HKI:Har Yanzu Matatar Man Fetur Ta Haifa Ba Ta Koma Aiki Ba
Published: 30th, June 2025 GMT
Majiyar ‘yan sahayoniya ta ce, sai zuwa watan Oktoba ne za a iya kawo karshen lalacewar da matatar man fetur din Haifa ta yi sanadiyyar harin makami mai linzami na Iran.
Jaridar “Time Of Isra’il” ta bayyana cewa a tsawon yakin kwanaki 12, Iran ta yi wa Isra’ila mummunan harin mai ciwo da sai yanzu ne sannu a hankali zurfinsa yake bayyana.
A jiya Lahadi ne matatar man fetur ta Haifa ta sanar da cewa; Wani karamin sashe nata ne zai fara aiki, saboda hare-haren makamai masu linzami na Iran.
Matatar man fetur din wacce ake kira da sunan : “BAZAN” ta ce sai zuwa wata Oktoba ne ake sa ran cewa za ta koma aiki baki daya.
A ranar 15 ga watan Yuni ne dai aikin matatar ya tsaya saboda hare-haren ramuwar gayya da Iran din ta kai, bayan da ‘yan sahayoniyar bisa cikakken goyon bayan Amurka su ka kawo wa Iran hari.
Ita dai wannan matatar man fetur din tana samarwa da HKI man fetur da ya kai kaso 59% da kuma Gas da ake amfani da shi a gidaje da ya kai kaso 52%.
A yayin harin, kamfani da yake tafiyar da matata ya sanar da halakar ‘yan sahayoniya 3.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya.
Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja.
Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaroYa ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025.
ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025.
A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da yajin aikin, don haka dukkanin malamai za su daina aiki a lokacin yajin aiki.
Wannan yajin aikin na zuwa ne duk da cewa har yanzu gwamnati da ASUU na ci gaba da tattaunawa don warware matsalolin da suka daɗe suna fama da su.
Wasu daga cikin matsalolinsu sun shafi batun albashi, kuɗaɗen alawus-alawus, da kuma yarjejeniyar da aka cimma tun shekarar 2009 tsakanin ɓangarorin biyu.
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya bayyana a ranar Laraba cewa gwamnati na matakin ƙarshe na tattaunawa da ASUU da sauran ƙungiyoyi don warware matsalolinsu.
Ya kuma ce gwamnati ta riga ta fitar da Naira biliyan 50 don biyan haƙƙoƙin malaman da suka cancanta, yayin da aka sake sakin wasu Naira biliyan 150 a kasafin kudin 2025 domin biyan buƙatun jami’o’i.