2025-07-26@01:11:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3547
«yan kwangila»:
Duk da cewa yanayin duniya ya yi babban sauyi, kamata ya yi a mayar da hankali ga hadin gwiwa, yayin da ake raya dangantaka tsakanin Sin da EU, kana bangarorin biyu su bi hanya mafi dacewa, da samun kyakkyawar makoma a shekaru 50 masu zuwa, da kuma kara samar da gudummawa ga dukkanin sassan duniya....
Mai magana da yawun jam’iyyar na wucin gadi ya ki janye ikirarinsa na cewa ADC na fuskantar manyan matsaloli a bangaren shari’a. “Muna da tabbaci kan doka a kowane mataki da muka dauka. Mun tabbatar mun rufe duk wata baraka da jam’iyya mai mulki za ta iya amfani da ita a kanmu,” ya kara da...
Ficewar Amurka daga yarjejeniyoyin kasa da kasa da hukumomin duniya ba sabon labari ba ne, don haka mene ne abun mamaki idan ta bar UNESCO a karo na uku? Wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN ta gudanar ya nuna cewa kashi 84.2 cikin dari na wadanda suka bayyana rayoyinsu ba su yi mamakin wannan...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara aikin gina shaguna guda dubu daya a cibiyar kasuwanci ta Farm Centre da ke Kano, wanda zai lakume kudi Naira Biliyan Uku da rabi (N3.5bn), domin bunkasa kudaden shiga na cikin gida na jihar. Shugaban Kungiyar Hadaka kan Tsaro, Zaman Lafiya da Warware Rikice-rikice a Jihar Jigawa, Muhammad Musbahu...
Tsofaffin shugabannin da suka rasu bayan kammala wa’adinsu Nnamdi Azikiwe An haife shi a ranar 16 ga Nuwamba, 1904, Dakta Nnamdi Azikiwe, wanda aka fi sani da “Zik of Africa,” fitaccen dan siyasar Nijeriya ne kuma mai kishin kasa wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen samun ‘yancin kai. Ya zama shugaban kasa na farko...
Kotun Tarayya da ke zamanta a Jihar Kano, ta bayar ta yanke wa fitaccen ɗan Tiktok, Al-Ameen G-Fresh da mawaƙi Hamisu Breaker, hukuncin ɗaurin wata biyar a gidan yari bayan samun su da laifin wulaƙanta takardun Naira. Mai shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukunci, inda ya yi musu ɗaurin wata biyar a gidan yari,...
JMI ta cilla taurarun dan’adam masu suna Nahid-2 kirar cikin gida zuwa sararin samaniya tare da nasara. Kuma ta yi amfani da kombo na kasar Rasha mai suna Vostochiny Cosmodrome don isar da tauraron zawa inda take so a sararin samaniya, a yau Jumma’a 25 ga watan Yulin shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv...
An takaita taro tsakanin kasashen turai da China a birnin Beijin zuwa ranar Alhamis kadai bayan da bangarorin biyu sun sami sabani a tsakaninsu kan al-amuran kasuwanci. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa an shirya gudanar da taron har na tsawon kwanaki uku amma kwotsom sai kasar China ta bukaci a...
Dakarun Runduna ta 3 ta ‘Operation Safe Haven’ masu wanzar da zaman lafiya a Jihar Filato sun ceto wani yaro ɗan shekara 12 a Ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Manjo Samson Zhakom ne ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Juma’a....
Babbar Kotun Jiha a Gombe mai lamba ta 3 ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu mutum uku bisa laifin haɗa baki da kuma kisan kai. Alƙalin kotun Mai shari’a Haruna Kereng ne ya jagoranci shari’ar, inda ya ce kotu ta sami Dauda Mohammed Abubakar (wanda aka fi sani da Agenda) da Kabiru...
Kwamitin ya nemi a mayar da sama da Naira miliyan 124, kusan dala 795,000 zuwa asusun gwamnatin tarayya, an kuma bayar da karin wasu kudade da suka hada da Naira miliyan 31.7 da dala 155,923.00, a matsayin wadanda aka kashe ba bisa ka’ida ba. An umarci ma’aikatar da ta kwato Naira miliyan 49.4 da aka...
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a 2023, ya karɓi ’yan APC zuwa jam’iyyar NNPP a Jihar Kano. Kwankwaso, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta shafinsa na X, inda ya ce waɗanda suka sauya sheƙar ’yan jam’iyyar APC ne. An kai hari a ƙauyuka uku da kashe mutum 7...
A ranar Juma’a wasu ’yan bindiga sun kai hari wasu ƙauyuka uku na Umualoma da Ndiakunwanta da Ndiejezie a garin Arondizogu, a Ƙaramar hukumar Ideato ta Arewa a Jihar Imo, inda suka kashe aƙalla mutane bakwai. An samu rahoton cewa, ’yan bindigar sun kai harin ne a kan babura sun yi ta harbin mutanen yankin...
Sai dai Sanatoci sun yi watsi da bayanin, inda suka zargi Ojulari da yin watsi da Majalisar. Kwamitin yana binciken tambayoyin tantancewa daga shekarar 2017 zuwa 2023, wanda ya nuna sabanin da ya kai Naira tiriliyan 210, ciki har da bashin da ba a tabbatar da shi ba na Naira tiriliyan 103. ‘Yan majalisar sun...
Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato. Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos. Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano...
Koda ya ke dai, a lokacin ‘yansanda sun yi nisa ban gudanar bincike, amma babu wanda suka iya kamawa, kuma ba a kara shigar da wata sabuwar kara a gaban kotu ba, duk tsawon wadannan shekarun. Wannan bukatar da Muyiwa ya biro da ita, tamkar bude wani sabon babi ne, kan batun hallaka manyan mutane...
“Sauran su ne Lawan Haruna, Opurum Patrick, Agbo James da Georgewill Onwubiko da sauransu. “Shugaban PSC ya ce su tuna cewa su abokai ne ga kowa, kuma ya kamata a kowane lokaci su yi daidai da abin da ‘yan Nijeriya ke bukata. Ya kuma ba su tabbacin cewa hukumar za ta ci gaba da yin...
Ya ce tituna a Arewa sun lalace kuma gwamnati tana nuna rashin kulawa ga yankin. “Jiya da jirgi zan biyo na taho, amma aka ɗage jirgi daga ƙarfe 3 na yamma zuwa 8 na dare, sai na taho ta mota. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano abin takaici ne. Wannan aikin titi tun lokacin farkon...
Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta jaddada cewa: Dole ne kasashen duniya su dauki matakin dakatar da kisan kare dangi a Gaza Mataimakin shugaban kasar Iran na farko Muhammad Reza Aref ya jaddada cewa: Dole ne a kawo karshen kisan gillar da yahudawan sahayoniyya suke yi a yankin Zirin Gaza cikin gaggawa ta hanyar daukar matakai...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa: Babu shakka Iran za ta ci gaba da inganta sinadarn Uranium Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana a jiya Alhamis dangane da tattaunawar da Iran za ta yi da kungiyar kasashen Turai da za a yi a yau Juma’a a birnin Istanbul na Turkiyya...
Ya ce, nan da shekarar 2030 za a bukaci hekta miliyan 300 domin samar da bukatar abinci. Don haka ne ya ce taken taron ranar yaki da kwararowar hamada na 2025 na da matukar tasiri domin tabbatar da daukan matakan da suka dace wajen kiyaye hamada da gurbacewar muhalli. A cewarsa, yunkurin zai tunkari manyan...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan hadin kai da karfafa fahimtar juna wadanda hidimar kasa take kawowa, akan samu wasu masu hidimar da sukan yi amfani da duk wata dama da suka samu don neman na sakawa a bakin salati. Yayin da wasu masu hidimar kasa sukan kama sana’a ko su saka hannun...
Kashe- Kashen 2025 Ya Fi Na 2024 Alkaluman bincike sun bayyana cewar ‘yan ta’adda sun dauki rayukan mutane a rabin wannan shekarar fiye da na shekarar 2024 da ta gabata kamar yadda Hukumar Kula da ‘Yancin Dan- Adam ta kasa ta bayyana a wannan watan. Kamar yadda alkaluman suka nuna, akalla mutane 2, 266...
Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya fada a wannan alhamis cewa yana shirin aikewa da tawaga zuwa kasar Senegal a cikin watan Augusta domin tattauna yadda aza magance matsalar basussukan da ke kan kasar da kuma fara tattaunawa kan tsarin sabon shirin lamuni. Kasar Senegal na fama da bashin biliyoyin daloli da gwamnatin...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bayyana cewa yana yawan karanta rantsuwar kama aiki da ya yi domin tunatar da kansa nauyin da ya dauka na yi wa al’umma hidima bisa gaskiya da amana. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Hamisu Mohammed Gumel, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar...
Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Tinubu da mayar da yankin Arewacin Nijeriya saniyar ware, yana mai cewa shugaban ya fi mayar da hankali wajen gina kudancin ƙasar ta hanyar amfani da albarkatun ƙasar. Kwankwaso ya bayyana haka ne yau Alhamis a wajen taron bana kan shawarwari na masu ruwa...
Gwamnatin Jihar Yobe ta raba tallafin kuɗi ga iyalan ’yan banga da suka rasa rayukansu da kuma waɗanda suka samu raunuka a bakin aiki. Kuɗaɗen wanda Daraktan ayyuka na musamman, Muhammad Alhaji Baba ya miƙa a madadin sakataren gwamnatin jihar sakamakon umarnin da Gwamna Mai Mala Buni ya bayar na a yi hakan. Hulk Hogan ya...
Kafafen watsa labarun HKI sun ce wani mutum a cikin motar da yake tukawa ya nufi kan ‘yan sahayoniya a mahadar “Hahsrun” a kusa da “Kafar-Yona”dake yammacin Tul-Karam. Bayan da matumin ya take ‘yan sahayoniyar ya fice daga yankin ba tare an iya tsayar da shi ba. Majiyar ta kara da cewa; 9 daga cikin...
Ministan Noma na Iran Gulam Riza Nuri Qazlajeh ya fada a yau Alhamis cewa; Iran tana a cikin kasahe biyar na sahun gaba da su ka yi fice wajen dabbobi. Minstan wanda yake jawabi a wani kamfani na samar da nono, ya ce, Iran tana da niyyar kara yawan dabbobin da suke samar da nono...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Majiyar asibitocin yankin Gaza ta tabbatar da cewa, Falasdinawa 115 sun yi shahada sanadiyyar yunwa saboda karewar abinci a cikin yankin. Ita kuwa hukumar Agajin MDD dake aiki a Falasdinu “Unrwa” ta sanar da cewa tana da dubban manyan motoci da suke cike da kayan abinci suna jiran a ba su umaranin shiga Gaza.” Motocin...
Shahararren ɗan kokawa ɗan ƙasar Amurka mai ritaya Terry Gene Bollea wanda aka fi sani da Hulk Hogan ya rasu yana da shekara 71 a duniya. A cewar TMZ da sauran rahotanni, likitoci sun mayar da martani a gidansa na Clearwater, da ke Florida da sanyin safiyar Alhamis kan Hulk Hogan ya kamu da bugun...

Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
Kwanan nan, darektar zartaswa ta hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD, Anacláudia Rossbach, ta yi hira da wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG, a hedkwatar hukumar kula da matsugunan dan Adam ta MDD dake Nairobi, babban birnin Kenya. Yayin da aka ambato sakamakon da ya fi jawo hankali...
A cewar ministan, shi da sauran abokan aikin sa, Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Ali Pate, da Ministan Kuɗi, Mista Wale Edun, sun halarci bikin ƙaddamar da ɗaya daga cikin manyan ayyukan, wanda ya gudana a Jihar Katsina. Cibiyoyin da aka ƙaddamar na cikin zagaye na farko na shirin gina sababbin cibiyoyin maganin ciwon daji...
Aikin gina tsibirin ciniki maras shinge na Hainan na kasar Sin ya samu gagarumin ci gaba sosai, inda gwamnatin kasar Sin ta sanar a jiya cewa, a ranar 18 ga watan Disamban bana, za a kaddamar da manufar kafa “kwastam mai zaman kansa a duk faɗin tsibirin ciniki maras shinge na Hainan” a hukumance, wadda...
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa...
An samu ɓarkewar cutar amai da gudawa wato kwalara a ƙananan hukumomi shida na Jihar Neja, inda rahotanni suka ce mutum 13 ne suka mutu tare da wasu mutane sama da 236 da ke jinya a asibiti. An fara samun ɓullar cutar ne a Ƙaramar hukumar Shiroro tun a ranar Lahadin da ta gabata zuwa...
An cimma matsaya kan zaɓensa bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Shugaba Bola Tinubu da gwamnonin APC. Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar za su tabbatar da naɗinsa a yau Alhamis. Farfesa Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato da ke yankin Arewa ta Tsakiya, yankin da suke da alhakin riƙe kujerar...
Wani jrigin saman fasinjoji mallakin kasar Rasha da ke dauke da mutum 50 ya yi hatsari a kusa da yankin Amur na kan iyakar kasar China. Kafar yada labarai ta Sky News ta rawaito cewa jirgin wanda ke dauke da fasinjoji, ciki har da kananan yara biyar da kuma ma’aikatan jirgi su shida, ya fadi...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi...
Ruwan sama kamar da bakin kwarya hade da iska sun yi ajalin mutum biyar sannan wasu 92 suka samu munanan raunuka a kananan hukumomi bakwai na jihar Yobe. Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) Dr Goje ne ya tabbatar da hakan a ranar Laraba a Damaturu. Ya ce iftila’in ya shafi al’ummomi...
Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin...

Asusun Kula Da Kananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya “UNICEF” Ya Yi Gargadi Kan Bala’in Jin Kai A Gaza
Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi karuwar bala’i na jin kai a Gaza Kazem Abu Khalaf, kakakin hukumar UNICEF a Falasdinu, ya tabbatar da cewa: Abin da ke faruwa a Gaza ba a taba ganin irinsa ba, yana mai cewa har yanzu yana ci gaba da tuntubar wasu ma’aikatan...

Ministan Lafiya Na Kamaru: Hadin-Gwiwa Ta Fuskar Kiwon Lafiya Ta Shaida Zumunci Mai Karfi Tsakanin Kamaru Da Sin
Ministan lafiya na kasar Kamaru, Manaouda Malachie ya bayyana jiya Talata 22 ga wata a Yaounde cewa, hadin-gwiwar Kamaru da Sin a bangaren kiwon lafiya ta haifar da babban alfanu ga jama’ar Kamaru, kana alama ce dake shaida dangantakar kut da kut gami da dadadden zumunci tsakanin jama’ar kasashen biyu. A wajen bikin cika shekaru...
Wani mummunan al’amari ya faru a Ƙaramar Hukumar Fika da ke Jihar Yobe, inda wata mata mai shekara 35, ta kashe mijinta da itace bayan rikici ya ɓarke a tsakaninsu a kan abinci. Rahotanni sun nuna cewa matar wacce ’yar garin Abba ce, ta ɗauki katon itacen girki ta rafka wa mijinta bayan rikici ya...

Gwamantin Kasar Siriya Ta Rufe Hanyoyin Shiga BirninSiweida Na Kasar Saboda Ci Gaba Da Bullar Rikici
Hukumomin rikon kwaryar Siriya sun rufe hanyoyin zuwa birnin Sweida bayan sake bullar wani tashin hankali Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da rufe hanyoyin da ke shiga lardin Sweida da ke kudancin kasar tun daga wayewar garin ranar Asabar, bayan kazamin fadan da aka gwabza tsakanin kabilar Bedouin da mayakan Duruz a cikin birnin....
Dakarun Sojin Najeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Ƙananan Hukumomin Rijau da Mariga a Jihar Neja. ’Yan ta’addan sun fito ne daga Jihar Zamfara, yayin da suke tafiya a kan babura ɗauke da muggan makamai. Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan kisan mutum sama da 100 Nentawe Yilwatda ne zai zama sabon shugaban APC na...
Tawagar kwararru daga hukumar makamashin Nukliya IAEA zata ziyarci kasar Iran nan ba da daewa ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Gharibabadi mataimakin ministan harkokin wajen kasar a bangaren sharia da kuma harkokin kasashen waje ne ya bayyana haka. Ya kuma kara da cewa tawagar zata tattauna da Jami’an gwamnatin...
Dakarun Sojin Operation Hadin Kai, sun daƙile hare-haren Boko Haram a garuruwan Monguno da Bitta da ke Jihar Borno, tare da wani kashe babban Kwamandan Boko Haram mai suna Ibn Khalid. Sun kuma kashe ’yan ta’adda da dama, ciki har da wani babban kwamandan ƙungiyar. NAJERIYA A YAU: Cututtukan da rumar daki ke haifarwa ga...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa Majalisar Dokokin Tarayya buƙatar ƙara ranto bashin Dala miliyan 347 daga ƙetare, ƙarƙashin shirin ciyo bashin na gwamnatin tarayyar na 2025 zuwa 2026. Hakan na ƙunshe cikin wata takarda da Tinubu ya aikewa majalisar, wadda Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya karanto a zamansu na yau Laraba. Dalilin...