HausaTv:
2025-07-03@16:56:44 GMT

An Gudanar Da Taron Girmama Shahidan Yakin Kwanaki 12 A Nan Tehran

Published: 3rd, July 2025 GMT

A jiya laraba ce aka gudanar da taron addu’a da kuma girmama shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka farwa kasar Iran a ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gudanar da taron girmamawan ne a masallacin Imam Khomane (q) da ke nan Tehran.

Labaran ya kara da cewa shahidan yakin kwanaki 12 dai sun hada da manya-manyan sojojin kasar kwamandan dakarun IRGC shahida Hussain salami, da babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Shahid Muhammad Bakri da kwamandan rundunar sojojin Khatamul anbiya (s) da ke nan Tehran Ghulam ali Rashti. Da sauransu. Sai kuma masana fasahar makamashin nukliya guda 6 da kuma wasu fararen hula wadanda HKI da Amurka suka kashe a wurare daban daban  daga ciki har da yan jarida uku a tashar talabijin ta labarai na farisanci a nan Tehran.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya

Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran ta jaddada cewa: Gudanar da masana’antun nukiliyar kasar za ta ci gaba da kuma fadada bunkasar da suke samu

Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, dangane da yadda yahudawan sahayoniyya da Amurka suka kai hare-hare kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ya jaddada cewa: Masana’antar nukiliya ba wani abu ba ne da za a iya rusa shi ta hanyar jefa masa bam saboda fasahar masana’antar nukiliya irin ta Iran tana bunkasa ce da ilimummukan masana ‘yan asalin kasa da suke da zurfin fasahar ilimin.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya watsa rahoton cewa: Mohammad Islami shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya bayyana cewa, bayan wani taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Laraba, don tattaunawa kan yadda gwamnatin ‘yan sahayoniyya da Amurka suka kai harin wuce gona da iri kan cibiyoyin nukiliyar kasar Iran, cewa: Wannan farmakin da aka kai kan Iran, wani rauni ne ga kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya da kuma nuna cewa dokar daji ta mamaye duniya, kuma wadanda ba su da karfi ba za su iya ci gaba da rayuwarsu ba lamarin da tuni al’ummar Iran suka fahimci hakan da kyau.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kalibof Yace: Iran Zata Maida Martani Mai Tsanani Kan HKI Idan Ta Sake Bude Yaki da Iran
  •  Muhsin Rizai: Jagoran Juyin Musulunci Na Iran Ya Bayar Da Umarni  Da Jagorantar Yakin “Wa’adussadiq 3”
  • Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
  • An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin
  • Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila
  • Wargajewar HKI Ba Makawa Inji Wani Janar Daga Sojojin JMI
  • Laftanar Kanar Shikarci: Sojojin Iran Suna Cikin Shirin Ko-Ta-Kwana Fiye Da Kowane Lokaci
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce; Dokar Majalisar Shawarar Musulunci Ta Kasar Kan Hukumar IAEA Dole Ne Aiki Da Ita
  • Iran Ta Bukaci Gudanar Da Bincike Kan Dalilin Isra’ila Na Kai Harin Kan Gidan Yarin Tehran