Mummunan Hatsari Ya Lashe Rayukan ‘Yan Mata 18 A Kasar Masar Dukkaninsu ‘Yan Kasa DA Shekara 21
Published: 28th, June 2025 GMT
Wani mummunan hatsari ya afku a Masar inda ‘yan mata 18 suka mutu sakamakon fashewar wata motar dakon mai
Wani mummunan hatsarin mota ya afku a kasar Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mata 18 da direban bas a kan hanyarsu ta zuwa gonar inabin domin girbin inabin.
Hatsarin ya afku ne a ranar Juma’a a kan hanyar yankin da ke gundumar Menoufia, bayan wata babbar mota ta yi karo da motar bas din da ke dauke da ‘yan matan 18.
Hotunan wannan mummunan hatsarin da aka yi ta yawo da su a shafukan sada zumunta, sun nuna yadda motar bas din ta lalace gaba daya. Hotunan akwatunan gawarwakin ‘yan matan da aka jera su sun haifar da bakin ciki sosa a tsakanin al’umma.
Jami’an tsaro sun cafke direban babbar motar da ke da alhakin hatsarin bayan ya arce daga wurin. An mika shi ga ofishin gabatar da kara na gwamnati, wanda ke gudanar da bincike.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma 2 Sun Rasu, 2 Sun Jikkata A Wani Rikicin Filin Gona A Yobe
Rikicin filin gona ya yi sanadin mutuwar mutum biyu tare da jikkata wasu biyu a ƙaramar hukumar Gulani da ke Jihar Yobe. Lamarin ya faru ne a daren Asabar bayan ce-ce-ku-ce tsakanin mazauna ƙauyukan Zango da Azere, waɗanda ke tsakanin iyakokin Gujba da Gulani.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Dungus Abdulkarim, ya bayyana cewa shalƙwatar ƴansanda ta Bara ta samu kiran gaggawa daga shugaban ƙauyen Zango a ranar 9 ga Agusta, 2025, da misalin ƙarfe 11:30 na dare, inda ya sanar da cewa wasu ƴan daba daga ƙauyen Azere sun kai mummunan farmaki kan manoma.
Gwamnatin Yobe Za Ta Yi Taron Girmama Ɗalibar Turanci Ta Duniya, Nafisa Abdullah Afam Osigwe Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar Lauyoyi Ta KasaWanda aka kashe sun haɗa da Sani Makeri, mai shekara 40, da Abdullahi Maicitta, mai shekara 35, dukkansu ƴan asalin Zango. An garzaya da waɗanda suka jikkata an kai su zuwa babban asibitin Damaturu domin samun kulawa.
SP Dungus ya ce rikicin ya samo asali ne tun bara lokacin damina, duk da ƙoƙarin hukumar ƴansanda wajen sulhu ta hanyar kwamitin daidaita iyakoki na Jiha. Kwamishinan ƴansandan jihar, CP Emmanuel Ado, ya la’anci harin tare da bayar da tabbacin cafke masu laifi, kana ya ja hankalin manoma su guji ɗaukar doka a hannu su kuma nemi sulhu ta hanyar hukumomi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp