Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Cewa: Al’ummar Iran Masu Juriya Za Su Tsaya Tsayin Daka Waje Kare Hakkinsu
Published: 29th, June 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu juriya za su tsaya tsayin daka har zuwa digon jini na karshe a kan duk wanda ya nemi juya akalarsu.
Araqchi ya rubuta a cikin shafinsa na yanar gizo a dandalin sada zumunta na X cewa: “Har yanzu, al’ummar Iran masu girma sun nuna wa duniya karfinsu da juriyarsu.”
Ya kara da cewa: Karfin kadawar guguwar masu kishin kasa da suka fito kan tituna domin karrama shuwagabannin soji da suka yi shahada, malamai, masu bincike, da ‘yan kasa, ciki har da mata da kananan yara da ba su ji ba ba su gani ba, da matsoratan ‘yan sahayoniyya suka yi wa kisan gilla, dukkansu suna dauke da sako karara.
Araqchi ya ci gaba da cewa: Sabanin gwamnatin ‘yan sahayoniyya masu Rauni, marasa karfi, Iraniyawa ba su taba boye hasarar da aka yi musu. Suna alfahari da shahidansu, su ne abin koyinsu. Ku tabbatar cewa, kowane jami’i ko masanin kimiyya da Iran ta rasa, akwai ɗaruruwan da suke layi don maye gurbinsu.
Ya jaddada cewa: Al’ummar Iran masu karfi da juriya za su tsaya tsayin daka har sai digon jini na karshe a kan duk wanda ke son yanke hukunci kan makomarsu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Al ummar Iran masu
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki.
Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki.
Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,”
A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda yake kaiwa da komowa domin kare muradun al’ummar Kaduna, tare da tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar kammala aikin cikin lokaci. Ya bayyana cewa an umarci kamfanonin da ke aikin da su rika aiki sau biyu a rana domin hanzarta cigaba ba tare da rage inganci ba.
Ministan ya kara da cewa amfani da fasahar siminti mai ɗorewa wanda zai tabbatar da cewa titin zai dawwama tare da rage kudin gyara nan gaba.
Kamfanonin da ke aikin sun yi alkawarin ƙara gaggautawa musamman a yankin Jere dake jihar Kaduna, inda ake sa ido sosai kan ci gaban aiki. Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma tabbatar da ci gaba da haɗin kai da Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya domin magance ƙalubalen da ke iya janyo tsaiko.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA