Aminiya:
2025-10-13@15:50:00 GMT

Zan yi takara a Zaɓen 2027 — Peter Obi

Published: 1st, July 2025 GMT

Tsohon Gwamnan Anambra, Peter Obi ya ce zai yi takarar shugabancin Nijeriya a 2027 domin ba zai shiga duk wata yarjejeniyar haɗakar takara da kowa ba.

Obi wanda ya yi takarar shugabancin Nijeriya a Zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar Labour (LP), ya tabbatar wa magoya bayansa cewa babu gudu babu ja da baya dangane da takararsa a babban zaɓen kasar na gaba.

An sanya dokar hana fita a Kaduna An ɗage jana’izar Aminu Ɗantata zuwa Talata

Sai dai ya ce idan har akwai wata yarjejeniya da zai kulla, ba za ta wuce wacce za ta ba shi damar zama shugaban ƙasa na wa’adi daya ba, sannan ya miƙa wa shugaba na gaba mulki a ranar 28 ga watan Mayun 2031.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar, Obi ya bayyana hakan a yayin amsa tambayoyin magoya bayansa  wata hira ta kai tsaye da aka yi da shi a shafin X a ranar Lahadi.

Obi ya musanta kulla yarjejeniyar tsayawa takara a karkashin tikiti daya da tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar.

Haka kuma, Obi ya ce duk wata haɗaka da za a yi wadda ba ta da kudirin kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihohin Benuwe da Zamfara…da kuma bunkasa tattalin arzikin Nijeriya, to kuwa babu shi babu ita.

Kazalika, Obi ya ce yana goyon bayan tsarin da zai bayar da damar a rika karɓa-karɓar mulki a tsakanin Kudu da Arewacin Nijeriya.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas October 2, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zaɓen Kamaru: Tchiroma Bakary na da kwarin gwiwa a yayin da ake jiran sakamako
  • Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi ASUU Kan Yajin Aiki, Ta Ce “Babu Aiki, Babu Albashi”
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice  
  • Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa
  • Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia
  • Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
  • Maƙiyan Jonathan Ne Kaɗai Za Su Zuga Shi Ya Fito Takara A 2027 – Oshiomhole
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya
  • 2027: INEC Ta Nemi A Gaggauta Amincewa Da Ƙudirin Sake Fasalin Tsarin Zaɓe