2025-07-29@16:08:23 GMT
إجمالي نتائج البحث: 5887

«wadanda suka canci»:

    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau. Sakataren Gwamnatin Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar a Talatar nan. Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri Sanarwar ta ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar suka zaɓa. Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne. Ya kuma yi kira ga...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ce akwai kwamitoci guda 30 da aka daurawa nauyin bibiyar yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Jihar ke sarrafa kudade domin gudanar da harkokin yau da kullum, gami da ayyukan raya kasa.   Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana hakan lokacin wata ziyarar aiki a karamar hukumar Babura. Yayi bayanin cewar, an dorawa Kwamatinsa alhakin duba kananan hukumomi domin tabbatar da shugabanci nagari a yankunan karkara.   A cewarsa, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da jadawalin kudaden da karamar hukuma ke samu daga kason arzikin kasa, da littafin hulda da banki,da takardun biyan kudade na voucher da kundin bayanan...
    Ambaliya sanadiyyar wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi ajalin mutane 30 a Arewacin China, lamarin da ya tilasta kwashe mutane fiye da 80,000 zuwa Beijing, babban birnin kasar. Jaridar Beijing Daily ta ruwaito cewa ruwan saman ya haddasa rufe hanyoyi da dama da kuma katsewar lantarki a kauyuka sama da 130 yayin da jami’an agaji ke ci gaba da aikin ceto. Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri A jiya Litinin ce Shugaban China, Xi Jinping ya ba da umarnin daukar matakan gaggauwa a yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliya sakamakon mamakon ruwan da ake hasashen za a ci gaba...
    Akalla mutane 7 ne aka ceto, bayan kifewar kwale-kwale a wani kogi da ke Zangon Maje, ƙaramar hukumar Taura, ta jihar Jigawa ranar Litinin. Shugaban ƙaramar hukumar Taura, Dr Shuaibu Hambali ne ya bayyana hakan ga Rediyon Najeriya a Dutse, babban birnin jihar. A cewarsa, lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, lokacin da wasu manoma ke dawowa daga gonakinsu a ƙauyen Zangon Maje, inda suka hau kwale-kwalen. Ya ce, jami’an bada agajin gaggawa  na yankin sun samu nasarar ceto mutane 7 a kokarin da suka yi na ceto wadanda lamarin ya shafa. Ya ƙara da cewa, masu ceton sun gano gawar mutum guda a yankin Yalleman da ke ƙaramar hukumar Kaugama. Dr Shuaibu ya bayyana cewa,...
    2. Asibitin Turai Yar’Adua 3. Asibitin Amadi Rimi 4. Asibitin Jibia 5. Asibitin Funtua Zango, ya ce gwamnati na ƙoƙarin tabbatar da cewa duk wanda ke fama da cutar ya samu magani cikin sauƙi ba tare da biyan kuɗi ba. Zazzabin taifod yana yaɗuwa ne musamman a lokacin damina, kuma yana da nasaba da amfani da ruwa mai datti da rashin tsafta. Alamomin cutar sun haɗa da ciwon ciki, ciwon kai, da gajiyar jiki. Gwamnati ta shawarci jama’a da su riƙa kula da tsafta da kuma hanzarta zuwa asibiti idan sun ga irin waɗannan alamomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da fara karɓar dalibai a sabbin darussa guda shida a fannin noma a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a shekarar karatun 2025/2026. Za a gudanar da shirye-shiryen ne a sabuwar Tsangayar Noma da aka kafa a garin Malam Sidi da ke Karamar Hukumar Kwami. A ranar Litinin bayan taron majalisar gudanarwar jihar, Kwamishinan Noma da Kiwo, Barnabas Malle, ya bayyana cewa an amince da fara aikin sabuwar tsangayar aikin nomar ce ranar 21 ga Watan Mayu, 2025. Sabbin darussan da aka amince da su sun haɗa da digir a bangaren Noma, Digiri a bangaren Gandun Daji da Dabbobin Jeji, Digiri a Kimiyyar Noma da Digiri a Kimiyyar Kasa, sai Digiri a fannin...
    Dan majalisa mai suna muhammad Mirzai ya ce; Kasashen turai sun zaku, akan su sami bayanai akan girman asarar da aka yi wa cibiyoyin Nukiliyar Iran don haka ya zama wajibi Iran din ta yi amfani da siyasar barinsu a cikin duhu. A yayin zaman da majalisar shawarar musulunci ta Iran ta yi a yau Talata, dan majalisar ya kuma yi bayani akan kallafaffen yakin kwanaki 12, ya yi ishara akan yadda HKI ta yi amfani da kirkirarriyar fasaha da kuma wasu hanyoyi na leken asiri,amma duk da haka ta ci kasa, saboda jagoranci mai cike da fasaha na jagora, da kuma yadda al’ummar kasar ta yi tsayin daka da goyon bayan tsarin musulunci. Haka nan kuma ya ce; Daga...
    Sannan su ɗaure kayan da iska za iya ɗauka. Ta kuma shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayi kafin tashi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jiya Litinin ne dai gwamnatin kasar Holland ta sanar da hana wa minstocin tsaron kasa Itmir Bin Gafir, da na kudi, Bitsirael Smotrich shiga cikinta. Kasar ta Holland ta zargi wadannan mutanen biyu da cewa suna ingiza sojojin HKI da yi wa Falasdinawa kisan kiyashi da kuma fadada yawan matsugunan ‘yan sahayoniya  a yankunan da aka ce nan ne za a kafa Daular Falasdinawa.  Haka nan kuma gwamnatin kasar ta Holland ta kira yi jakadan HKI a birnin Hauge domin gargadinsa akan yanayin da ake ciki a Gaza, da cewa babu yadda za a iya ci gaba da jurewa akansa, ko kare dalilin jefa yankin cikin wannan halin.” Wannan matakin na kasar Holland ya zo ne gabanin wani taro...
    Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da naɗa Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Gusau kuma Sarkin Katsina na Masarautar Gusau. Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan, inda ya bayyana cewa an yi naɗin ne bisa ga shawarwarin da masu zaɓen sarakuna na masarautar Gusau suka bayar, tare da bin al’ada da dokokin da suka dace. A wata sanarwa da mai taimakawa na musamman kan harkokin yaɗa labarai a ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, Sulaiman Ahmad Tudu, ya fitar, ya ce sabon Sarkin, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, shi ne ɗa na farko ga marigayi Sarki, kuma kafin naɗin nasa yana riƙe da mukamin Bunun Gusau. Alhaji Abdulkadir ya hau karagar...
    Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 15 da ake zargi da laifuka daban-daban, ciki har da wani kasurgumin  dan fashi da  makami mai suna Mu’azu Barga, a wani samame da aka lakaba wa suna “Operation Kukan Kura”.   Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano. Ya ce samamen, wanda dakaru na musamman suka gudanar a unguwannin Sheka, Ja’oji, da Kurna a ranar 26 ga Yulin 2025, na da nufin gano da kuma hana aikata laifuka, bisa umarnin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun.   Kiyawa ya bayyana cewa, wadanda aka kama ‘yan tsakanin shekaru 14 ne zuwa 28, kuma an...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamna Lawal ya taya sabon sarki murna, tare da roƙon Allah Ya bashi hikima da ikon yin jagoranci na gari. Ya kuma buƙace shi da ya ci gaba da bin kyawawan ɗabi’u da tafarkin tsofaffin sarakuna domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a masarautar Gusau. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Sai dai ya gode wa PDP bisa damar da ta ba shi ya tsaya takara a 2023, amma yanzu lokaci ya yi ne da zai yi gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mata a Arewacin Najeriya na fuskantar kalubale da dama a fannin karantar kimiyya. Akwai darussan da a mafi yawan lokuta ba mata kadai ba, har da mazan na kaurace musu. NAJERIYA A YAU: Matakan Da Muke Dauka Don Karfafawa ’Yan Najeriya Kwarin Gwiwar Kada Kuri’a —INEC DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Shirin Najeriya a Yau ya yi nazari  ne kan dalilan da suka sa matan Arewacin Najeriya ke tsoron karantar ilimin kimiyya. Domin sauke cikakken shirin, latsa nan
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Idan aka maimaita ta’asar kai hari kan Iran, za ta mayar da martani ta hanyar da ba za a iya boyewa ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya mayar da martani kan barazanar da jami’an Amurka suka yi a baya-bayan nan, inda ya ce idan aka sake kai hari kan Iran, za ta mayar da martani mai tsauri wanda ba zai yiwu a iya boye ba. Araghchi ya kara da cewa a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin din nan cewa: Iran, kasar da ke da al’adun gargajiyar da ta shafe shekaru dubu bakwai na wayewar kai, ba za ta taba mika kai ga barazana...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta musanta zargin yin katsalandan a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Ismail Baqa’i, ya musanta zargin katsalandan din Iran a tattaunawar tsagaita bude wuta a Gaza. A yayin da yake amsa tambaya game da ikirarin da shugaban kasar Amurka ya yi na cewa Iran na tsoma baki a shawarwarin tsagaita bude wuta a zirin Gaza, ya ce: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da dukkan kasashen duniya tana yin kakkausar suka kan kisan gillar da ake yi a Gaza tare da goyon bayan duk wani tsari da zai kai ga dakatar da aikata laifuka da kuma rage radadin wahalhalun da al’ummar Gaza suke ciki. Baqa’i ya jaddada cewa; Masu yin shawarwarin...
    Martanin da Rasha ta mayar dangane da sabon wa’adin Trump na kawo karshen yakin Ukraine Mataimakin shugaban kwamitin tsaron Rasha Dmitry Medvedev ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump game da takaita wa’adin tsagaita bude wuta tsakanin Rasha da Ukraine, yana mai cewa matakin kunna yaki ne. Medvedev ya rubuta a kan dandalinsa na X cewa: “Trump yana wasa, irin wasan gargadi tare da Rasha: Na kayyade mata kwanaki 50 ko 10 … amma ya kamata ya tuna abubuwa biyu: Na daya Rasha ba Isra’ila ba ne ko kuma Iran. Na biyu. duk wani sabon gargadi yana matsayin barazana ne kuma matakin kunna wutar yaki ne. Ba tsakanin Rasha da Ukraine ba, amma tare da kasarsa. Amurka ta...
    Mummunar yunwa a Gaza.. Wakilin gidan talabijin na Al-Alam ya bayyana cewa: Shi da iyalansa kwana biyu ba su ci abinci ba Wakilin gidan talabijin na Al-Alam na kasar Iran ya ruwaito cewa: An samu barkewar yunwa mai tsanani a Gaza, inda ya tabbatar da cewa ya kwashe kwanaki biyu bai ci komai ba. Basil Khairudden wakilin gidan talabijin na Al-Alam a Gaza, ya ce: “A ranar Juma’a, shi da iyalinsa da daukacin al’ummar Gaza ba su iya samun ko da biredi guda da za su ci ba, sakamakon yunwa da ake fama da ita a Gaza.” Ya tabbatar da cewa a Gaza akwai mutanen da ba su ci abinci ko da sau daya a tsawon kwanaki uku. A ranar...
    Amma yanzu, babu matsalar gaba ɗaya a ƙananan hukumomi 11, yayin da aka samu sauƙi a wasu tara. Ya ce har yanzu ana fama da hare-hare a ƙananan hukumomi huɗu: Faskari, Ƙankara, Safana da Matazu. Kwamishinan ya jaddada cewa jami’an tsaro suna iyakar ƙoƙarinsu, kuma gwamna yana ci gaba da tattaunawa da manyan jami’an tsaro domin kawo ƙarshen matsalar. Ya buƙaci al’umma da su daina suka, su kuma tallafa wa jami’an tsaro da addu’a da fahimta, ganin irin sadaukarwar da suke yi domin kare rayukan jama’a. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Sama da mutum 100 daga cikin jami’an tsaron al’umma da  Gwamnatin Katsina ta samar ne suka suka mutu a yayin aikin karaɗe ’yan bindiga da suka addabi al’ummomin jihar. Wannan ƙari ne a kan sojoji da kuma aƙalla jami’an ’yan sanda 30 da suka rasu a yayin aikin tabbatar da tsaron rayuwa da duniyoyin al’umma, a cewar ma’aikatar tsaron jihar. Kwamishinan tsaron jihar, Nasir Mua’zu ya sanar da haka ne a martaninsa kan wasu rahotanni da ke yawo a kafofin sada zumunta, waɗanda ya ce ana amfani da su domin tayar da hankalin jama’a. Mu’azu ya ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Raɗɗa yana yin iya bakin koƙarinsa wajen shawo kan matsalar ’yan ta’adda kuma ana samun nasara a kansu. Kwamishinan...
    Ya bayyana halin da aka shiga mara daɗi, inda ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da waɗanda suka yi asarar dukiyoyi, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta tallafa musu wajen sake gina musu gidajen su da sauya muhallinsu. Fintiri ya kuma soki waɗanda ke yaɗa rahotannin ƙaryar game da lamarin, ba tare da fahimtar ainihin abin da ke faruwa ba, inda ya ce hakan yana da nasaba da tuggun siyasa da son zuciya. Ya bayyana cewa maƙasudin ambaliyar sun haɗa da ruwan sama mai yawa da toshewar hanyoyin ruwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
    Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labaru na yau da kullum. A wajen taron, wani dan jarida ya yi tambaya game da sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da aka kulla tsakanin Amurka da kungiyar EU. A yayin da yake ba da amsa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin a ko da yaushe tana ba da shawarar cewa, ya kamata dukkan bangarori su warware bambance-bambancen tattalin arziki da cinikayya ta hanyar tattaunawa, domin kiyaye yanayin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa. Bugu da kari, dangane da taron tattauna batun tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka a kasar Sweden, Guo Jiakun ya bayyana cewa, matsayin kasar Sin kan batutuwan da suka...
    An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa. Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji. DW ya ruwaito cewa ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu. Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa Iran a shirye take ta fadada hulda da kasashen turai, amma kuma wannan ba zai sa ta saryar da hakkinta na sarrafa makamashin nukliya karshen dokokin kasa da kasa wadanda suka amince mata ta yi haka ba. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a yau Litinin a lokacinda yake ganaw da sabon jakadan kasar Faransa a Tehran pierre Cochard wanda ya mika masa tarkardun fara aikinbsa. Shugaban ya kara da cewa an takurawa kasar Iran dangane da shirinta na makamashin nukliya a bayan. Amma daga yanzun kuma ba zata amince da irin takurawa ta bay aba. Ya kuma bayyana cewa tattaunawa tsakanin Iran da kasashe...
    Shugaban kungiyar Hamass ya bayyana cewa HKI da gwamnatin kasar Amurka sun janye daga tattaunawa tsakaninsu da kungiyar ne don sake komawa yaki har zuwa lokacinda zasu shafe falasdinawa a gaza. Tashar talabijin nta Presstv a nan Tehran ya nakalto Kkalilul Hayya, yana fadar haka a wani jawabin da aka watsa a tashoshin talabijin nay au Litinin. Alhayya ya bayyana cewa akwai ci gaba a tattaunawar tsagaiuta wuta tsakanin kungiyar da HKI da kuma Amurka, amma janyewar HKI da kuma Amurka a wannan tattaunawar wata dasisa ce don ci gaba da kissan kiyashi a gaza. Ya ce: masu shiga tsakanin sun tabbatar da cewa akwai ci gaba a tattaunawar da ake yi a doha, sai dai sun janye ne don...
    Alkalin alkalan JMI Gholamhussain Muhsen Ejei, ya bayyana cewa, babu shakka gwamnatin kasar Amurka tana da hannu a hare-haren da ake dangantawa da kungiyar yan ta’adda ta Jaishul Zulm da ya faru a cikin wani kotu a garin Zahidan na lardin sistan Baluchistan a cikin yan kwanakin da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto alkalin alkalan yana fadar haka a lokacinda ya kai ziyara a gaisuwar wadanda abin ya shafa. Ya kuma bukaci mataimakinsa ya gabatar da dukkan bukatun da wadanda abin ya shafa suka gabatar. A cikin maganar sa alkalin alkalan ya bayyana cewa, an halaka mutane uku a musayar wuta da yan ta’addan a kusa da kotun. Sannan JMI ta samar da shahidai...
    Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya bukaci shuggaban kasar Amurka Donal  Trump ya taiama ya kawo karshen yaki a Gaza, ya kuma kawo karshen walar da Falasdinawa suke ciki. Jaridar The Nation ta kasar Amurka ta nakalto shugaba Sisi yana fadar haka a wani jawabinda ya gabatar a yau Litinin, inda yayi alkawaliwa mutanen kasar masar kan cewa masar bazata taba kyale mutanen Gaza a halin da suke ciki ba har abada. Ya ce: Gwamnatin kasar Masar tana daga cikin kasashen da suka tsaya don ganin an kawo karshen wannan yakin, tare da Amurkan da kuma kasar Qatar don tabbatar da cewa an kawo karshen yakin . Shugaban daga karshe ya gabatar da shawarar samar da kasashe biyu a matsayin...
    A yankin sweida na kudancin kasar Siriya mazauna wurin sun bayyana cewa abinci da ruwa da kuma kayakin bukatu nay au da kullum sun fara karanci sosai a yankin saboda yakin makonni uku da suke fafatawa da sojojin sabuwar gwamnati a Damascus. Jaridar The National ta Amurka ta bayyana cewa yankin sweida na kudancin kasar Siriya wanda kuma HKI ta dade tana shigowa yankin ta fita a halin nyanzu yana fama da karancin abinci da ruwansha. Sannan da alamun har yanzun sojojin sabuwar gwamnatin kasar Siriya tana ci gaba da hana shigowar abinci da ruwa yankin duk tare da shelanta tsagaita wuta da aka yi. Labarin ya kara da cewa. an kashe daruruwan mutane a fafatawar da mayakan hTI suka...
    Shugaba Bola Tinubu ya karrama ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya da lambar yabo ta OON. Shugaban ya bai kowacce ’yar wasa  a tawagar ta Super Falcons kyautar gida mai ɗakuna 3 a rukunin gidaje na Renewed Hope da kuɗi dala dubu 100. Haka kuma, shugaban ya kuma bai wa masu horas da tawagar kyautar dala dubu 50.  
    Kasar Sin ta bullo da wani shirin bayar da tallafin kula da yara a fadin kasar wanda zai fara aiki daga shekarar 2025, a wani bangare na kokarin tallafa wa iyalai da kuma karfafa yawan haihuwa. Shirin zai bai wa iyalai tallafin yuan 3,600, kimanin dalar Amurka 503, a kowace shekara a kan kowane yaro da bai kai shekaru uku da haihuwa ba. Za a kebe tallafin daga cire harajin kudin shiga kuma ba za a kidaya shi a matsayin kudin shiga na iyalai ko na mutum daya ba a yayin da ake tantance masu karbar taimakon, inda abun zai zama kamar dai irin na wadanda ke karbar alawus na cin abinci ko kuma wadanda ke rayuwa cikin matsananciyar wahala....
    Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhinin sa kan rahotannin ambaliya mai tsanani da ta faru a Yola, Jihar Adamawa, wacce ta yi sanadiyar  mutuwar mutane, da asarar dukiyoyi da kuma raba dimbin jama’a da muhallansu. A cikin wata sanarwa, Gwamna AbdulRazaq ya ce kungiyar NGF na jajantawa gwamnatin Jihar Adamawa ƙarƙashin jagorancin Mai Girma Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri yayin da suke kokarin tara kayan agaji da daukar matakan rage illar wannan iftila’in. Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar ta yaba da matakin gaggawa da ‘yan sanda da kuma dakarun sojin Najeriya suka dauka na tura rundunonin ruwa, bisa gayyatar gwamnatin jihar, domin taimaka wa al’ummar da abin ya shafa a wannan lokaci...
    Ruwan sama mai ƙarfn gaske ya haddasa mummunar ambaliya a Yola ta Kudu, Jihar Adamawa, inda mutane da dama suka mutu, yayin da wasu da dama suka rasa matsugunnansu. Yankunan da ambaliyar ta fi shafa sun hada da Shagari, Sabon Pegi da Anguwan Tabo. Ayyukan ceto suna ci gaba da gudana, inda Sojoji da hukumomin agaji ke kwashe mazauna yankunan da abin ya shafa. Hukumomi sun shawarci mazauna yankunan da ke fuskantar barazanar ambaliya da su gaggauta barin wuraren, kasancewar ana hasashen karin ruwan sama.   RN  
    Jami’an Hukumar Tsaron Farin Kaya DSS da takwarorinsu na rundunar sojin ƙasa sun kashe aƙalla ’yan ta’adda 45 da ke addabar wasu sassan Jihar Neja. Bayanai sun ce an kashe ’yan ta’addan ne a ƙauyen Iburu da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a ranar Juma’ar da ta gabata bayan jami’an DSS sun tattaro bayanan sirri kan harƙallar miyagun a yankin. Mutum miliyan 1.2 na fama da ciwon hanta a Kano Najeriya ta ba wa Habasha kyautar iri da itatuwan cashew 100,000 Majiyoyin tsaro sun ce DSS ta samu bayanan sirri kan wani hari da ’yan ta’addan ke shirin kaiwa ƙauyen Iburu a kan babura, lamarin da sojojin da ke shirin ko-ta-kwana suka tari hanzarinsa. Ɗaya daga cikin majiyoyin ya shaida cewa...
    Hukumar Tsarin Fansho na Hadin Gwiwa tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi a Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta raba sama da Naira Biliyan 1 da dubu 500 ga tsofaffin ma’aikata 569. Yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin a gaban Gidan Fansho kafin fara rabon kudin, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na jihar a matsayin daya daga cikin mafi nagarta a kasar nan. A cewarsa, fiye da jihohi ashirin sun kai ziyara jihar Jigawa domin koyon yadda take tafiyar da shirin fansho. Ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi saboda dagewarsa da kuma jajircewarsa wajen dorewa da inganta tsarin fansho a jihar. Alhaji Dagaceri ya yabawa Gwamna Namadi kan...
    Jam’iyyar ta bayyana cewa bayan bincike daga reshen jam’iyyar na jihar Kaduna, ya tabbatar da cewa El-Rufai ba halataccen ɗan SDP bane. Saboda haka, Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya kafa masa takunkumin shekaru 30, har zuwa shekarar 2055, ya hana shi sake neman zama mamba ko hulɗa da jam’iyyar ta kowace fuska. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba da shawarar a soke ko kara inganta aikin titin gina hanya mai tsawon kilomita biyar a karamar hukumar Gabasawa. Wannan mataki ya biyo bayan karɓar rahoton da Kwamitin  Majalisar kan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci ya gabatar dangane da ambaliyar da ta afku a Zakirai, cikin karamar hukumar ta Gabasawa. Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin, Alhaji Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana wasu muhimman shawarwari da suka hada da: Umurtar kamfanin da ke aikin gina hanyar da ya faɗaɗa magudanar ruwa a yankin da abin ya shafa da kuma gaggauta kai agajin gaggawa ga waɗanda ambaliyar ta shafa. Sauran shawarwarin sun haɗa da tura tawagar ƙwararru daga ma’aikatun ayyuka da muhalli na jihar...
    Gwamnatin Kano ta sanar da cewa akwai aƙalla fiye da mutum miliyan 1.2 da ke fama da ciwon hanta da ake kira Hepatitis B a faɗin jihar. Kwamishinan Lafiya, Dokta Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan yau Litinin yayin wani taron manema labarai a Cibiyar Tiyata ta Gaggawa da ke Asibitin Nasarawa a birnin Dabo. Najeriya ta ba wa Habasha kyautar iri da itatuwan cashew 100,000 An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja Aminiya ta ruwaito cewa wannan sanarwar na zuwa ne a daidai Ranar Ciwon Hanta ta Duniya ta bana. Kwamishinan ya bayyana ciwon hanta a matsayin matsala babba da ana iya magance ta matuƙar an miƙe tsaye a kai. Ya yi bayanin cewa muddin...
    A kokarinsa na gano hakikanin dalilan da suka sa aka bayar da beli ga wani sanannen mai safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu, da aka ce an sako shi bisa umarnin Kwamishinan Sufuri na Kano, Ibrahim Ali Namadi, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wani kwamiti na mutum takwas domin gudanar da bincike mai zurfi. Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Umar Faruk Ibrahim ne ya kaddamar da kwamitin a madadin gwamnan. An umurci kwamitin da ya gudanar da binciken cikin mako guda, domin gano hakikanin abin da ya faru da kuma ba da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka. Shugaban kwamitin shi ne Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Dokoki,...
    122- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko, idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata mun bayyana yadda. Ummul muminina Aisha...
    121- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko , mun tsaya inda muka bayyana yadda Talha da Zubair suka nemi izinin Amirulmuminina (a) na zuwa...
    120-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da haka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshin da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane Rastan na Aya. Shahid Murtadha Muttahhari, ko kuma cikin littafin mathnawa na maulana Jalaluddeen Rum ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ////… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sarir Imam Al-Hassan Almujtaba (a) diyar Fatima (s) kuma jikan manzon All..(s) na farko , mon tsaya inda muka bayyana yadda Talha da Zubair suka bukaci Amirulmuminina (a) ya yi masu izini...
    Jam’iyyar ta buƙaci hukumar INEC da sauran hukumomi da su lura cewa El-Rufai ba ɗan jam’iyyar ba ne, kuma bai da hurumin wakiltar ta a kowanne mataki. SDP ta kuma jaddada ƙudurinta na kare dimokuraɗiyya ta cikin gida da kuma adawa mai tushe da gaskiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Najeriya ta ba wa ƙasar Habasha kyautar itatuwan cashew guda 2,000 da kuma irin cashew guda 100,000. Najeriya ta bayar da kyautar irin ne a wani bangare na yunƙurin taimaka wa ƙasashen biyu wajen samar da abinci mai yawa da kuma ƙarfafa dangantakarsu. Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayar da wannan kyauta, da za ta iya shuke ƙasa mai fadin hekta 600. Shettima ya bayar kyautar ce a lokacin da ya isa birnin Adis Ababa, babban birnin kasar, domin halartar Babban Taron Majalisar Xinkin Duniya Kan Tsarin Abinci. Arewa za ta kayar da Tinubu a zaɓen 2027 —Babachir Matsalar Lantarki: Ga tsada ga rashin wuta An gano gawar mutum 15 bayan hatsarin kwalekwale a Neja Ministan Harkokin...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa;Yunwar da mutanen Gaza suke fama da ita na tsawon watanni biyar, laifi ne maras tamka da HKI take tafkawa, da ya zama wajibi kungiyar kasashen musulmi ta yi taron gaggawa akansa. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran Dr. Isma’ila Baka’i wanda ya gabatar da taron manema labaru a yau Litinin ya kuma yi Magana akan tattaunawar da Iran ta yi da kasashen turai akan shirinta na makamin Nukiliya, ya ce: Tattaunawar da aka yi ta da kasashen turai manufarta ita ce dauke wa Iran takunkuman da aka kakaba mata akan shirinta na Nukiliya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Kasashen na turai ba su da hakkin su kakabawa Iran...
    Kasar Amurka ta sanar da dakatar da bai wa mutanen Nijar bisa ta shiga cikin kasarta har illa masha Allahu. Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka ne ya tabbatar da cewa an dakatar da bayar da bisa din ga ‘yan kasar Nijar da suke son shiga cikin kasar, saboda abinda ya kira matsala da ake da ita da gwamnatin Nijar, ba tare da yin Karin bayani ba.  Sai dai kuma sanarwar ta yi togiya akan jami’an diflomasiyya da sauran jami’an gwamanti,kamar yadda wani sako na diplomasiyya ya nuna a ranar 25 ga watan Yuli. Wannan matakin na  Amurka ya biyo byan rashin jituwar da ake da shi a tsakanin gwamatin Amurka da gwamnatin Jamhuriyar Nijar. A watan Satumba...
    A yau Litinin ne za a yi jana’izar sanannen mawakin kasar Lebanon wanda ya yi fice da wakokin gwgawarmaya da kishin kasa wanda zai sami halartar wakilan gwamnatin kasar da kuma al’umma. Jana’izar za ta kasance ne a majami’ar  Raqad Sayyida dake garin Bakfaya. Asibitin Khuri da Rahbani ya rasu ya cika da mutane tun da safiyar yau domin daukar jana’izarsa zuwa garin Bakfaya. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Rahbani ya rasu yana dan shekaru 69 bayan da ya yi gajeruwar rashin lafiya. A lokacin rayuwarsa ya shahara da wakoki na gwgawarmaya da kishin kasa, daga cikin da akwai wakar da ya yi wa Shahid Sayyid Hassan Nasarallah.
    Wani jami’in kasar Ukiraniya ya bayyana cewa, a kalla mutane 8 ne su ka jikkata sanadiyyar munanan hare-haren da Rasha ta kai wa birnin Kiev ta hanyar amfani da makamai masu linzami. Shugaban sha’anin tafiyar da Mulki na soja a birnin Kiev Taimur Tikatishinko ya wallafa sanarwa a shafinsa na “Telegram’ cewa; A tsakanin wadanda su ka jikkata din da akwai karamin yaro dan shekaru 3, kuma tuni an dauki mutane 4 zuwa asibiti, daya daga cikinsu yana cikin mummunan hali. Shi kuwa magajin birnin na Kiev Fitali Kikitshiko cewa ya yi, mutanen da su ka jikkata suna zaune ne a cikin gidaje mabanbanta a unguwa daya. Har ila yau ya kara da cea; Harin ya haddasa fashewa mai karfi...
    Al’ummar Arewacin Najeriya na shirin kayar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027 saboda ƙuncin rayuwa da kuma tsare-tsaren gwamnatinsa da suka mayar da yankin saniyar ware. Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal  ne ya bayyana haka, yana mai cewa gamayyar shugabanni da ’yan siyasar Arewa na haɗa ƙarfi da ƙarfe domin tsayar Da ɗan takara da nufin yaƙar gwamnatin Tinubu a zaɓen 2027. Babachir David Lawal ya bayya cewa shugabannin siyasar Arewa na aiki tare da Kungiyar Kare Muradun Arewa (ACF) da Kungiyar Dattawan Arewa (NEF) domin cin ma wannan manufa, kuma “Babu yadda za a yi mutum ya ci zaɓe na tare da samun goyon bayan waɗannan ƙungiyoyin ba.” Ya ƙara da cewa tsare-tsaren Tinubu ciki...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Duk da ƙarin kuɗin wutar lantarki da sabbin dokokin da aka yi don inganta ɓangaren, yawancin ’yan Najeriya na ci gaba da fama da karancin wutar da kuma tsadarta. Wannan matsalar babu wanda ta bari, daga manyan masana’antu zuwa ƙananan gidaje a sassa daban-daban a Najeriya. Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya sanar cewa gwamnati tana aiki don magance matsalolin, amma duk da haka ’yan Najeriya na ci gaba da kokawa kan matsalar, wadda ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. A watan Fabrairun 2024, Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu kan sabuwar Dokar Wutar Lantarki. Ta bayyana cewa munafar dokar ta haɗa da taimakawa da kuma bai wa jihohi damar samarwa, turawa, da kuma rarraba wutar lantarki na ƙashin kansu...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Tattaunawar makamashin nukiliya wani zaɓi ne mai mahimmanci wanda ya ƙarfafa matsayin Iran a duniya Ministan harkokin wajen kasar Iran Seyyed Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa; Kasarsa ta shiga shawarwarin makamashin nukiliya ba na                         kai tsaye ba da Amurka bisa wata cikakkiyar shawarar kasa. Ya kara da cewa; Wannan mataki na diflomasiyya ya karfafa kimar Iran a duniya, bayan da ta samu goyon bayan kasashe fiye da 120 wadanda suka yi Allah wadai da cin zarafin da yahudawan sahayoniyya suka yi wa Iran a baya-bayan nan. Hakan dai ya zo ne a yayin wata ganawa da aka yi da Araghchi, inda ya yi nazari kan batutuwan da suka shafi makamashin nukiliyar...
    Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran. Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba. A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mai ba da shawara ga Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya bayyana cewa: Hanyar Zangezur wata shiri ne na Amurka don matsawa kasashen Rasha da Iran. Ali Akbar Velayati mai ba wa Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran shawara kan harkokin kasa da kasa, ya dauki aikin Zangezur (arewa maso yammacin Iran) a matsayin wani aikin Amurka na matsawa kasashen Rasha da Iran lamba. A cikin wani sako na tunawa da Sheikh Safi al-Din Ardebili, Velayati ya yi tsokaci kan batutuwan da suka shafi Azarbaijan da mashigar Zangezur, yana mai cewa, “Makiya Iran karkashin jagorancin ‘yan sahayoniyyan duniya da Amurka, suna neman ta hanyar tsare-tsare irin su mashigar Zangezur, don ciyar da manyan ayyukan siyasa a karkashin fakewa da...
    Babban jami’in kungiyar Hamas a Zirin Gaza ya bayyana cewa: Makiya yahudawan sahayoniya suna rufe gazawar sojojinsu da kisan kare dangi Khalil al-Hayya babban jami’in kungiyar gwagwarmayar Musulunci  ta Hamas a zirin Gaza ya jaddada cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya suna rufe gazawar sojojinsu ta hanyar kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen hula. A cikin wani jawabi kai tsaye ta gidan talabijin, Al-Hayya ya bayyana cewa: “Ya ku ‘ya’yan Dakarun Qassam, da na Quds Brigade, da kuma sauran kungiyoyin gwagwarmaya, abin da kuke yi ya kawo cikas ga farmakin da motoci masu sulke na makiya suke yi. Khalil ya jaddada cewa: Babban hafsan hafsoshin sojin makiya yana rufe gazawar sojojinsa da kisan kare dangi da suke aiwatarwa kan fararen...
    Dakarun kasar Yemen sun sanar da sabbin zabukan kara rurutan bude wuta kan makiya a matsayin martani ga abubuwan da suka faru a Gaza Dakarun sojin kasar Yemen sun bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin jiya Lahadi cewa: Suna tunanin zafafa yakin da suke yi da ‘yan mamaya dangane da abin da ke faruwa a Zirin Gaza na kisan kare dangi da kakaba masifar yunwa kan al’ummar yankin. Rundunar sojin kasar ta Yemen ta tabbatar da fara aikin killace teku kashi na hudu a kan makiya, inda zasu kai hari kan dukkanin jiragen ruwan kamfanonin da ke aiki a tashar jiragen ruwa na Isra’ila, ba tare da la’akari da kasarsu ba, da kuma duk inda sojojin...
    Fiye da mutane 21 ne suka mutu a wani harin ta’addanci da aka kai kan wani coci a gabashin Kongo Rahotonni sun tabbatar da cewa; Sama da mutane 21 ne aka kashe a wani hari da mayakan ‘yan tawayen kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) suka kai kan wani cocin Katolika da ke gabashin Kongo, wanda ya hada da kona gidaje da shaguna a yankin. A ranar Lahadin da ta gabata ne mayakan da suke da alaka da kungiyar Allied Democratic Forces (ADF) da ke samun goyon bayan kungiyar ‘yan ta’adda ta ISIS suka kaddamar da harin ta’addanci kan wata majami’ar Katolika a gabashin Kongo. “Sama da mutane 21 ne aka kashe a ciki da wajen cocin,” Dieudonné Duranthabo, wani jami’in...
    An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja. Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar Asabar. Kifewar kwalekwalen ta auku ne a sakamakon karonsa da wani kututture bayan ya ɗauki fasinjojin daga yankin Guni zai kai su kasuwar mako-mako da ke yankin Zumba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro. Manajan Hukumar Albarkatun Koguna ta Ƙasa (NIWA), mai kula da yankin, Akapo Adeboye, ya ce an gano gwawar mutum 15, amma ana ci gaba neman wasu mutum uku, ko da yake cewa...
    An gano gwawar mutum 15 a yayin da ake ci gaba neman wasu uku bayan hastarin kwalekwale da ya auku a yankin Ƙaramar Hukumar Shiroro da ke Jihar Neja. Kwalekwalen ya kife ne a yayin da yake ɗauke da mutum 43 da buhuna 60 na shansherar shinkafa da shanu uku da tumaki biyu a ranar Asabar. Kifewar kwalekwalen ta auku ne a sakamakon karonsa da wani kututture bayan ya ɗauki fasinjojin daga yankin Guni zai kai su kasuwar mako-mako da ke yankin Zumba da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro. Manajan Hukumar Albarkatun Koguna ta Ƙasa (NIWA), mai kula da yankin, Akapo Adeboye, ya ce an gano gwawar mutum 15, amma ana ci gaba neman wasu mutum uku, ko da yake cewa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ’Yan Najeriya da dama ne dai aka bayyana ba sa fitowa kaɗa kuri’a a duk lokacin da zaɓe ya zagayo. Wasu daga cikin ’yan ƙasar sun bayyana rashin jin daɗin abun da hukumar zaɓe ke yi, rashin yarda da sakamakon zaɓuɓɓukan da suka gabata da dai sauransu a matsayin dalilansu na rashin kaɗa ƙuri’a. Ko waɗanne matakai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) take ɗauka don ƙarfafawa ’yan Najeriya gwiwan fitowa su kada ƙuri’a a zaɓen 2027? NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makaranta Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A...
    Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin, Zhao Leji, ya kai ziyarar sada zumunta a kasar Kyrgyzstan daga ranar 23 zuwa 24 ga wata, inda ya gana da shugaban kasar Kyrgyzstan Sadyr Nurgozhoevich Japarov a birnin Bishkek. Yayin ganawarsa da Japarov, Zhao Leji ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa tare da kasashen tsakiyar Asiya ciki har da Kyrgyzstan, don inganta gina al’umma mai makoma bai daya tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya. Japarov ya bayyana cewa, layin dogo tsakanin Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan, ba wai wata muhimmiyar hanyar sufuri ce kadai ba, har ma wata “hanyar abokantaka” ce dake sa kaimi ga bunkasar tattalin arzikin yankin.(Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Domin neman mafita da samar da zaman lafiya mai ɗaurewa, gwamnan ya kafa kwamiti na musamman da zai hhaɗa ukkanin bɓangarorin da abin ya shafa da jami’an gwamnati domin daddale asalin filayen da aka ware domin noma da ware iyakokin noma da kuma na kiwo domin tabbatar da adalci da gaskiya a tsakanin kowane ɓangare. Gwamnan ya jaddada cewa dukkanin ɓangarorin biyu na manoma da makiyaya kowa na da rawar da yake takawa wajen ci gaban tattalin arziki, don haka ya nemi a mutunta juna a zauna lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    A dai-dai lokacinda hankalin mutane da dama suka tashi dangane da abinda ke faruwa a Gaza, kasashen Faransa da saudia sun shirya gudanar da gagarumin Taro a birnin New na kasar Amurka a dai-dai lokacinda ake gudanar da babban taron majalisar dinkin duniya na shekara-shekara. Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Faisal Bin Farhan yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, za’a gudanar da taron a ranar 28-29 ga watan Yulin da muke ciki , kuma akwai fatan kasashen duniya zasu tattaunawa wannan batun sosai don kawo karshen rikicin gabas ta tsakiya bayan shekaru fiye da 70 ana gudanar da ita. Ministan ya kara da cewa a wannan taro...
    Majiyar sojojin HKI ta bada sanarwan cewa sun tsaida yaki na wucin gadi a gaza, don baya kungiyoyin agaji na MDD su shigar da abinci zuwa zirin gaza inda Falasdinawa suke mutuwa saboda yunwa. Babu wata majiya ta MDD ko kuma na kungiyoyin agaji masu zaman kansu da suka tabbatar da labarin. Kuma mafi yawan kungiyayin sun bayyana cewa sai gani a kasa. Don hki ba abar amincewa bace. Tun shekara ta 2023 ne HKI ta kara tsananta hana shigo da abinci gaza.
    Allah Ya yi wa tsohon shugaban Jami’ar Tarayya ta Kashere da ke Jihar Gombe, Farfesa Alhassan Gani, rasuwa a safiyar Lahadi a wani asibiti da ke Abuja. Ya rasu yana da shekaru 66 a duniya. Gwamnatin APC ta jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — Shugabar LP Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Kafin rasuwarsa, Farfesa Gani yana koyarwa a Sashen Kimiyyar Halittu na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi. Farfesa Gani, ya yi fice wajen sadaukar da kansa wajen ci gaban ilimi, musamman lokacin da yake jagorantar Jami’ar Kashere. Gwamna Inuwa Yahaya ya aike da saƙon ta’aziyyarsa Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana rasuwar Farfesan a matsayin babban rashi ga harkar ilimi da...
    Ma’aikatar sharia a nan Tehran ta bada sanarwan yake hukuncin kisa kan mutane biyu mambobi a kungiyar yan ta’adda ta MKO ko wadanda aka fi sani da munafukai. Kamfanin dillancin larabann Tasnim na JMI ya nakalto majiyar ma’aikatar na cewa mutanen biyu  Mahdi Hassani da Behrouz Ehsani, sun yi amfani da makamai wadanda suka hada da gurneti da kuma wasu ind suka kashe mutane fararin hula a dai dai lokacinda ake hargitsi a cikin kasar don tada hankalin mutane da kuma wargaza harkokin tsaro a cikin kasar. Labarin ya kara da cewa an tabbatar da tare da wata shakka ba suna aiki tare da kungiyar ta MKO wadanda suke adawa da JMI tun ranar kafa ta. Kungiyar MKO dai it...
    Janar majid Khatami Shugaban Bangaren Leken Asiri Na dakarun IRGC masu kare juyin juya halin musulunci ya bayyana cewa, rundunarsa tana sa ido akan take –taken kasashen Turai dangane da ayyukan sharrin da HKI take gudanarwa a yankin. Ya kuma kara da cewa rundunarsa tana da hanyoyin wadanda zata yi amfani da su , wanda daga karshe turawan ne zasu cutu a goyon bayan da suke bawa HKI. Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya nakalto Janar Majid Khatami yana fadar haka a lokacinda yake jawabi a taron addu’a da girmama Ghulam Hussan Ghaiba a nan Tehran. Dangane da marigayin ya bayyana cewa ya kasance cikin wadanda suka je yakin kare kasa na shekaru 8, kuma a cutu da makaman guban da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya zanta ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Afganistan Amir Khan Muttaki a yau Lahadi inda bangarorin biyu suka tattauna dangantaka tsakanin kasashen biyu da kuma al-amuran yankin wadanda suka hada da batun gaza da kuma halin da take ciki. Kamfanin dillancin labaran Tasnima na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana cewa kasar Iran ta kira taron gaggabawa na kungiyar OIC ta kasashen musulmi don tattauna wannan batun. A nashi bangaren muttaki ya bukaci gwamnatin kasar Iran ta maida yan kasar Afganistan wadanda suke zauna a kasar zuwa gida tare da mutuntasu. Kafin haka dai a lokacin yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da Iran jami’an tsaro a kasar...
    An fitar da wani sabon tsarin aiki na Shanghai na gina wani yanki da zai zamo kan gaba a fagen tafiyar da motoci masu tuka kansu jiya Asabar, yayin da ake ci gaba da gudanar da taron fasahar kirkirarriyar basira na duniya a birnin dake kudancin kasar Sin. An tsara shirin ne da nufin ganin motoci masu tuka kansu a mataki na 4 sun yi jigilar fasinjoji fiye da miliyan shida nan da shekarar 2027, tare da bude hanyoyi sama da kilomita 5,000 domin motocin masu tuka kansu, tare da tabbatar da cewa an sanya wa fiye da kashi 90 cikin dari na sabbin motocin birnin na’urorin tuka kai na mataki na 2 da kuma mataki na 3. An rarraba...
    Muƙaddashiyar Shugabar Jam’iyyar LP, Sanata Nenadi Esther Usman, ta ce gwamnatin APC ce ta fi jefa ’yan Najeriya cikin talauci sama da kowace gwamnati a tarihin ƙasar nan. Da ta ke zantawa da manema labarai a Jihar Kaduna, Sanatan ta ce jam’iyyar LP ta shirya tsaf don gyara kurakuran da gwamnatin APC ta tafka. Gwamna Bauchi ya sasanta manoma da makiyaya a Darazo Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa Ta roƙi ’yan Najeriya da su bai wa LP goyon baya, inda ta ce jam’iyyar za ta kawo canji na gaskiya. Ta ce halin da ake ciki na wahala a ƙasar nan ya yi muni ƙwarai, kuma ta d6ora alhakin hakan kan gwamnatin APC. Game da sauya...
    Daga ranar 24 ga wata, zuwa jiya Asabar 26 ga wata, an gudanar da babban taron kasa da kasa, dangane da fasahar rage asarar hatsi a birnin Jinan na kasar Sin, inda a wajen taron aka sanar da sakamakon da kasar Sin ta samu a fannin takaita asarar hatsi. An bayyana cewa, a bangaren asarar hatsi da a kan samu yayin da ake girbin hatsi da injuna, yawan asarar alkama, da shinkafa, da masara, da aka samu a kasar Sin a shekarar 2024, ya kai kaso 0.93%, da 1.76%, da kuma 2.06%, adadin da ya ragu da kaso 1% zuwa kaso 2%, bisa na shekarar 2021, ta yadda aka magance asarar hatsin da yawansa ya kai kilo biliyan 25 cikin...
    Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya jagoranci zaman sasanci domin kawo zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da manoma a garin Nahuta da ke Ƙaramar Hukumar Darazo. Wannan sasanci na zuwa ne bayan makonni uku da aka shafe ana rashin jituwa tsakanin ɓangarorin biyu. Ambaliya ta yi ajalin mutane, ta lalata gidaje a Adamawa LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman A taron da aka yi a ranar Lahadi, gwamnan ya yaba da yadda dukkanin ɓangarorin suka fahimci juna. Gwamna Bala, ya buƙaci jama’a da su guji duk wani abu da zai tayar da hankali, tare da yin kira a bin doka da oda. Ya ce gwamnati tana ɗaukar matakai domin hana rikici...
    Babban sufeton ƴansanda na ƙasa, Kayode Egbetokun ya sake tabbatar da ƙoƙarin rundunar wajen tabbatar da cikakken tsaro a faɗin ƙasar nan ta hanyar samun bayanan sirri daga jami’ansu. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan ya ce rundunar ta duƙufa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan, sannan ya buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanan sirri da goyon baya domin samar da tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane da dama tare da lalata gidaje a Ƙananan Hukumomin Yola ta Arewa da ta Yola Kudu a Jihar Adamawa. Ruwan sama mai ƙarfi da ya fara sauka tun da safiyar ranar Lahadi, ya haifar da ambaliya mai tsanani a sassan birnin. An gabatar da kundin dokar hana cin zarafin mata a Gombe Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF Yankunan da lamarin ya shafa sun haɗa da Yola Bye Pass, Sabon Pegi, Yolde Pate, da Modire. Gidaje da dama sun nutse, gonaki sun lalace, hanyoyi kuma sun katse, lamarin da ya hana mutane da ababen hawa zirga-zirga. Rahotanni sun nuna cewar mutane da dama sun rasu, ciki har...
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja. A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10. Ya ce wannan nasara wata hanya ce da ke ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya. Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata  Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC...
    Idan aka aiwatar da wannan aiki yadda ya kamata, zai iya zama abin koyi a tsarin samar da gidaje a Nijeriya. Amma in aka bar shi ya faɗa cikin halin almubazzaranci da rashin kulawa da ya jima yana faruwa, to zai iya zama wani sabon abin misalin da ba zai amfani talaka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya (Super Falcons) ta samu a gasar cin kofin Afrika na mata (WAFCON) 2025, inda ya ce yana sa ran karɓar kofin daga hannunsu a Abuja. A cikin wata hira ta bidiyo da aka yi da shugaban ƙasa jim kaɗan bayan wasan, tare da kyaftin din tawagar, Rasheedat Ajibade, da wasu ‘yan wasan da jami’an tawagar, Tinubu ya taya su murna bisa lashe kofin karo na 10. Ya ce wannan nasara wata hanya ce da ke ɗaukaka darajar Nijeriya a idon duniya. Nijeriya Ta Lashe Gasar Kofin Nahiyar Afirika Ta Mata  Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban APC...
    A ƙoƙarinta na daƙile cin zarafin mata da yara, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus, ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi mata (GBV) ga Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun goyon bayan sarakunan gargajiya wajen aiwatar da dokar a matakin ƙasa. Taron da aka gudanar a zauren Ƙaramar Hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’ai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma. LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF A wajen taron, Kwamishinar ta jaddada cewa dokar na buƙatar goyon bayan al’umma gaba ɗaya, musamman sarakunan gargajiya,...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Da marecen jiya Asabar ne dai sojojin HKI su ka kutsa cikin jirgin ruwan da yake dauke da masu fafutuka da su ka fito daga kasashe mabanbanta, wadanda suke son zuwa bagar ruwan Gaza domin kawo karshen killace yanki da aka yi tun 2006 da kuma kisan kiyashin da HKI take yi musu. Kananan jiragen ruwa na sojojin HKI ne su ka nufi jirgin ruwan mai suna; “Hanzalah” sannan su ka kutsa cikinsa. Bayan shigar sojojin cikin jirgin ruwan sun hau cikinsa sannan su ka fara  dukan mutanen da suke cikinsa.  MAsu kula da jirgin na Hanzalah sun bayyana cewa; Sojojin HKI sun kame mutanen da suke cikin jirgi tare da yin awon gaba da su, zuwa wani wuri. Dama...
    Ana samun Karin bakaken fatar Amurka da suke baro kasar suna dawo wa nahiyar Afirka domin samun kyakkyawar rayuwa a cikinta. Mafi yawancin bakaken fatar suna nuna rashin gamsuwarsu da yanayin tattalin arziki da kuma siyasa na Amukra da su ka taka rawa wajen sa su, daukar matakin komawa Afirka da can ne asalin kakanninsu. Wani dan kasar Amurka da ya rika yawo a tsakanin kasashe mabanbanta na Afirka a karshe ya tare a kasar Kenya, ya bayyana yadda yake jin ya saje a cikin nahiyar Afirka fiye da a can Amurka. Auston Holleman wanda ya shahara da wallafa sakwanni a You Tube ya kara da cewa; Dukkanin mutane a Afirka sun yi kama da juna, ba  kamar acikin turai,...
    Dubban ‘yan Najeriya magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta ” Super Falcon” sun yi bikin samun nasarar da kungiyar tasu ta samu, wasan karshe na samun kofin nahiyar Afirka na kwallon kafa na mata. A wasan da aka yi kafin hutun rabin lokaci, ‘yan wasan kasar ta Moroko sun yi bajinta, inda  su ka ci kwallaye 2-0, sai dai bayan komawa hutu, ‘yan wasan na Najeriya sun farke kwallon da aka zura musu, sannan kuma su ka kara da daya akai.  Sai dai duk da cewa an sami galaba akan kungiyar kwallon kafar ta Moroko, magoya bayanta da suke bakin ciki, sun jinjinawa kungiyar tasu. Wasu sun bayyana cewa ba su tsammaci za a sami galaba akansu ba,, domin sun...
      Alamomin wannan cuta ta zafin Mahaifa ita ce: 1) Ciwon mara mai daurewa (2) Wasan al’ada (3) Ganin jinı dunkule-dunkule lokacin al’ada.   Yadda za a magance: Sai ki nemi Sanya da Shammar da Albabinaj da Zuma sai ki tafasa su sannan ki riga sha sau uku a rana.   2. Matsala ta biyu sanyin Mahaifa: Wannan shi ne ake ce masa sanyin mahaifa. Shi ne idan abu ya shiga cikin mahaifar sai sanyi yaí masa yawa sai ya kasance ya fi yadda ake bukata saboda haka ciki ba zai samu ba donmin yana zarce kwana arba’in yana matsayin maniyyi bai koma jini ba, don haka ciki ba zai samuba.   Alamun sanyi mai hana haihuwa 1- Fitar farin...
    Daraktan Gidajen Rediyon Muryar Nijeriya (VON), Jibrin Ndace, ya bayyana cewa an kammala shirin fara watsa shirye-shirye da harshen Mandarin, wanda shi ne harshe a hukumance na ƙasar China. Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai tare da tawagar VON ga Jakadan China a Nijeriya, Yu Dunhai. Ndace ya ce ƙara harshen Mandarin zai kawo yawan harsunan da VON ke amfani da su zuwa tara. A yanzu, hukumar na watsa shirye-shirye da Hausa, Igbo, Yarbanci, Fulfude, Turanci, Faransanci, Larabci da Swahili. Ya bayyana cewa dukkan kayan aiki da tsare-tsare sun kammala don fara aikin, da nufin tabbatar da ɗorewar wannan sabon shiri. China Ta Mayar Da Martani Kan Barazanar Trump Na Ƙarin Haraji Ga...
    Shugaban kasar Iran ya yi kiran cewa: Ina masu fafutukar kare hakkin bil’adama suke a bala’in Gaza? Shugaban kasar Iran Dr. Masoud Pezeshkian ya jaddada muhimmancin sauya salon tafiyar da gwamnati da kuma karfafa alaka da kasashen da ke makwabtaka da ita, yana mai cewa masu takama da kare hakkin bil’adama suna nuna fuska biyu a aikinsu, inda suka yi shiru kan munanan laifukan da ake yi wa al’ummar Gaza. A safiyar yau ne shugaba Pezeshkian ya isa ma’aikatar harkokin wajen kasar, inda ya gana da mataimakan ministoci da daraktocin ma’aikatar. A lokacin da yake jawabi a taron, shugaban ya ce, “Tun da yake dan majalisar shawarar Musulunci bai canza ba, har yanzu shi mutum daya ne, dole ne al’umma...
    Isra’ila ta ce za ta bai wa ayarin Majalisar Dinkin Duniya damar shiga Gaza domin raba kayan agaji da magani, bayan makonni na matsin lamba daga hukumomi da kasashen duniya. Sanarwar da rundunar sojin Isra’ila ta fitar ranar Asabar, ta ce ta bayar damar komawa jefa kayan agajin ta jiragen sama – abin da aka ce bai wadatar ba, baya ga hadarin da ke tattare da shi. Super Falcons ta lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark Rundunar sojin ta ce ta fara aiwatar da wasu jerin matakai na inganta kai agajin a yankunan da ke da tarin jama’a Hakan dai na zuwa ne a yayin...
    Kasar Iran ta bayyana sake kulluwar hulda da Amurka ta hanyar masu shiga Tsakani Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa Majid Takht-Ravanchi ya sanar da cewa: Wasu kasashe na tuntubar Iran da Amurka a matsayin masu shiga tsakani. Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran mai kula da harkokin siyasa ya shaidawa tashar Haber Turk ta Turkiyya cewa: Akwai tuntuba tsakanin Iran da Amurka ta wasu kasashe masu shiga tsakani, yana mai cewa: “Wasu kasashe suna hulda da Iran da Amurka, kamar yadda kuka sani, don haka Iran tana tattaunawa da Oman a matsayin mai shiga tsakani.” Da yake amsa tambaya game da ganawar da kungiyar Tarayyar Turai a Istanbul, ya ce: “Iran ta sake gudanar...
    Shugaban kasar Amurka ya shiga sahun masu mafarkin zasu rusa kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ke Falasdinu Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi barazanar kawar da kungiyar Hamas idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba, yana mai zargin kungiyar da rashin son cimma matsaya. A halin da ake ciki kuma, fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sanar da cewa; Yana nazarin hanyoyin da Amurka za ta bi domin kwato fursunonin yahudawan sahayoniyya daga Gaza. Da alama mai shiga tsakani na Amurka ya yanke shawarar jagorantar kai farmakin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke kaiwa Gaza, inda shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta kawar da kungiyar Hamas. Ya yi ikirarin cewa: Kungiyar...
    Amfani da man kwakwa da man Amla: Daga farko ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man Amla. Daga nan sai ki gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin ya huce. Sannan ki zuba man a kwalba kina shafa wannan hadin a fatar kanki da gashinki kamar sau uku a sati. Amfani da Lemon Tsami: Ki samu ruwan Lemun Tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma man Amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar hadin a kanki har tsawon minti talatin, sannan ki wanke da ruwan Dumi. Za ki iya yin wannan hadin sau biyu a wata. Amfani da Alo Bera:...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, ta sake kafa tarihi bayan ta doke ƙasar Maroko da ci 3–2 a wasan ƙarshe na gasar WAFCON. Yanzu haka Super Falcons ta lashe kofin karo na 10, wanda shi ne adadi mafi yawa da wata ƙasa ta taɓa lashewa a tarihin gasar. ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba Maroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu cikin mintuna 25 ta hannun Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy, lamarin da ya tayar da hankalin magoya bayan Super Falcons a filin wasa na Rabat. Amma Najeriya ba ta karaya ba. A minti na...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta kaddamar da dashen itatuwa na shekarar 2025 tare da sabunta kudirin farfado da fiye da hekta 5,000 da ta lalace a fadin jihar. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a wajen bikin kaddamar da shirin da aka gudanar a shatale-tale na Pentagon da ke Dutse babban birnin jihar.   Ya bayyana aikin dashen itatuwan a matsayin ɗaya daga cikin alkawuran da gwamnatinsa ta ɗauka domin ci gaban al’umma, inda ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen raya muhalli da kare shi. Ya ce: “Wannan yana da alaƙa da manufofinmu da suka shafi ƙaddamar da tsare-tsare da suka dace da kare muhalli, da ƙarfafa juriya da dorewar muhalli, da kuma...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, ta sake kafa tarihi bayan ta doke ƙasar Maroko da ci 3–2 a wasan ƙarshe na gasar WAFCON. Yanzu haka Super Falcons ta lashe kofin karo na 10, wanda shi ne adadi mafi yawa da wata ƙasa ta taɓa lashewa a tarihin gasar. ADC ce kaɗai za ta iya magance matsalolin Arewa — David Mark Dole gyaran kundin tsarin mulki ya haɗa kan ƙasa da shugabanci na gari — Abba Maroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu cikin mintuna 25 ta hannun Ghizlane Chebbak da Sanaa Mssoudy, lamarin da ya tayar da hankalin magoya bayan Super Falcons a filin wasa na Rabat. Amma Najeriya ba ta karaya ba. A minti na...
    Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2. An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo. Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya Ƙasar Moroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu a minti na 14 da minti 24. Amma Nijeriya ta farke duka ƙwallaye biyu kuma ta jefa ta uku a minti na 89 na wasan, da wannan sakamakon Nijeriya ta samu nasarar lashe gasar karo na 10 a...
    Tawagar ƙwallon ƙafa ta mata a Nijeriya (Super Falcons) ta samu nasarar lashe kofin ƙasashen nahiyar Afirika na mata bayan doke masu masaukin baƙi Maroko a wasan ƙarshe da ci 3 da 2. An buga wasan ne a daren ranar Asabar, wanda ya ƙayatar da masu kallo. Musuluntar Wata Ce Ya Ja Hankalina Shiga Fim – Sailuba Dadin Kowa Masanin Kimiyyar Na’ura Mai Kwakwalwa Robert Tarjan Ya Jinjinawa Dabarun Sin Na Ingiza Ilimin Kimiyya Ƙasar Moroko ce ta fara jefa ƙwallaye biyu a minti na 14 da minti 24. Amma Nijeriya ta farke duka ƙwallaye biyu kuma ta jefa ta uku a minti na 89 na wasan, da wannan sakamakon Nijeriya ta samu nasarar lashe gasar karo na 10 a...
    Tsoffin gwamnoni da suka fara mulki a shekarar 1999, da ake kira “Class of ’99,” sun gana da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Fadar Gwamnati da ke Abuja a ranar Juma’a, inda suka gabatar da shawarwari na aiki domin magance matsalolin tsaro, inganta tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi a fadin ƙasar. Tawagar, ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnan Jihar Edo, Lucky Igbinedion, ta haɗa da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume, da wasu tsoffin gwamnoni da suka yi mulki tare da Shugaba Tinubu lokacin da yake Gwamnan Jihar Lagos. Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar da ta ɗauki fiye da awa guda, Igbinedion ya bayyana cewa ziyarar tasu na da nufin yin wata ganawa da ɗan...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.” Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar. Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin...
    Masu karatu za su so jin dan takaitaccen tarihinki? An haife ni a garin Gombe, amma sai daga bisani na bar garin Gomben da zama na dawo Kano, tun ina ‘yar shekara biyar da haihuwa, sakamakon mahaifina yana aiki a Kanon. Kazalika, na girma a gaban iyayena, na yi firamare da sakandare duk a garin Kano, sannan kuma ban taba yin aure ba; budurwa ce ni.   Wace irin rawa kike takawa a cikin masana’antar shirya finafinai ta Kannywood? Ina fitowa ne a matsayin Jaruma kawai, amma kuma ina da niyyar zama mai bayar da umarni a nan gaba kadan insha Allah.   Me ya ja hankalinki, har kika tsunduma harkar fim? Wato batu na gaskiya, fim yana burge ni...