaban duniya da Sin ta gabatar, kana zai gana da babban magatakardar MDD, da jagororin kasashe masu ruwa da tsaki kan batun. (Saminu Alhassan)     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    A yau Juma’a shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Donald Trump. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce jam’iyyarsa a shirye ta ke, ta haɗa kai da APC, idan an shirye karɓar sharuɗansu. Kwankwaso, ya faɗi haka ne a gidansa da ke Miller Road a Kano, lokacin da ya karɓi baƙuncin tsohon jigon APC a jihar, Buhari Bakwana, tare da wasu jiga-jigai. Babu wani hari da aka kai sakatariyar NUJ a Yobe — ’Yan Sanda An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Ya bayyaa musu yadda shi da wasu ’yan siyasa wajen kafa jam’iyyar APC a 2013 kuma sun sha wahala kafin kafuwarta. “Babu wanda zai faɗa min irin wahalar da muka sha wajen kafa APC....
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe, ta ƙaryata rahotannin da ke nuna cewar an kai hari sakatariyar ƙungiyar ’yan jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu. Wannan na cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Juma’a. An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce abin da ya faru shi ne wani jami’in tsaro da ke gadin wajen ne ya samu rauni a ƙafarsa ta hagu. A cewarsa, raunin ba shi da alaƙa da harbin bindiga, kamar yadda wasu shafukan Internet suka wallafa. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:45 na daren ranar...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya ziyarci iyalan tsohon Shugaban Ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari a Jihar Kaduna bayan halartar ɗaurin auren ɗan tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari. Da zuwansa, Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, da ɗan marigayin, Yusuf Buhari, tare da wasu suka tarbe shi. Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Game Da Bunkasa Ci Gaban Mata An Dakatar Da Shugabannin Makarantun Sakandire 6 A Sakkwato Kan Rashin Bin Dokokin Aiki Shugaba Tinubu ya gana da uwargidan marigayin, Aisha Buhari, da sauran ‘ya’yansa, inda ya sake yi musu ta’aziyya. Ya kuma tabbatar wa Aisha Buhari cewa zai ci gaba da kula da ayyukan alheri Buhari ya bari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona al’aurar ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
    Wata mata mazauniyar garin Magama Gumau a Ƙaramar Hukumar Toro, Jihar Bauchi, ta shiga hannun ’yan sanda biyo bayan ƙona farjin ’yarta mai shekaru 10 kacal a duniya, kan zargin maita. Rahotanni sun nuna cewa matar ta yi amfani da cokali ta hanyar sanya shi a wuta ya yi zafi sannan ta umarci ’ya’yanta biyu suka riƙe yarinyar sannan ta ƙona ta. Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe Wannan ya jefa yarinyar cikin mawuyacin hali, inda ta ke fama wahalar yin fitsari da bayan gida. Bayan lamarin ya faru, maƙwabta sun kai ƙarar matar wajen ’yan sanda. An garzaya da yarinyar zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa...
    Rundunar ƴansanda a Jihar Bauchi ta tabbatar da kama wata mata, wadda ake zargi da yi wa wata yarinya ‘yar shekara bakwai mummunan rauni ta hanyar ƙona mata al’aura da wuka mai zafi a garin Magama Gumau, ƙaramar hukumar Toro. Rahotanni sun ce matar ta zargi yarinyar da maita, lamarin da ya sa ta yi amfani da wuka da aka zafafata a wuta wajen ƙona jikinta. Ihun yarinyar ne ya jawo hankalin maƙwabta, inda suka yi gaggawar zuwa suka ceceta tare da sanar da ‘yansanda. Gwamnan Bauchi Ya Gargaɗi Magoya Bayan Wike A PDP An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi Wani mai fafutukar kare haƙƙin yara a yankin, Kabiru Mohammed Abdulkadir, ya...
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dawo bayan shafe tsawon lokaci baya jihar biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da  Shugaba Tinubu ya yi. A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wadda tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas (rtd), ya jagoranta. ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki Magoya bayan gwamnan sun taru a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal domin tarbarsa bayan dakatar da shi na tsawon watanni shida, amma daga baya suka watse bayan shafe lokaci suna jira ba tare da ganinsa ba. Da safiyar ranar Juma’a, magoya bayan suka koma Filin Jirgin Sama na Fatakwal. Jirgin...
    Matasa takwas a jihar Jigawa sun lashe tallafin kasuwanci na Naira miliyan biyu daga British Council ƙarƙashin shirin Youth Connect. Kowane ɗaya daga cikinsu ya samu Naira dubu dari biyu da hamsin domin fara ayyukan kasuwanci. An gudanar da shirin ne tare da haɗin gwiwar Kings Trust International, CITAD, da gwamnatin jihar Jigawa. Matasa tamanin aka horas a tsawon makonni takwas kan kasuwanci, fasahar zamani da kuma ƙwarewar tallatawa, inda daga cikinsu guda takwas suka fito a matsayin zakaru. Wakilin British Council, Dr. Yahaya Janga, ya shawarci matasan da su yi amfani da horon da suka samu da kuma tallafin wajen kafa kasuwanci mai dorewa. Ya kuma yaba wa gwamnatin Jigawa da sauran abokan hulɗa da suka tallafa...
    Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da sanyin safiyar Juma’a. Rahotanni sun ce yayin harin, maharan sun harbi wani jami’in ɗan sanda da ke gadin sakatariyar suka ji masa rauni ƙafa. An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda maharan suka buɗe wuta. Shugaban ƙungiyar NUJ reshen jihar, Rajab Ismail Mohammed, ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali da kuma babbar barazana ga lafiyar ’yan jarida...
    A yau a Nijeriya, kalmar “Japa” ta zama gamagari wajen bayyana yadda matasa da dama ke barin ƙasar domin neman ingantacciyar rayuwa a wasu ƙasashe. Abin da ya bambanta shi yanzu shi ne inda suke nufa: ba kawai Turai da Amurka ba kawai, har ma da ƙasashen Afirka maƙwabta. Yawaitar tsadar rayuwa da ƙarancin ayyukan yi da rashin tsaro, da kuma faɗuwar darajar Naira sun sanya matasa su fara duba wasu ƙasashen Afirka a matsayin mafaka. Mutum 1,666 ne suka kashe kansu a Legas cikin shekaru biyar – ’Yan sanda Akasarin masu kai mana hare-hare daga jihohin da suka kewaye mu suke – Gwamnatin Filato Maimakon tsallaka tekun Bahar Rum da haɗarin mutuwa, da dama daga cikinsu sun fara kallon...
    Mutane da dama na nuna damuwa game da mmakomar ayyukansu tun bayan fitowar fasahar AI.   Sai dai yayin da wasu manazarta suke ganin fasahar za ta raba mutane da ayyukansu, wasu kuwa gani suke yi wannan ba abu ne mai yiwuwa ba. NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Shirin Najeriya A Yau na wanna lokaci zai yi nazari ne kan sayyukan da fasahar AI za ta iya raba mutane da su. Domin sauke shirin, latsa nan
    Ina gaida Mahaifiyata da Mahaifina, Hajiya Saratu da Alhaji Aliyu Minjibir. Sai Gidana Alhaji Musa Yusuf, sai aminiyata Hajiya Kubra Bashir Abdullahi, sai Ƴa ta Mariya, da ƙannena Rashida Aliyu Minjibir, Zainab Aliyu Minjibir, Aliya Aliyu Minjibir, Aliyu Aliyu, Abubakar Aliyu Minjibir Muhammad Aliyu Minjibir, da fatan sun yi juma’a lafiya. Saƙo daga Maryam M. Aminu  Saƙon gaisuwata zuwa ga Babata da Babana, sai ƙawayena kamar su; Nawal, Zee-zee Kwalale, Halima Saleh, Fatima Kabir, Maryam Isma’il (Namesake), Keleri. Sannan ƴ an’uwana Yaya, Muhammad, Iman, Al-Amin(TK),  Ummulkhurthum, Jawad, Zainab Aminu, Abba, Abdulrahman, Jawahir, Fatima. Saƙo daga Muhammad Abdullah, Unguwar Fagge Jihar Kano: Ina gaishe da mahaifiyata da mahaifina dan ba zan fara ba sai na fara da su, sannan ina gaishe...
    Kwamitin tsaro na MDD a jiya Alhamis 18 ga watan Satumba, ta kasa samun wani kuduri wanda kenufin tabbatar da zaman lafiyaa gaza da kuma tsagaita wuta a dai-dai lokacinda gwamnatin kasar Amurka wacce take da hakkin hawan kujeran na ki wato Veto ta haka kudurin wucewa. Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto dan rahotonta a NewYork yana  cewa dalilan da gwamnatin Amurka ta bayar na hana wannan kudurin wucewa sun hada da abinda ta kira rashin yin allawadai da kungiyar Hamas da kuma da kuma ambatun hakkin HKI na kare kanta a gaban hamas. Kafin haka dai ta sami amincewar dukkan sauran mambobin kwamiton tsaron 14. Jami’an diblomasiyya sun bayyana cewa, ba wannan ne karon farko...
    An sabunta wannan ƙididdiga kusan shekaru shida kamar yadda ya kamata a yi. Abin da ya kamata mu mai da hankali a kai shi ne, ƙididdiga da bayanai su kasance masu sahihanci kuma a yawaita samun su. “An sabunta ƙididdigar, kuma ya nuna mana ainihin halin da muke ciki. Don haka, duk wani ra’ayi na son zuciya da wani ke ganin ya kamata mu kasance kusa da kashi 30, wannan ra’ayinsu ne kawai. Muhimmin abu shi ne an sabunta ƙididdiga watanni da dama da suka wuce, kuma abin da muke gani yanzu shi ne raguwar hauhawar farashi da ta ci gaba.” Fasua ya kuma ambaci cewa Naira ta samu tagomashi a kwanakin baya kuma farashin mai na hauhawa a kasuwar...
    Najeriya ta tabbatar da shirinta na karɓar Wasannin Kungiyar Kasashen Renon Ingila na 2030, inda za ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta kafa wannan tarihi tun 1930. Shugaba Bola Tinubu, ta bakin Shugaban Ma’aikatansa Femi Gbajabiamila, ya ce gwamnati ta ba da cikakken goyon baya, ta kuma shirya samar da dukkan abubuwan more rayuwa, tsaro da masauki kafin lokaci. A jawabansu daban daban, Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa Shehu Dikko da Shugaban Kungiyar Wasannin Renon Ingila Habu Gumel, sun bayyana cewa Najeriya ce damar Afirka mafi cancanta, yayin da kwamitin neman karɓar gasar ya gabatar da shirin gudanar da wasanni 15, ciki har da kwallon ƙafa. Najeriya da Indiya ne ke neman karɓar gasar, inda za a...
    Kazalika, masu sukar na ganin cewa, gwamnatin ta yi watsi da irin halin ƙuncin rayuwa da musamman talakwan ƙasar, ke ci gaba da fuskanta, kamar dai, na ci gaba da hauhawan farashin kayan masarufi da ƙarin kuɗin Man Fetur da ƙarin kuɗin wutar lantarki da ƙarancin albashin da ake biyan ma’aikata, musamman na gwamnati, wanda a baya, ta yi alƙawarin lalubo masu da mafita. Wannan batun na ƙarin albashin, tamkar dai wani cin zarafi wanda kuma abu ne, da ke tattare da hatsari. Kusan tun lokacin da shugaba Bola Tinubu, ya ɗare Karagar shugabancin ƙasar, ya rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa, na gudanar da mulki, inda gwamtainsa, ta rage yawan ɗimbin tawagar da take kwasa, na yin tafiye-tafiye, musamman...
      A ranar 18 ga watan Satumban shekarar 1931, sojojin Japan suka tarwatsa wani sashi na layin dogo dake karkashin ikonsu, a kusa da birnin Shenyang, tare da zargin sojojin kasar Sin da aikata barna, domin su fake da hakan wajen kai hari barikin sojojin Sin dake kusa da birnin na Shenyang a daren ranar, da kuma hakan ne suka kaddamar da mamayar da suka kitsa cikin kasar Sin. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A baya bayan nan, tawagar likitocin kasar Sin ta 24 dake aikin agajin kiwon lafiya a janhuriyar Nijar, ta gudanar da tiyatar ALT irinta ta farko da aka yi nasarar gudanarwa a yankin yammacin Afirka. An gudanar da tiyatar ne a babban asibitin gwaji na kasar ta Nijar. Kuma ana gudanar da tiyatar ALT ne ta hanyar yankar wasu sassan fata da tsokar cinyar mara lafiya, domin dasawa a wasu sassan jikinsa da suka lalace sakamakon wata matsala. Ana kallon nasarar da aka samu ta aiwatar da wannan tiyata a Nijar, a matsayin nasarar da za ta cike gibin da ke akwai a fannin, a yankin yammacin Afirka. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya amsa tambayar da aka yi masa game da fara nuna fim din kasar Sin mai taken 731 a sassan kasar, inda ya ce, irin wannan fim na tunatar da jama’a muhimmancin koyon darussa daga tarihi, da kokarin wanzar da zaman lafiya. Kakakin ya ce, Sin kasa ce dake bude kofa ga kasashe waje, kuma mai hakuri da tsaro. Ana maraba da jama’ar sassan kasa da kasa, ciki har da na Japan, su shigo kasar Sin don yin yawon bude ido, da karatu, da kasuwanci da kuma rayuwa. Haka kuma, Sin za ta ci gaba da tabbatar da tsaron baki ’yan kasashen waje dake zaune a sassanta. (Murtala Zhang)...
    Benfica ta sanar da naɗa José Mourinho a matsayin sabon kociyanta, domin maye gurbin Bruno Lage, wanda ƙungiyar ta karo bayan da Qarabag ta doke ta a gasar Zakarun Turai ranar Talata. Benfica ta kori Lage duk da cewa wasa ɗaya kawai ya yi rashin nasara a dukkanin gasa a bana. Wata sanarwa da Benfica ta fitar a ranar Alhamis ta bayyana cewa, Mourinho mai shekaru 62 zai jagoranci ƙungiyar har zuwa kakar wasanni ta 2026/2027, tare da zaɓin raba gari a ƙarshen kakar nan. An yanke wa Soja hukuncin kisa ta hanyar rataya Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar Tsohon kociyan Chelsea, Real Madrid da Manchester United, ya dawo Benfica ne bayan ya rasa aiki a...
    Kotun ta kuma samu Musa da mallakar harsashi na musamman har guda 34 mai nauyin (7.62mm) ba bisa ƙa’ida ba.   Ga laifin kisan kai, sashe na 220 na kundin laifuffuka da kuma hukuncin da ke karkashin sashe na 221, Musa an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya. A laifi na biyu na mallakar harsasai ba bisa ka’ida ba, sashe na 8 (1) na dokar bindigogi, an yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru biyu a gidan yari. Bugu da ƙari, an kore shi daga aikin sojan Nijeriya acikin ƙasƙanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Wata babbar kotun sojin Najeriya da ke zamanta a sansanin sojoji ta Maxwell Khobe da ke garin Jos a Jihar Filato ta yanke wa wani soja mai suna Lukman Musa hukuncin kisa ta hanyar rataya. An yanke wa Musa hukuncin kisa ne a ranar Alhamis bayan da aka same shi da laifuka biyu kan kisan gilla da aka yi wa wani direban babur mai ƙafa uku mai suna Abdulrahman Isa a garin Azare na Jihar Bauchi. Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu Daily Trust ta ruwaito cewa, an fara shari’ar Musa ne a farkon watan Agustan 2025 bayan kama shi biyo bayan binciken haɗin gwiwa da...
    Dong Jun ya bayyana haka ne yayin taruka daban-daban da ya yi da shugabannin rundunonin tsaro na kasashen Malaysia da Cambodia da Myanmar da Namibia da Rwanda da Senegal, wadanda dukkansu ke birnin Beijing domin halartar taron dandalin tsaro na Xiangshan karo na 12. Da yake yi musu maraba, Dong Jun ya ce taron na wannan karo na da matukar muhimmanci ga tarihi. Ya kara da cewa, a shirye rundunar sojin Sin ta ke ta ci gaba da raya dadaddiyar abotar dake tsakaninta da dukkan bangarori wajen karfafa tuntubar juna da hadin gwiwa kan tsaro, da hada hannu wajen tunkarar hadura da kalubale a duniya. Yayin tarukan, dukkan ministocin tsaron kasa da kasa da suka halarci taron, sun bayyana kudurinsu...
    A yau Alhamis ne ne aka kai wasu hare-hare biyu na suka da wuka akan mashigar ‘al-karamah’ dake kan iyakar Falasdinu da Jordan. Majiyar ‘yan sahayoniya wacce ta ambaci labarin ta kuma ce; A matakin farko an kai hari ne ta hanyar bude wuta da bindiga akan sojoji, sannan aka kai wani harin ta hanyar sara da wuka. Harin ya yi sanadiyyar kashe sojoji biyu da kuma jikkata wasu da dama. Jim kadan bayan kai wannan harin ne dai,sojojin HKI su ka killace yankin baki daya domin yin bincike. A cikin watan Satumba an kai wani harin irin wannan wanda ya yi sanadiyyar halakar ‘yan sahayoniya 3 da kuma jikkata wasu da dama. Wannan harin na ‘yan gwagwarmaya ya zo...
    Bayanai na cewa, wannan munduwa mai ɗimbin tarihi, mallakin Fir’auna Amenemope ne, yayin da ta yi ɓatan-dabo a gidan tarihin da ake adana da ita. An rarraba hoton munduwar zinarin ga jami’an da ke aiki a kan iyakokin ƙasar daban-daban da suka haɗa da filayen jiragen sama da tashohin jiragen ruwa da zummar daƙile fasaƙaurinta zuwa ƙetare. ’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa Munduwar mai ɗauke da ado na musamman, na da matuƙar daraja tun zamanin Fir’aunan, yayin da ake danganta ta da tsofaffin gumakan da aka yi bautar su a can baya, sannan an ce tana da ƙarfin warkarwa. Munduwar na cikin jerin kayayyakin...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) tare da haɗin gwiwar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF sun shirya horar da aikin ceto yayin ambaliya,  a Ƙaramar Hukumar Auyo. Taron horaswar ya haɗa masu ruwa da tsaki daga hukumomi daban-daban, inda aka bai wa mahalarta ƙwarewa da ilimin da ya dace domin samun nasarar ceto da kuma kai dauki ga al’ummomin da ambaliya ta shafa. A yayin horon, an gudanar da darussa kan dabarun bincike da ceto, bayar da taimakon farko, da hanyoyin kwashe jama’a daga wuraren da ambaliya ta shafa. Wannan shiri ya nuna jajircewar SEMA, NEMA, da UNICEF wajen horar da...
    Hukumar Kididdiga ta kasar Sin ta samar da alkaluman tattalin arziki na watan Agusta a kwanan nan, alkaluman da suka nuna cewa, tattalin arzikin Sin yana ci gaba da bunkasa ba tare da tangarda ba, musamman a fannin sana’o’in ba da hidima, inda ma’aunin ISP game da ayyukan ba da hidima ya karu da kashi 5.6% idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar da ta gabata. Abin lura shi ne, a matsayin wani muhimmin bangare na sana’o’in ba da hidima na zamani, sana’ar al’adu ita ma tana nuna gagarumin ci gaba. A taron dandalin kasa da kasa kan harkokin al’adu na “Golden Panda” da aka gudanar kwanan nan, ministar fasaha, al’adu, yawon bude ido da tattalin arzikin kirkire-kirkire ta Najeriya,...
    A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma’aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki. Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala taro na musamman da shugabannin sassa na hukumar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar. Yayi bayanin cewar, hukumar zata bada bitar ne ga jami’an da kuma shugabannin shiyya-shiyya kan hanyoyin kara kula da walwala da jin dadin maniyyata da kuma dabarun magance kalubale yayin gabatar da aikin hajji. Yana mai cewar bada horo na da matukar mahimmaci duba da yadda...
    Hukumar bunkasa ilimin gaba da sakandare ta jihar Jigawa ta shirya taron tattaunawa ga jami’an gudanar da shirin koyawa dalibai musamman wadanda suke da nakasu a jarrabawar NECO ko WAEC wato Remedial program don su sami nasarar cin jarrabawar da za ta basu damar ci gaba da karatu a makarantun gaba da sakandare. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban hukumar, Dr Abbas A Abbas ya bayyana cewar gwamnatin jihar jigawa karkashin jagorancin Malam Umar Namadi ta sahalewa hukumar gudanar da shirin da ta saba yi duk shekara wajen baiwa daliban da suka fadi a jarrabawar NECO ko WAEC koyarwa ta musamman. Yana mai cewar, sahalewar na da nufin basu damar sake rubuta jarrabawar don su sami dukkanin abun da...
    Rundunar ‘yan Sandan Jihar Jigawa ta bada sanarwar nasarar cafke wani sojan bogi da ƙarin wasu mutum biyu da ake zargi da satar mota a ƙauyen Sabon Sara. Kamar yadda Kakakin rundunar ’yan sanda na Jigawa, SP Shiisu Lawan Adam ya sanarwa manema labarai a garin Dutse cewa, an kama matashin sojan bogin da abokansa da ake zargin su da satar mota a ƙauyen Sabon Sara, cikin ƙaramar hukumar Kafin Hausa. Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin minista Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya A cewar majiyar an kama sojan bogin mai suna Kabiru Musa da abokan aikinsa Umar Ali da Sabi’u Bashir, dukkansu ‘yan asalin Jihar Kano. A cewar kakakin rundunar waɗannan...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa lokacin da take kokarin tserewa daga harin ’yan bindiga a ƙauyen Allawa da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta Jihar Neja. Hakkin ya fito ne daga bakin Hakimin Bassa, Bagudu Amos, yayin wani taron tattaunawa da mata kan rikici da zaman lafiya mai taken: “Ƙarfafa Matakan Kare Fyade da Cin Zarafin Mata a Jihar Neja”. Gwamnatin Gombe ta gyara hanyoyin kiwo domin daƙile rikicin manoma da makiyaya HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara Taron dai wata kungiya mai zaman kanta mai suna Tunani Initiative ce ta shira shi, tare da hadin gwiwar gidauniyar Dorothy Njemanze Foundation da kuma gidauniyar Foundation, domin ƙarfafa gwiwar mata wajen magance cin zarafin jinsi...
    Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis. Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar. Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m Sai dai a ranar Laraba, Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci tare da umartar gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar da su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba. A halin yanzu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya miƙa mulki...
    Gwamnatin mamayar Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare kan Gaza a rana ta 713 a daidai lokacin da kasashen duniya ke shiru Sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza a rana ta 713, inda suke ci gaba da yin amfani da ruwan bama-bamai ta sama da na bindigogi, inda suka kashe mutane da ke fama da yunwa da rashin muhallan, tare da goyon bayan siyasa da soji na Amurka, gami da shirun kasa da kasa, da gazawar da ba a taba gani ba daga kasashen duniya. Sojojin mamayar Isra’ila sun kaddamar da hare-hare da dama ta sama tare da aiwatar da kisan kiyashi, lamarin da ya ta’azzara wahalhalun da mutane sama da...
    Gwamnatin jihar Kano ta aika dalibai 588 zuwa jihohin Arewa 13 a karkashin shirin musayar dalibai na shekarar 2025/2026.   An kai daliban zuwa jihohinsu da suka hada da Adamawa, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina, Kebbi, Taraba, da Nasarawa. Bugu da kari, an kai dalibai daga Yobe, Kaduna, Sokoto, Borno, da Kwara lafiya zuwa inda suke, yayin da wasu dalibai 78 kuma za a kwashe su zuwa jihohin Neja da Benue a ranar 30 ga Satumba, 2025.   Kano dai na daya daga cikin jihohin Arewa 19 da ke halartar wannan shiri, wanda aka tsara shi domin inganta hadin kan kasa, hadewa da fahimtar al’adu tsakanin jahohin mambobin kungiyar.   Da yake jawabi ga manema labarai bayan tafiyar da daliban, kwamishinan...
    Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan asarar rayuka da aka yi a gobarar da ta tashi a ranar Talata a Afriland Towers da ke Broad Street, a  Legas.   A cikin wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma hukumomi da ma’aikatan hukumar tara haraji ta tarayya (FIRS), United Capital, United Bank for Africa (UBA) Plc, da kuma Afriland Properties Limited.   Ya kuma jajanta wa wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan bala’in, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.   Shugaba Tinubu ya yaba da matakin da hukumomin gaggawa...
    Ya jaddada cewa dakarun tsaron Nijeriya suna da ƙarfin da za su iya fatattakar ’yan ta’adda, amma abin da ya rage shi ne samun ingantaccen shugabanci da ƙwarin gwiwa daga fadar shugaban ƙasa. Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin ceto ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziƙi ya kamata su zama fifiko. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziƙi, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa Naira biliyan 330 a matsayin tallafi. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, inda ya ce an raba kuɗin ne ta Ofishin Tsare-tsaren Jin-ƙai na Ƙasa (NASSCO), domin rage wa talakawa wahalar cire tallafin mai da sauyin musayar kuɗaɗen waje. An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m A cewarsa, aƙalla gidaje miliyan 19.7 (sama da mutum miliyan 70) aka sanya a Rajistar Tsarin Tallafa Wa Talakawa, kum tallafin ya kai ga gidaje miliyan 15. “Zuwa yanzu, gidaje miliyan 8.5 sun samu aƙalla Naira...
    Masu bincike a Turai sun yi amfani da fasahar ƙirƙirariyyar basira ta AI don yin hasashen matsalolin lafiya da ɗaiɗaikun mutane za su iya fuskanta cikin shekaru goma masu zuwa ko fiye na rayuwarsu. Sun ce fasahar na amfanin da bayanan rashin lafiyar da mutum ya yi a baya, domin hasashen cutuka fiye da dubu ɗaya da ke barazanar kama mutum, tun ma kafin soma bayyana. An wallafa cikakkun bayanan binciken – da suka bayyana da gagarumar nasara – a mujallar kiwon lafiya ta Nature. An horar da fasahar AI ɗin ta hanyar amfani da bayanan lafiyar mutane dubu ɗari huɗu – da ba a bayyana sunayensu ba – a Birtaniya da Denmark. Zuwa yanzu ba a soma amfani da...
    Gwamnatin Jihar Zamfara ta roki Hukumar Raya Kasashen Waje ta Kasa (FCDO), Premier Urgence Internationale (PUI), da sauran masu ruwa da tsaki da su kara tallafa wa ‘yan gudun hijirar da ke jihar.   Kwamishinan Bada Agaji na Jiha Alhaji Salisu Musa Tsafe ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron na kwana guda kan shirin ceton rayuka da karfafawa da kuma juriya (LEARP) wanda kungiyar FCDO ta dauki nauyin shiryawa a Abuja.   A wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Bashir Kabiru Ahmad, Kwamishinan ya bayyana cewa a halin yanzu jihar na karbar dubban ‘yan gudun hijira daga al’ummomi sama da 1,008 a fadin kananan hukumomin 14, kamar yadda...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da DSS sun kashe ’yan ta’addan ƙungiyar IPOB da yawa. Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce tawagar ta lalata sansanonin IPOB a yankin Ezioha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, da kuma a Umuele, Ubuakpu, da Amakor a Ƙaramar Hukumar Njaba. ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? Ya ce da yawa daga cikin mambobin ƙungiyar sun mutu yayin samamen, wasu kuma an kama su, yayin da wasu suka tsere da raunuka. Okoye, ya ƙara da cewa an gano bindigogi da harsasai da dama a...
    Uwargidan shugaban kasar Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira da a kara fahimtar juna a tsakanin kasashe tare da yin addu’ar samun zaman lafiya a duniya a yayin da ake fama da rikice-rikice a duniya.   Ta yi wannan kiran ne a lokacin da ta karbi bakuncin jakadan Qatar a Najeriya Ali bin Ghanem Al-Hajri a ofishinta da ke Abuja. Uwargidan shugaban kasar, yayin da take mayar da jawabi game da harin da aka kai a birnin Doha na baya-bayan nan, ta jaddada cewa, zaman lafiya, kamar yadda manyan addinai ke wa’azi, muhimmin abu ne ga bil’adama, kuma ya kamata ya kasance muhimmin fifiko ga dukkan kasashe.   Tattaunawar da aka yi a yayin ziyarar, wadda ta kasance a...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar wa kungiyar mafarauta/Yanbulala reshen jihar Jigawa na rundunar a shirye ta ke ta shirya wani horo na kara musu karfin gwiwa ga mambobinsu.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Dahiru Muhammad ya bayar da wannan tabbacin ne a yayin wani taro da aka yi da mafarauta/Yanbulala na yankin wanda Lamido Wada ya jagoranta a Dutse babban birnin jihar.   Ya bayyana cewa, Rundunar za ta hada gwiwa da wadanda abin ya shafa domin fuskanatar kalubalen zirga-zirga don daukar matakin da ya dace.   A cewarsa, rundunar ta ci gaba da  shirye-shiryen ‘yan sanda da al’umma ke tafiyar da su ta hanyar samar da hadin gwiwa mai karfi da masu ruwa da tsaki da suka himmatu...
    Shugaban Hukumar Nukiliya ta Iran ya ce barazanar da makiya Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke ci gaba da yi tun bayan harin ba-zata da Isra’ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin nukiliyar kasar, na kara nuni da cewa dole ne hukumar IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai, ba wurin aiwatar da siyasar adawa da kasar Iran ba. Mohammad Eslami, wanda shi ne shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na Kyodo na Japan a wata rubutacciyar hira da aka buga a ranar Laraba. Ya kara da cewa halin da ake ciki na tsaro na cikin hadari, domin kuwa yanayi da ya yi kama da lokacin yaki saboda irin barazana da...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda da aiwatar da wannan harin ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a ranar 17 ga Satumba, 2024. “Ku ne masu gani na gaskiya, tushen begenmu, kuma sadaukarwar ku ga Allah ita ce ke ba wa rayuwa ma’anarta ta har abada, ku ne hasken da ke shiryar da mu domin bin hanya, kuma juriyarku ita ce zuciyar juriyarmu,” in ji Sheikh Qassem a cikin sakonsa ga mutanen da suka jikkata a harin. “Me zan iya ce muku? Don yanzu ku ne malamai, masu ba da shawara, ku ne jagorori, saboda kun yi sadaukarwa kuma kuna a kan yi,...
    Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran a wata ganawa da takwaransa na kasar Masar ya bayyana cewa: Iran da Masar sun mallaki wasu al’adu guda biyu masu cike da tarihi masu alfahari da fa’ida, kuma fadada hadin gwiwar da ke tsakaninsu zai kara taimakawa wajen tabbatar da moriyar al’ummomin kasashen biyu da ma sauran al’ummomin yankin. Babban labarin jaridar Pars Today na cewa, Shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian a yau litinin a ci gaba da tarukan da yake yi a gefen taron gaggawa na kasashen musulmi da kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a birnin Doha na kasar Qatar ya gana da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sisi. Da take bayyana fatan gaggauta kulla alaka a tsakanin kasashen biyu, Pezeshkian...
    Dan wasan kokawa mai nauyi na Iran ya samu lambar zinare ta farko a gasar cin kofin duniya. Wasan karshe da na rarrabuwar kawuna na manyan nau’ikan nau’ikan nauyi hudu na gasar kokawa ta duniya da aka yi a yammacin Lahadi a Zagreb. A cewar Pars Today, Amirhossein Zare daga Iran wanda ya taba zama zakaran duniya sau biyu kuma ya samu lambar azurfa da tagulla a gasar Olympics, ya fafata da Georgi Meshvildishvili, wanda ya samu lambar tagulla daga gasar Olympics ta Paris da ke wakiltar Azarbaijan a wasan karshe. Zare ya yi nasara da ci 5-0, inda ya samu lambar zinare ta uku a gasar cin kofin duniya. Bugu da kari, a wannan gasar, Ahmad Mohammadzadeh Javan dan...
    Wani ɗan kasuwa a Jihar Katsina mai suna Anas Ahmadu da matarsa, Halimatu wadda ke ɗauke da juna biyu, da kuma ’yarsu mai shekaru biyu, sun kuɓuta daga hannun ’yan bindiga, bayan sun shafe kwanaki 21 a hannunsu. An sako su ne a daren ranar Laraba bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 50, kamar yadda wani ɗan uwansu ya bayyana wa Aminiya. Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? “Alhamdulillah! Anas, Halimatu da ’yarsu sun kuɓuta. Yanzu haka suna kan hanyarsu ta zuwa gida, amma sai da aka biya ’yan bindigar kuɗin fansa Naira miliyan 50,” in ji shi. An sace su ne a...
    Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta ce ma’aikatanta hudu sun mutu a gobarar da ta tashi a ginin Afriland Towers da ke titin Broad da ke Legas, a ranar Talata. Aminiya ta rawaito yadda gobara ta mamaye ginin da ke dauke da banki, hukumomi da wasu kamfanoni. Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas? A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, mai magana da yawun Shugaban FIRS, Zaach Adedeji, wato Dare Adekanmbi, ya ce hukumar na cikin jimami da alhini kan rasuwar ma’aikatan nata. Sanarwar ta ce, “Cike da alhini da bakin ciki, FIRS na sanar da rasuwar ma’aikatanta...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar.   Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kamar yadda ya barta, wasu kuwa gani sukeyi akwai babban kalubale dake gaban gwamnan. Domin sauke shirin, latsa nan
    A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma. Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar. A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin. Yayin mika kayayyakin ga mai...
    Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya shirya taron manema labarai a yau 17 ga wata, inda aka bayyana cewa, tun daga fara aiwatar da shiri na 14 na shekaru 5 na raya kasa, wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, karfin kamfanoni mallakar gwamnati ya kara karuwa, kuma jimillar kadarorinsu ta wuce yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da dalar Amurka tiriliyan 12.6. Darektan kwamitin sa ido kan kadarori mallakar gwamnati na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Zhang Yuzhuo ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 har zuwa yanzu, jimillar kadarorin kamfanoni mallakar gwamnati ta karu daga kasa da yuan tiriliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka kimanin tiriliyan 10, zuwa sama da yuan tiriliyan 90, kwatankwacin sama da...
    Gwamnan Sakkwato, Dakta Ahmad Aliyu, ya ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani guda 20, tare da riguna ruwa (life jackets) 2,000, domin rage haɗurran da ke aukuwa sakamakon ambaliya da nutsewar jirage a sassan jihar. An ƙaddamar da jiragen ne a ƙaramar hukumar Wamakko a ranar Laraba, inda gwamnan ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin shirin gaggawa na tallafa wa al’ummar da ke fama da illar ambaliya da haɗurra a ruwa. Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB “Mun dauki wannan mataki bayan rahotannin da muke samu na yawaitar hatsarurruka da rasa rayuka da dukiya sakamakon jiragen katako da mutane ke amfani da su,” in ji Gwamna Ahmad...
      Wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Folasade Boriowo, ya fitar, ta ce a karon farko cikin shekaru da dama, daliban Nijeriya za su ci gaba da karatun tarihin Nijeriya tun daga Firamare 1 zuwa karamar Sakandare 3 yayin da daliban SSS 1 – 3 za su koyi sabon darasin da aka samar na ‘Civic and Heritage Studies’, wanda ya hada tarihin Nijeriya da Ilimin zamantakewar Jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce alkaluman baya bayan nan da aka fitar cikin Mujallar Economist, sun shaida yadda hada-hadar cinikayyar fitar da hajoji ta kasar Sin ke kara bunkasa cikin sauri a shekarar nan ta bana, inda fannin ke samun karuwar abokan hulda, da daidaiton matsayi cikin tsarin samar da hajojin masana’antu na kasa da kasa. Kakakin ya kara da cewa, kasashen duniya suna maraba da hajojin kasar Sin, kuma yakin ciniki da haraji ba su yi wani babban tasiri kan kasar Sin ba. A fannin hada-hadar cinikayya, sanya shinge ba alama ce ta karfin gwiwa ba, kuma katangar da Amurka ke ginawa kanta, daga karshe za ta illata karfinta ne. Lin Jian, wanda ya...
    Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na  jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse. Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci. Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa. Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci...
    Kamfanin Microsoft ya sanar da ƙwace shafukan yanar gizo na wasu kamfanoni 340 a Najeriya bayan samunsu da laifin sarrafa fasahohin kamfanin ba bisa ƙa’ida ba, musamman satar bayanan mutane. Sanarwar da Microsoft ya fitar ta ce matakin ya biyo bayan wani umarni da wata kotu a Amurka ta bayar tun a farkon wannan wata, wadda ta bai wa kamfanin damar ɗaukar matakin ladabtarwa ga waɗanda ke amfani da fasaharsa ba tare da izini ba. An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Steven Masada, mataimakin shugaban sashen lauyoyi na Microsoft da ke kula da laifukan intanet, ya bayyana cewa waɗannan kamfanoni sun ɗauki bayanan abokan hulɗarsu sama da 5,000,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin. A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya. Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince...
    Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da samun nasarar cafke Ifeanyi Eze Okorienta, wanda aka fi sani da “Gentle de Yahoo”, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin ƙungiyar IPOB, a wani samame da ta kai a yankin kudu maso gabashin ƙasar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito wata majiya daga hedikwatar rundunar sojin tana cewa an cafke Gentle de Yahoo ne yayin farmakin da sojojin suka kai a ranar Lahadi kan sansanonin ’yan ƙungiyar a cikin wani dajin da ke ƙaramar hukumar Okigwe a Jihar Imo. An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Majiyar ta ce a yayin cafke jagoran na IPOB, an kuma ƙwato...
    Saboda wannan baiwa daga Allah, iyalai da ‘yan uwan mai akuyar suka sanar da shirye-shiryen gudanar da bikin murnar haihuwar ‘ya’yan akuyar a ranar Lahadi mai zuwa a Garun Dakasoye, karamar hukumar Garun Malam ta Jihar Kano, inda za a yi musu suna da kuma karatun Alkur’ani mai girma.   A nasa bangaren, mahaifin budurwar, Malam Aliyu dake Garin Dakasoye, ya tabbatar da cewa za su gudanar da bikin domin nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki bisa wannan ni’ima da ya ba su.   Ya kara da cewa: “Mun gode wa Allah bisa wannan arziki, kuma muna sa ran gudanar da bikin tare da sanya musu suna domin nuna godiya ga Allah mai daukaka.” Daga kanmu, magana ta ƙare....
    Da safiyar yau 17 ga watan Satumba, aka bude dandalin tattauna batutuwan tsaro na Xiangshan karo na 12 da zai dauki kwanaki 3, daga raneku 17 zuwa 19 ga wannan nan, bisa jigon “daukaka tsarin duniya da inganta neman ci gaba cikin lumana”, a nan birnin Beijing. Tawagogi sama da 100 na gwamnatocin kasashe daban-daban da yankuna da wakilan kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar taron, inda yawan masu rajista ya wuce 1,800. Da safiyar yau, taron ya shirya tarukan tattaunawa guda 6 bisa jigon “ma’anar cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiyya” da “madaidaitan hanyoyi da manyan kasashe za su bi na yin mu’ammala”, da “hanyoyin warware rikice-rikicen shiyya-shiyya”, da “cika shekaru 80 da kafuwar MDD: samun...
    Har kullum, Sin za ta ci gaba da martaba ka’idojin kare hakkokin kamfanoninta. Duba da cewa manhajar TikTok ta shafe tsawon shekaru tana aiki a Amurka, ta kuma samar da dumbin ayyukan yi ga tarin Amurkawa, tare da bayar da gudummawa ga tattalin arzikin kasar, ya kamata gwamnatin kasar ta baiwa manhajar damar cin gajiya daidai da sauran makamantanta dake kasar. Kamar dai ko da yaushe, burin Sin shi ne wanzar da daidaito da cimma moriyar bai daya tare da Amurka.     Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe...
    Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe. Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai. Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi Ya ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.” Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana...
    Rahotannin da suke fitowa daga Gaza sun ce, fiye da Falasdinawa 35 ne su ka yi shahada daga Safiyar yau Laraba zuwa  tsakiyar rana,sanadiyyar hare-haren da HKI take kai wa. Hakan tana faruwa ne a daidai lokacin da ma’aikatar  kiwon lafiya a Gaza ta yi gargadi akan cewa asibitocin yankin sun kusa daina aiki baki daya. Tashar talabijin din ‘aljazira’ ta kasar Qatar ta ce,adadin wadanda su ka yi shahada har zuwa marecen yau sun kai 51,38 daga cikinsu a cikin birnin Gaza kadai. A gefe daya rahoton tashar talbijin din ta ‘aljazira’ ya  bayyana cewa; HKI ta yanke hanyoyin sadarrwa na “Internet’ a fadin Gaza, haka nan kuma ta hana hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) shigar da makamashi...
    Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye dokar ta-ɓaci da ya ayyana ta tsawon watanni shida a Jihar Ribas. Tinubu, ya ayyana dokar tun a ranar 18 ga watan Maris, 2025, saboda rikicin siyasa da ya haifar da tsaiko a harkokin mulki tsakanin ɓangaren Zartarwa da Majalisar Dokokin jihar. NECO ta saki sakamakon jarabawar 2025 Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi A jawabin da ya gabatar a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba, Tinubu ya ce matakin dokar ta-ɓacin ya cimma manufarsa, kuma ba za a tsawaita ba ƙarewar wa’adin da aka gindaya. “Ina farin ciki yau game da bayanan da ke hannuna, an samu yanayin fahimta a tsakanin dukkanin masu ruwa...
    A yau, 17 ga watan Satumba, Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta-ɓaci da ya ƙaƙaba wa al’ummar jihar Ribas biyo bayan rashin jituwa da yaƙi ci yaƙi cinyewa da ya dabaibaye ɓangaren zartarwa da na dokokin jihar.     Cikakken bayani na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD. Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana. Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a...
    Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido. An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje. Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma. Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar...
    Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi. Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq. Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Sun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi. A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana...
    Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ba ta da niyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027. Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati don amfaninta. Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo “Wannan gwamnati ba ta shirya gudanar da zaɓen adalci ba. Daga yadda suke tafiyar da al’amura, za ka gane yadda suke tarwatsa jam’iyyun siyasa....
    Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar. “Mun fara wannan shiri fiye da shekara...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta amince da ƙarin kasafin kuɗi na Naira Biliyan 75 na shekarar 2025, ga gwamnatin jiha da kuma ƙananan hukumomi 27. Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kaɗan bayan zaman majalisar da aka gudanar a gidan gwamnati dake Dutse, babban birnin jihar. Ya bayyana cewa, wannan ƙarin kasafin kuɗi ya samo asali ne daga ƙarin kuɗaɗen shiga domin biyan buƙatun kuɗaɗen da suka taso, da kuma ƙarfafa manyan fannoni da za su kawo ci gaba mai ɗorewa a faɗin jihar. Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, majalisar ta amince da Naira Biliyan 58 ga gwamnatin jiha da kuma Naira Biliyan 17 ga Kananan Hukumomi 27,...