Iraki Ta Kai Karar HKI Kan Amfani Da Sararin Samaniyar Kasar Don Kaiwa Iran Hare hare
Published: 2nd, July 2025 GMT
Firai ministan kasar Iraki Muhammad Shia assudani ya bayyana cewa kasarsa ta shigar da karar HKI a gaban kwamitin tsaro na MDD saboda keta hurumin sararin samaniyar kasar don kaiwa kasar Iran hare-hare.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto sudani yana fadar haka, ya kuma kara da cewa HKI ba tare da neman izinin gwamnatin kasar ba a cikin yakin kwanaki 12 da JMI ta shiga sararin samaniyar kasar daga nan kuma ta kai hare-hare kan sansanonin sojojin da kuma cibiyoyin fararen hula daga kasar ta Iraki.
Duk ba tare da amincewar kasar ba.
Firai ministan ya yi allawadai da hare-haren ya kuma bukaci a huklunta HKI kan hakan. Y ace kasar Iraki bata da garkuwan sararin samania isassu wadanda zasu kare ta daga shigowar kasar ta Iraki.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Ba Za A Iya Kawar Da Fasahar Nukiliya Da Karfi Ba
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a iya kawar da fasahar nukiliya ta hanyar harin bam ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Ba za a iya kawar da fasaha da kimiyyar da ake bukata don inganta sinadarin Uranium ta hanyar kai hare-haren bama-bamai ba.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta CBS, Araqchi ya yi tsokaci kan ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na cewa ana iya komawa tattaunawa da Iran a cikin wannan mako: Araqchi yana mai mayar da martini da cewa: “Ba ya jin za a dawo da tattaunawar cikin gaggawa.”
Ya kara da cewa: “Kafin yanke shawarar komawa kan tattaunawar, dole ne Iran ta fara tabbatar da cewa Amurka ba za ta sake kai wa kasarta harin soji ba yayin tattaunawar.”
Ya ce: Ya yi imani tare da wannan la’akari, cewa har yanzu Iran tana bukatar karin lokaci, amma kofofin diflomasiyya ba za su taba rufewa ba.