Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA
Published: 30th, June 2025 GMT
A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli da dama ga tsaron yankin da ma duniya baki daya.
A yayin wannan tattaunawa, shugaba Pezeshkian ya ce, wadannan ayyuka na nuna fuska biyu sun haifar da matsaloli da dama ga harkokin tsaro na yanki da na duniya, kuma ana sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA za ta mutunta haƙƙin kasashe da guje wa ɗabi’a nuna fuska biyu a fagen ayyukanta da kuma kare haƙƙin ƙasashe membobinta.
A martanin da shugaban kasar Faransa ya nuna dangane da matakin Iran na dakatar da hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, shugaba Pezeshkian ya soki yadda babban sakataren hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ke bayar da rahotannin da ba su dace ba kan shirin makamashin nukiliyar Iran da kuma rashin yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: hukumar kula da makamashin nukiliya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Tinubu Ya Rantsar Da Farfesa Dakas James Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki Ta Kasa
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ɗakin taro na Majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.
Kafin a fara taron, Shugaban Ƙasa ya rantsar da Farfesa Dakas James Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki ta Ƙasa da Kwamishina.
Majalisar ta kuma dakatar da taron na minti ɗaya domin girmama marigayi Cif Audu Ogbe, wanda ya kasance memba a majalisar a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari, haka kuma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Cif Ogbe ya rasu a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78.
Daga Bello Wakili