Leadership News Hausa:
2025-11-27@22:28:14 GMT

2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu

Published: 29th, June 2025 GMT

2027: Ƴan Adawa Na Ƙara Ƙaimin Kawar Da Tinubu

Wannan ne ma dalilin da yasa wasu ke ganin hadakar za ta iya yin karfi kwarai da gaske, kasancewar ta samu wakilci a sassa daban-daban na wannan kasa.

Dalili kuwa shi ne, ‘yansiyasa ne da a baya suka samu damar rike manya-mnyan mukamai, sannan kuma har zuwa yanzu yana da tasiri a fagen siyasar kasar yadda ya kamata.

Manya-manyan jiga-jigan da ake gani a cikin wannan sabuwar tafiya ta hadakar jam’iyyar sun hada da:

Jagoran adawa a kasar, wanda a baya ya sha yin takarar shugabancin kasa, sannan kuma ko a shekarar 2023 shi ne ya zo na biyu bayan da ya samu kuri’a kusan miliyan bakwai.

Alhaji Atiku Abubakar, wanda a yanzu dan jam’iyyar PDP ne; ya kasance guda kuma jigo a siyasar Nijeriya, tun lokacin da ya zama mataimakin shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a shekarar 1999 zuwa 2007.

Tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda ya fito daga Jihar Adamawa da ke Arewa maso gabashin Nijeriya, Bafulatani ne da ake yi wa kallon daya daga cikin masu matukar tasiri a fagen siyasar Nijeriya.

Atiku, na daga cikin fitattun mutanen da suka kulla wannan hadaka da ta haifar da jam’iyyar APC a shekarar 2014, da ta yi nasarar kwace mulki daga hannun jam’iyyar PDP a 2015.

A halin da ake ciki yanzu dai, jam’iyyar PDP na da gwamnoni kimanin 10 a fadin wannan kasa, koda-yake dai kuma, har yanzu babu gwamnan da ya bayyana amincewa da bin Atikun zuwa sabuwar jam’iyyar hadakar, duk da dai ana ganin watakila ficewar tasa za ta sa wasu daga cikin gwamnonin ficewa su su bi shi.

Haka zalika, tsohon dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar LP, na daya daga cikin mutane na gaba-gaba a kafa wannan sabuwar tafiyar ta jam’iyyar ADA.

Peter Obi , wanda tsohon Gwamnan Jihar Anambra ne, ya kasance na uku a zaben shugaban kasar da ta gabata a 2023, inda ya samu kuri’a fiye da miliyan shida.

Obi, dan asalin kabilar Igbo ne daga Kudu maso gabashin wannan kasa, wanda da ya samu farin jini yadda ya kamata, musamman a tsakanin ‘yan kabilarsa.

Wannan dalili ne ma yasa ake ganin jam’iyyar tasa ta LP ta samu nasara a jihohin kasar nan 12, ciki har da Jihar Legas da Abuja a zaben shugaban kasar na 2023.

Kazalika, jam’iyyarsa ta LP na da gwamnan guda daya a Jihar Abia, sannan kuma ana ganin watakila ya bi shi cikin wannan sabuwar hadaka da ake shirin yi.

Har wa yau, a watan Maris da ya gabata ne Malam Nasiru el-Rufai ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC tare da kuma da komawa jam’iyyar SDP.

Tsohon gwamnan, ya kasance Ministan Abuja a tsakanin shekara ta 2003 zuwa 2007, kafin ya zama gwamnan Jihar Kaduna da ke Arewa maso yammacin kasar, na tsawon wa’adi biyu, wato tsakanin 2015 zuwa 2023.

Fitaccen ɗan siyasar, a kakar zaben 2023; wanda Bahaushe ne dan asalin garin Zaria, ya kasance na gaba-gaba wajen goyon bayan Bola Ahmed Tinubu na APC.

Sai dai kuma, bayan lashe zaben na Tinubu; sai kuma baraka ta kunno kai a tsakaninsa da Nasiru, bayan da majalisar dattawa ta ki amincewa da tantance shi, domin ba shi mukamin minista a gwamnatin ta Tinubu.

Rotimi Amaechi, shi ma guda ne cikin tsofaffin hannu a bangaren siyasar wannan kasa, domin kuwa ya kasance tsohon Gwamnan Jihar Ribas mai arzikin mai fetur da ke yankin Kudu maso kudancin wannan kasa daga 2007 zuwa 2015.

Haka nan, bayan kammala wa’adinsa a matsayin Gwamnan Jihar Ribas din, tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya nada shi ministan sufuri na tsawon shekara takwas daga 2015 zuwa 2023.

Har ila yau, A shekarar 2022 ya bayyana anisarya ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023, to amma kuma sai ya sha kaye a hannun Tinubu a zaben fitar da gwani.

A wata hira da ya yi da BBC a baya-bayan nan, tsohon ministan ya ce; a shirye yake domin shiga duk wata hadakar da za ta kawar da gwamnatin Tinubu a halin yanzu.

A gefe guda kuma, Rauf Aregbesola ya taba rike mukamin Gwamnan Jihar Osun da ke Kudu maso yammacin Nijeriya, har na tsawon wa’adi biyu daga 2010 zuwa 2018.

A shekarar 2019, tsohon shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya nada shi, mukamin ministan harkokin cikin gida, mukamin da ya rike har 2023.

Aregbesola Bayerabe ne da ya fito daga yankin Kudu maso yammacin Nijeriya.

A farkon shekarar nan ne, Rauf Aregbesola ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar ta APC.

Tsohon jami’in soji, wanda ya taba zama Gwamnan Mulkin Soji na Jihar Neja daga 1984 zuwa 1986, Dabid Mark; dan asalin Jihar Benuwai ne.

Kazalika, ya rike mukamin ministan sadarwa; kafin ya zama dan majalisar dattawa mai wakiltar Benuwai ta Kudu a cikin jihar ta Benuwai.

Har ila yau, shi ne Shugaban Majalisar Dattawa mafi jimawa a mukamin, bayan jagorantar majalisar na tsawon wa’adi biyu, wato shekara takwas daga 2007 zuwa 2015.

Sannan, ya kasance dan asalin kabilar Idoma daga yankin Arewa ta tsakiyar Nijeriya, shi ma yana cikin wannan hadakar jam’iyyar adawa, dumu-dumu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: shugaban kasar gwamnan Jihar Gwamnan Jihar wannan kasa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran

Daga Bello Wakili 

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi.

’Yan ta’addan sun kai hari makarantar  ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar.

Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja.

An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu.

Shugaba Tinubu ya yaba wa jami’an tsaro bisa ƙoƙarin da suka yi wajen ganin an kubutar da dukkan mutanen da ’yan ta’adda suka sace.

Ya umarci jami’an tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa don ceto sauran ɗaliban da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.

“Ina farin cikin cewa an samu dukkan ’yan mata 24. Ya zama wajibi mu ƙara tura jami’an tsaro  yankunan da ke da rauni don hana sake faruwar irin wannan lamari. Gwamnatina za ta bayar da dukkan tallafin da ake buƙata don cimma haka,” in ji Shugaba Tinubu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC
  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’ani
  • Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • Tinubu Ya Nuna Farin Cikinsa Bisa Bayyanar Daliban Kebbi, Ya Bukaci a Ceto Sauran
  • An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia
  • Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja