Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Bayyana Cewa: Ba Za A Iya Kawar Da Fasahar Nukiliya Da Karfi Ba
Published: 1st, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ba za a iya kawar da fasahar nukiliya ta hanyar harin bam ba
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ya jaddada cewa: Ba za a iya kawar da fasaha da kimiyyar da ake bukata don inganta sinadarin Uranium ta hanyar kai hare-haren bama-bamai ba.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta CBS, Araqchi ya yi tsokaci kan ikirarin shugaban Amurka Donald Trump na cewa ana iya komawa tattaunawa da Iran a cikin wannan mako: Araqchi yana mai mayar da martini da cewa: “Ba ya jin za a dawo da tattaunawar cikin gaggawa.
Ya kara da cewa: “Kafin yanke shawarar komawa kan tattaunawar, dole ne Iran ta fara tabbatar da cewa Amurka ba za ta sake kai wa kasarta harin soji ba yayin tattaunawar.”
Ya ce: Ya yi imani tare da wannan la’akari, cewa har yanzu Iran tana bukatar karin lokaci, amma kofofin diflomasiyya ba za su taba rufewa ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Takht-Ravanchi: Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa kan hakkinta na nukiliya
Wani babban jami’in diflomasiyyar Iran ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Turai da kuma kare hakkinta na nukiliya cikin lumana.
Mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da tashar dillancin labaran Turkiyya, a lokacin da yake amsa tambaya kan tattaunawa da aka shirya yi tsakanin Iran da E3 (Faransa, Birtaniya da Jamus) a nan gaba, yayin da kuma an riga an gudanar da zama zagaye na biyu na masana da kwararru a matsayin sharar fage a birnin Istanbul na kasar Turkiyya a karshen watan Yuli.
“Yanzu, wadannan shawarwari za su ci gaba, mun yanke shawarar ci gaba, kuma za mu yi hakan,” in ji shi.
Sai dai ya jaddada bukatar yin taka-tsan-tsan don tabbatar da cewa babu wanda zai yi amfani da shawarwarin bangarorin biyu a matsayin wata hanya ta cimma burins ana siyasa.
Ya bayyana fatan cewa kasashen Turai uku za su fahimci cewa “idan manufar ita ce cimma yarjejeniya mai ma’ana tsakanin bangarorin biyu, to komai mai yiwuwa ne.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sudan: Al-Burhan ya ce babu sulhu tsakaninsu da dakarun RSF August 16, 2025 Mali: An kama wasu Manyan Sojoji da Wani Bafaranshe bisa zargin yunkurin juyin mulki August 16, 2025 Wata Kotu a Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci August 16, 2025 Hizbullah Ta Ce Ba Zata Ajiye Makamanta Ba August 15, 2025 China Tace Bata Goyon Bayan A Sake Dorawa Iran Takunkuman MDD August 15, 2025 An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza August 15, 2025 India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar August 15, 2025 Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 HRW; Kai Hari Kan Gidan Yarin Evin Na Iran Laifin Yaki Ne August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci