Iran ta bukaci gudanar da binciken gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya kan harin da yahudawan sahayoniyya suka kai gidan kurkukun Evin

A cikin wata wasika da ya aike wa babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar, jakada kuma zaunannen wakilin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Sa’ed Irawani, ya yi kira da a gaggauta gudanar da bincike mai tsanani kan harin da ‘yan sahayoniyya suka kai gidan yarin Evin da ke birnin Tehran.

A cikin wasikar, Irawani ya rubuta cewa: Wannan harin da aka kai a ranar Litinin, 23 ga watan Yunin wannan shekara ta 2025, an nufi wani gidan yarin farar hula da gangan, wanda hakan ya sabawa dokokin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa da kuma muhimman ka’idojin Yarjejeniya ta Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin da yake yin Allah wadai da harin, jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Bisa la’akari da irin hadari da kuma munin wannan mugun aiki da aka aikata, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bukaci kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da babban sakataren Majalisar da su yi Allah wadai da harin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai wa gidan yarin Evin. Ba tare da wata shakka ba, harin yana matsayin babban cin zarafi ga dokokin jin kai na ƙasa da ƙasa da dokokin haƙƙin ɗan adam na duniya.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: a Majalisar Dinkin Duniya

এছাড়াও পড়ুন:

An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta ce, ta kama wani mai babur mai suna Kadir Owolabi, yana ɗauke da ƙoƙon kan mutane uku.

Mai magana da yawun rundunar, CSP Omolola Odutola ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a Abeokuta ranar Talata.

Gwamnati ta amince a kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda 9 Bello Turji bai miƙa wuya ba har yanzu — DHQ

Odutola ta ce, binciken da jami’an ’yan sandan tafi da gidanka suka yi a jakar wanda ake zargin, ya kai ga gano wasu kan mutane guda uku.

Ta ce, jami’an tsaro ne suka gudanar da aikin bincike na yau da kullum daga rundunar ’yan sanda na tafi da gidanka na 71 PMF, a yankin Awa da ke Ijebu, da ƙarfe 2:00 na rana.

A ranar Litinin, a kan babbar titin Ijebu Ode zuwa Ibadan a mahaɗar ’yan gudun hijira, Oru Ijebu.

“A yayin atisayen, jami’an sun cafke Kadir Owolabi wanda ke kan babur, inda aka gudanar da bincike a kan jakunkunansa, an gano wasu kan mutane guda uku.

“Bincike na farko ya kai ga kama wani wanda ake zargi, mai suna Jamiu Yisa, mai shekara 53, a bayan sakatariyar Ƙaramar hukumar Ijebu Ode,” in ji ta.

Odutola ta ce, Kwamishinan ’yan sanda jihar, Lanre Ogunlowo ya umurci hukumar binciken manyan laifuka ta jihar da ta ɗauki ragamar lamarin domin gudanar da bincike mai zurfi.

Kakakin rundunar ta ƙara da cewa, rundunar ta sake jaddada aniyarta na ɗaukar ƙwararan matakai na yaƙi da miyagun laifuka, ta kuma  buƙaci mazauna yankin da su ba ’yan sanda haɗin kai tare da ba jama’a tabbacin amincewa da su da kuma basu kariyar sirri.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kama mai babur ɗauke da ƙoƙunan kan mutane a Ogun
  • Iran Ta Bukaci Mayar Da Martani Kan Aniyar Isra’ila Ta Mamaye Yankunan Kasashe Domin Kafa ‘Babbar Isra’ila’
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ya Bayyana Isra’ila A Matsayar ‘Yar Yaudara
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Fatali Da Batun Kafa Gwamnatin Hadaka A Kasar Sudan
  • Gwamna Sule Ya Ziyarci Gidan Yarin Keffi Bayan Tserewar Fursunoni 16
  • Wani Bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Karbe Mulkin Jihar
  • Fursunoni 16 sun tsere daga gidan yarin Keffi
  • Harin ’yan fashi: An rufe Federal Poly Bauchi Bauchi
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Sanar Da Mutuwan Mutane 60 Saboda Yunwa A El-Fasher Na Sudan
  • Ruwan Wutan sojan Nijeriya Ya Kashe ‘Yan Bindiga A Zamfara.