To sai dai ana bibiyar kwallon kafa tsakanin magoya baya a Nahiyar Turai da Kudancin Amurka, sannan kowacce takan samar da fitattun ‘yan wasan da suke fice a nahiyar da kuma duniya a fannin kwallon kafa. Wannan yana biyo bayan zuba hannun jari da bunkasa wuraren wasan kwallon kafa da gasa mai inganci da kayatarwa musamman a Nahiyar Turai.

Nahiyar Turai ta lashe kofin duniya guda 12, idan ka kwanta da tara da Kudancin Amurka ta dauka a tarihi. Kungiyoyin Turai, musammam masu buga gasar English Premier League da Spanish La Liga da Bundesliga ko Serie A, sune suka mamaye lashe Champions League da kuma Club World Cup a tarihi.

Sannan nahiyar Turai tana zuba kudi da hannun jari a fannin ci gaban kwallon kafa ta matasa tun daga tushe, hakan ya sa kungiyoyinsu ba sa rasa ‘yan wasan da za su buga musu wasa, kuma masu inganci da kwarewa a manyan kungiyoyi.

Gasar wasan Turai tana da yanayi mai karfi a wasannin da ake yi, wanda mutane da yawa suka yi imanin tana da inganci da kayatarwa, hakan ya kan sa tawagar kasa kan yi kokari, duk lokacin da ta je babbar gasar kwallon kafa ta duniya.

Kudancin Amurka na da tarihin kwallon kafa, tare da fitattun ‘yan wasa irin su Pele da Maradona da Messi da sauransu da suka fito daga Kudancin Amurka. Ana matukar kaunar kwallon kafa a Kudancin Amurka. Kaunar kwallon kafa a kudancin Amurka kamar al’ada ce mai karfi, yadda ake kishin kungiya da yadda ake cika filayen wasa da samar da yanayi mai kayatarwa a lokacin da ake manyan wasanni.

Kudancin Amurka na ci gaba da samar da ‘yan wasa masu hazaka na musamman, amma yawancin ‘yan kwallon suna kaura zuwa Turai tun suna kanana, suna yin tasiri mai karfin a wasannin Turai, yayin da ake rashi daga Kudancin Turai. Idan za mu yi lissafin yawan samun maki a Club World Cup da ake bugawa a Amurka, Kudancin Amurka ce kan gaba da wasannin  da aka buka daga lokacin da aka hada wannan rahoton.

Mai biye da ita sai Nahiyar Turai, sannan sauran da suka bi baya a yawan hada maki a Club World Cup a bana. Tsakanin kungiya shida daga Kudancin Amurka, Botafogo ta samu maki shida, Flamengo maki bakwai, Fluminense maki bakwai, Riber Plate maki hudu, Palmeiras maki biyar da kuma Boca Juniors mai maki biyu, kenan jimilla maki 4.1.

Duk da Nahiyar Turai tana da kungiya 12 dake wakiltarta, tana da maki 48, idan kayi jimilla zai kai 4.00, kenan Kudancin Amurka ce kan gaba. Kenan za a samu kungiyoyin Kudancin Amurka da yawa da za su kai zagayen ‘yan 16, in ban da Boca Junior da ba ta yin kokari daga cikinsu kuma tuni ta fita daga gasar.

Nahiyar Afirka ce ta uku a kokari a Club World Cup mai matsakaicin maki 1.75, inda Mamelodi Sundowns ta hada maki hudu, sai Esperance Tunis mai maki uku da Al Ahly da Wydad Casablanca da ba su sami maki ko daya ba daga wasa biyu a cikin rukuni. Nahiyar Kudancin Amurka mai kungiya biyar ta samu matsaikacin maki 1.20, inda kungiyar Lionel Messi, Inter Miami ta samu maki biyar daga guda tara.

Nahiyar Asia ce ta biyar da maki 0.50, inda kungiyar Saudiyya, Al-Hilal ta samu maki biyu daga karawa uku kuma tuni ta fice daga gasar. Ta karshe ita ce Nahiyar Oceania mara maki, wadda aka durawa kungiyar New Zealand kwallo 16.

Za a iya cewa yayin da Kudancin Amurka ke da al’adar son kwallon kafa sau da kafa da kuma samar da ‘yan wasa na musamman ‘yan baiwa, Turai a halin yanzu tana kan gaba ta fuskar ingancin gasa, mai dan karen farin jini da kayatarwa sannan a Turai ana ci gaba da kokari wajen kawata wasannin kwallon kafa da fasahar zamani domin gujewa kuskuren alkalanci da kuma daidaita kashe kudade.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Nahiyar Turai kwallon kafa

এছাড়াও পড়ুন:

Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa

 

Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, kamar aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da kara musayar manyan jami’ai, da mu’amala kan manyan tsare-tsare, ta yadda za a inganta fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da cimma sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. (Mai Fassara: Maryam Yang)

 

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya October 10, 2025 Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yaushe Lamine Yamal Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
  • Zuwa Kofin Duniya: Za A Yi Ta Ta Kare A Nahiyar Afirka
  • Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon
  • Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh
  • Ayyukan Da Suka Sauya Fuskar Zamfara A Ƙarƙashin Gwamna Dauda Lawal
  • Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 
  • An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
  • Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa
  • Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha
  • Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka  Rusa A Arewacin Yankin