Amurka ta dakatar da bai wa Ukraine tallafin makamai
Published: 3rd, July 2025 GMT
Amurka ta dakatar da tallafin makaman da take bai wa Ukraine, tana mai bayyana damuwa kan raguwar makamanta a rumbun adana su.
Mai magana da yawun Fadar Gwamnatin Amurka, Anna Kelly a watan sanarwar da ta fitar, ta ce a halin yanzu muradun Amurka ne kan gaba ta bangaren tsaro, don haka dole ne ta dakatar da duk wani tallafin makamai da take bai wa Ukraine din.
Wannan na zuwa ne daidai lokacin da Rasha ke ci gaba da fadada hare-harenta a kan kasar, yayin da aka kwashe sama da shekaru biyu ana gwabza yaki tsakanin kasashen da ke makwabtaka da juna.
Rahotanni na cewa, Ukraine za ta shiga tsaka mai wuya, musamman yadda za ta ci gaba da fuskantar Rasha ba tare da irin makaman Amurka ba, yayin da Shugaba Vladimir Putin, ya shawarci Ukraine din da ta mika wuya.
Tuni aka shiga damuwa a wannan kasa da ke gabashin Turai, inda gwamnatin kasar ke ganin daga lokacin da aka fara samun tsaikon tallafin Amurka, Rasha za ta kara samun kwarin gwiwar kai farmaki babu kakkautawa.
A halin da ake ciki Ukraine ta shiga tsaka mai wuya, domin baya ga katse tallafin makamai, matakin da shugaba Trump ya dauka na dakatar da ayyukan Hukumar Raya Ƙasashe ta Amurka, ya shafi ayyukan jin kai a wannan kasa, sakamakon cewa tana cikin kasashen da suke karbar tallafin USAID sosai.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Rasha Ta Jaddada Aniyarta Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Jamhuriyar Musulunci Ta Iran
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya bayyana cewa: Kasarsa na da niyyar karfafa hadin gwiwa da Iran da kuma kara karfin tsaron kasar ta Iran
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergei Riyabkov ya jaddada cewa: Kasar Rasha za ta karfafa hadin gwiwa da Iran a dukkan fannoni, gami da kara karfin tsaron kasar ta Iran.
Riyabkov ya shaidawa manema labarai a ofishin jakadancin Iran da ke birnin Moscow cewa: “Za su karfafa hadin gwiwa a aikace tare da Jamhuriyar Musulunci ta Iran a dukkan fannoni, yana mai jaddada cewa: Dole ne a karfafa karfin tsaron kasar Iran, saboda Rasha tana da gogewa mai kima a wannan fanni, kuma za ta ci gaba a kan hakan.”
A ofishin jakadancin Iran, Riyabkov ya kuma sanya hannu a littafin ta’aziyya ga shahidan Iran da aka kashe a harin wuce gona da iri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.
Wani abin lura a nan shi ne cewa: A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne yahudawan sahayoniyya suka ci gaba da kai hare-hare kan yankunan birnin Tehran da wasu garuruwa da dama da suka hada da cibiyoyin nukiliya, cibiyoyin kiwon lafiya, asibitoci da kuma wuraren zama a fadin kasar.