Mai magana da yawun hukumar raya hadin-gwiwa da sassan kasa da kasa ta kasar Sin, Li Ming, ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, Sin ta riga ta kaddamar da ayyuka kimanin dubu 15 na inganta kwarewar ma’aikata karkashin hadin-gwiwarta da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa sama da 180, inda aka horas da kwararrun ma’aikata fiye da dubu 500 a bangarori daban-daban, al’amarin da ya taimaka wa kasa da kasa samun ci gaba.

Kana kuma, akwai ’yan kasashen Afirka da dama wadanda suka yi amfani da manufofi da dabarun kawar da talauci da suka koya a kasar Sin, don taimaka wa ayyukan yaki da fatara a kasashensu.

 

Kakakin ya kara da cewa, tun daga shekaru sama da 70 da suka gabata zuwa yanzu, kasar Sin na mayar da hankali kan ainihin bukatun kasashe masu tasowa ta fuskar neman ci gaba, da koya musu fasahohin zamani da akidun neman ci gaba, al’amarin da ya samar da goyon-baya ga bunkasar kasashe masu tasowa. (Murtala Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro.

Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000

A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje.

An ruwaito sun taɓa kashe ɗan sanda a shekarar 2024, kuma suna samun bayanai daga dilolin miyagun ƙwayoyi a wuraren shaƙatawa. A

An ƙwato bindiga ƙirar gida, gatari da adduna 13, mota, kwamfuta huɗu, wayoyi 13 da talabijin huɗu.

Haka kuma, a Nunbu Bashayi da ke Sanga, an kama mutane bakwai da ake zargi da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.

Dukkanimsu sun amsa laifinsu kuma ana neman ragowar waɗanda suke tsere.

A wani samame daban, ’yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata fashi, fyaɗe da damfara.

Sun saba kai hari gidajen mutane, ɗaukar kuɗaɗen mutane, aikata fyaɗe sannan su riƙa ɗaukar bidiyo tsoratar da mutane.

A Zariya kuwa, an kama wasu mutane tara da suka haɗa da maza da mata waɗanda ake zargi da yi wa direban Adaidaita sahu fashi ta hanyar zuba masa magani a abin sha.

Rundunar ta kuma kama wani likitan bogi mai suna Adamu Abubakar Muhammed wanda ya yi wa mutane tiyata ba tare da shaidar karatun likitanci ba.

Ya yi amfani da takardun bogi wajen yin aiki na tsawon wata guda kafin a gano shi.

Kwamishinan, ya ce duk waɗanda aka kama suna hannun rundunar, kuma za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.

Ya gode wa jami’an tsaro da al’umma kan haɗin kai, inda ya yi da a ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin inganta tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Kashe Sama da Naira Miliyan 5 Don Tallafawa Shirin AGILE
  • An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya- Shugaba Tinubu
  • Mutuwar Sheikh Dahiru Bauchi Babban Rashi Ne Ga Kasa Baki Daya
  • Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
  • ’Yan sanda sun kama masu laifi 34 a Kaduna
  • Larijani: Hadin gwiwar Iran da Pakistan na taimaka wa zaman lafiya a yankin
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Faduwar Darajar Kuɗi Na Kara Tsananta Kalubale Ga Kotunan Shari’a — CJN