2025-12-05@22:42:06 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7129

«Zariya»:

    Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya (FIFA), ta kammala fitar da jadawalin Rukunin Gasar Kofin Duniya ta 2026. Za a gudanar da gasar ne a Amurka, Kanada da Mexico daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026. Ina nan a PDP duk da sauya sheƙar ’yan majalisar Ribas — Wike DSS ta...
    Mutanen garin Dadin-Kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu Deba a Jihar Gombe, sun shiga damuwa kan yadda wata Dorinar ruwa ta addabi yankin, ta hanyar kashe mutane da kuma lalata gonaki. Cikin watanni biyu, Dorinar ta kashe mutum biyu, ta karya wasu biyu, sannan ta jikkata wasu huɗu, waɗanda yawanci manoma da masunta ne a...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP. Ya yi wannan bayani ne a Abuja a ranar Juma’a yayin da yake mayar da martani kan ficewar wasu ’yan majalisar dokoki na Jihar Rivers daga PDP zuwa jam’iyyar APC. Na kashe N100bn a kan harkar tsaro a...
    Hukumar Tsaro ta DSS ta kama wani likita da ake zargin yana ba da magunguna tare da kula da ’yan bindiga masu garkuwa da mutane da ke wasu sassan jihar Kwara. An kama wanda ake zargin, wanda ba a iya gano sunansa ba a lokacin rahoton, a yankin Jebba bayan rahotannin sirri sun nuna cewa...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baghaei ya yi tir da takunkuman tattalin arzikin da kasar Amurka take ci gaba da dorawa JMI na shekaru masu yawa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta  bada nakalto Baghaei yana fadar haka a dai dai ranar tunawa da ranar haramcin takunkuman tattalin arziki na bangare...
    Shugaba Bola Ahmad tinubu na tarayyar Najeriya ya nada wasu karin jakadu 65 wadanda suka hada da sanatoci masu ci da kuma tsoffin gwamnoni har’ila yau da kwararrun jakadu. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa shugaban ya aikawa majalisar dokokin kasar wasika dangane da hakan, wasika wacce shugaba majalisar dattawa Godswill Akpabio ya...
    Pars Today – Vladimir Putin ya yi tafiya zuwa Indiya don ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu. Vladimir Putin, shugaban Rasha, ya isa New Delhi a ranar Alhamis, 4 ga Disamba, a ziyararsa ta farko zuwa Indiya tun bayan fara yakin Ukraine a 2022. Ziyarar ta kwanaki biyu na da nufin zurfafa haɗin gwiwa tsakanin tsaro da...
    Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasa ransa bayan fada ya barke a lokacin bikin radin suna a ƙauyen Kwata da ke Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi. Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a ranar Talata lokacin da sa’insa ta barke tsakanin wasu matasa ta rikide ta zama fada, wanda ya...
    Rundunar ’yan sandan jihar Borno ta kama matashin nan da ake zargi da kashe makwabciyarsa a unguwar Shuwari II, a garin Maiduguri babban birnin jihar, ta hanyar daba mata wuka. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na dare a ranar Talata. Amurka...
    Ƙasar Amurka ta yi barazanar sanya takunkumin izinin shiga kasarta ga ’yan Najeriyar da aka gano suna ɗaukar nauyi ko goyon bayan ayyukan da ke take ’yancin yin addini da yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana haka a cikin wani saƙo da ya wallafa a shafin X, inda...
    Babban taron Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wasu kudurori guda biyu da ke kira da a kawo karshen mamayar Isra’ila a Falasdinu da kuma Tuddan Golan na Siriya. Djibouti, Jordan, Mauritania, Qatar, Senegal, da Falasdinu ne suka gabatar da daftarin kuduri game da Falasdinu. Kasashe 151 ne suka kada kuri’a a kan hakan, yayin...
    Dan wasan taekwando na kasar iran  Abolfazl zandi ya samu lambar yazo ta zinariya a ranar farko ta gasar takwando ta duniya  da ake gudanarwa a birnin Nairobi na kasar kenya , kuma ita ce lambar yabonsa na biyu a cikin kwanaki 35, Gasar tana gudana ne a filin wasa na moi international sport center...
    Jirgin Fadar Shugaban Kasa da Gwamnatin Najeriya ta saka a kasuwa da nufin sayarwa ya kasa samun mai saye kusan watanni biyar bayan ɗora shi a dandalin sayar da jiragen sama na duniya. A sakamakon haka, tuni ma kamfanin dillancin da ke kula da sayar da jirgin samfurin Boeing 737-700 Business Jet ya janye jerin...
    Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Najeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin...
    Gwamnonin Arewaci, na shirin dakatar da haƙar ma’adinai a wasu yankuna da ake fama da matsalar tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ta’addanci. Wannan batu ya fito ne daga taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna daga 1 zuwa 2 ga watan Disamba, 2025....
    Tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya san dalilin da ya sa ya yi murabus. Badaru, ya ajiye aiki ne a ranar Litinin, inda ya ce matsar rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus. Ƙudirin dokar hukuncin kisa ga masu satar mutane ya tsallake karatu na biyu Tsaro: Gwamnatin Kano...
    Majalisar Dattawa ta amince da wani sabon ƙudiri da ke neman a gyara dokar yaƙi da ta’addanci, domin a ɗauki garkuwa da mutane a matsayin babban laifi na ta’addanci. Ƙudirin, wanda Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar, ya tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin satar mutane, ba tare da wata zaɓin tara...
    Hukuma ko kungiyar ‘The Guinness World Records organization’ ta bada sanarwan cewa daga yanzu ta daina karban duk wata bajinta ko wani al-amiri da ya shafeta daga HKI saboda ta’asan da take aikatawa a Gaza, wanda kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama a duniya sun tabbatar da cewa, kissan kare dangine. Kamfanin dillancin labaran IP na...
    Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan  sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya. Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja. Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu,...
    Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnatinsa na shirin sayen jirage marasa matuƙa da wasu kayan aiki domin kare yankunan da ke iyakar Kano da Katsina. Kakakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne, ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Gobara ta ƙone kasuwar katako a Abuja CBN ya...
    Gwamnatin Amurka ta sanar da soke bada mafaka ga wasu kasashen duniya 19 wadanda suka hada da na Afrika guda 10. Wannan matakin, ya zo ne bayan harin da aka kai a Washington kwanan nan, kuma ya shafi  kasashe 19, da suka hada da Chadi, Congo, Equatorial Guinea, Eritrea, Libya, Somalia, Sudan, Burundi, Saliyo da...
    Hukumar bada agaji da samar da ayyukan ga falasdinawa na majalisar dinkin duniya UNRWA ta fadi cewa isra’ila ta hana motoci makare da kayan agaji guda 6000 shiga yankin Gaza da suke dauke  da abinci magunguna da za su iya wadatar da yankin na tsawon watanni 3. Kakakin kungiyar ta UNRWA Adnan Abu Hasna ya...
    Wani ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu ya je karvar kuxin fanshonta Ana binciken wani tsohon ma’aikacin jinya a qasar Italiya bisa zargin ya yi shigar mahaifiyarsa da ta mutu kuma ya je ma’aikatar fansho a matsayin mahaifiyarsa don neman fanshonta. Haka kuma an gano ya voye gawarta a cikin gidansa har tsawon shekaru...
    Har yanzu ban bar yin waqa ba-Yusuf Lazio Daga Musa Kutama, Kalaba Yusuf Muhammad Abdullahi da aka fi sani da Yusuf Lazio, fitaccen jarumi ne a Masana’antar Finafinan Hausa, wato Kannywood. Jarumin ya yi shura a fim xin Na-Ladidi, inda ya ce, haxa waqa da fim a lokaci xaya, a wurinsa ba wani abu ba...
    Majalisar Dattawan Najeriya za ta tantance wanda Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, a zamanta na yau Laraba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga ofishin Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Opeyemi Bamidele. Mako mai Majalisa za ta kada ƙuri’a kan ƙudurin ƙirƙirar sabbin jihohi...
    Majalisar Wakilai za ta ƙada kuri’a a ranakun 10 da 11 ga watan Disamba kan muhimman kudurorin gyaran kundin tsarin mulkin 1999, ciki har da kirkirar sabbin jihohi da kafa ’yan sandan jihohi. Mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Okezie Kalu, ya sanar da jadawalin a zaman majalisar, inda ya ce tattaunawa kan kudirin sauya kundin tsarin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ana sa ran Majalisar Dattawa za ta tantance tare da tabbatar da Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin Ministan Tsaro, bayan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunansa zuwa majalisar.   Wannan naɗin ya zo ne a wani lokaci da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen...
    Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya  Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. An yi garkuwa da manoma 11 a Kudancin Kaduna Mutane 9,854 na ɗauke da cutar AIDS a Yobe  Sanarwar...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya          hana abokan gaba cimma mummunar manufarsu akan kasar. Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama ranar “Mutane Masu Bukata Ta Musamman” ta duniya ya bayyana cewa a yayin...
    A yau Talata ne mai bai wa shugaban kasar ta Nigeria, shawara akan watsa labaru Bayo Onanuaga ya sanar da Nadin na Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin wanda zai maye gurbin Alhaji Muhammad Badru Abubakar da ya yi murabus a jiya Litinin. Janar Musa ya rike mukamai masu yawa na soja gabanin Nadin nasa...
    Ma’aikatar harkokin wajen Njgeria ta sanar da bai wa dan takarar shugabanncin  kasar Guinea Bissau, Fernando Dias da Costa, ya kuma tsaya takara ne a tare da shugaban kasar  Umar Sisoko  Embalo da sojoji su ka kifar da gwamnatinsa kwanaki kadan bayan zabe. A ranar 27 ga watan Nuwamba ne dai Dias Da Costa ya...
    Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon babban hafsan tsaron, Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya  Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Talata. Sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio wasiƙar sanar da shi sabon...
    Fargaba ta lulluɓe al’ummar Ungwan Nungu da ke gundumar Bokana a Ƙaramar Hukumar Sanga ta Jihar Kaduna, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da mazauna yankin 11 a ranar Asabar yayin da suke dawowa daga gonakinsu. Mazauna yankin sun ce an tare mutanen ne a wata hanyar daji da ke kusa da unguwar da...
    Rahotanni da suka fito daga Najeriya sun nuna cewa ministan tsaro Alh mohammadu Badaru Abubakar a ranar 1 ga watan Decemba ya mika takardar ajiye aiki a matsayinsa na ministan tsaron kasa, saboda wasu dalilai da suka shafi lafiyarsa, Kamar yadda kakakin shugaban kasa Bayo Onanuga ya bayyana cewa shugaba tinubu ya amince da takardar...
    Ministan harkokin wajen kasar iran Abbas Araqchi  ya fadi cewa iran tana ci gaba da aiki da diplomasiya duk da cikas da Amurka take kawo  wa a tattaunawar da ba ta kai tsaye ba, ganin cewa Amurka tana amfani da karfi wajen gudanar da harkokin duniya . Yace idan bangaren Amurka ta nuna shirinta na...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar kansar mama na ɗaya daga cikin manyan cututtukan da ke addabar mata a Najeriya da ma duniya baki ɗaya.   An kiyasta cewa mata sama da dubu ɗari biyu na kamuwa da cutar a kowace shekara a Najeriya, yayin da miliyoyin mata a duniya ke fama da...
    Wakilan kasashen Afirka da suka hallara a birnin Algiers sun sabunta wani yunkuri don amincewa da laifukan ‘yan  mulkin mallaka a hukumance, tare da ayyana mulkin mallaka a matsayin laifi kan bil’adama, da kuma tabbatar da an biya diyya bisa ga barna da cin zarafi da aka yi wa al’ummomin Afirka. Taron, wanda aka gudanar...
    An kashe wani ɗan sanda a wani mummunan hari da ’yan bindiga suka kai gidan Babban Jami’in Ɗan Sanda (DPO) mai kula Babba Ofishin ’Yan Sanda da ke Aujara a Ƙaramar Hukumar Jahun ta a Jihar Jigawa.   Da misalin ƙarfe 4:00 na asuba, ranar 25 ga Nuwamba, 2025, ne wasu ’yan bindiga suka kai farmaki...
    Matatar Man Fetur ta Dangote a Najeriya ta sanar a wannan  Litinin cewa tana da ikon isar da lita biliyan 1.5 na man fetur a kowane wata, kuma ta yi kira ga hukumar kula da masana’antu da ta tabbatar da hakan a cikin alkalumanta na yau da kullun, bayan da hukumar ta fitar da bayanai...
    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa  ya yi watsi da barazanar Shugaban Amurka Donald Trump na cire Pretoria daga taron G20 na shekara mai zuwa, yana mai sake tabbatar da matsayin Afirka ta Kudu na memba da aka kafa wannan dandali na kasa da kasa tare da ita. Trump ya sanar a ranar Laraba da...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri da tsohon Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa a Fadar Shugaban Kasa. Ganawar Tinubu da Janar CG Musa ya auku ne a ranar Litinin da dare, jim kadan kafin sanarwar murabus din Ministan Tsaro, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar. Majiyoyi na cewa gananawar shugaban kasa...
    Daga Shamsuddeen Mannir Atiku  Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta karɓi daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya zarce naira miliyan dubu dari tara da tamanin da biyar daga bangaren zartarwa jihar. Da yake gabatar da kasafin kudin a  zauren majalisar, Gwamna Malam Uba Sani ya bayyana kasafin a matsayin na sauye-sauye da ci-gaba wanda aka...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baqaei ya bayyana cewa Amurka ce Babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, saboda ganin abinda take yi a halin yanzu a kasar Venezuela da kuma wasu kasashen Afirka. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka...
    Anicen Ekane dan adawa na jam’iyyar African Movement for New Independence yana daga cikin fitattun yan  siyasa a kasar Kamaru, kuma yana goyon bayan Issa Chiroma a zaben shugaba kasa wanda aka gudanar a kasar a cikin watan Octoban da ya gabata. Issa Chiroma dai ya shelanta cewa shi ya lashe zaben shugaban kasa wanda...
    Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu. Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna. ’Yan sanda sun gano zinaren N23m...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 13 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren da suka ɓace...
    ’Yan sanda sun gano tare da miƙa wa wata mata zinarenta da kuɗinwu ta kai Naira miliyan 23 da suna ɓace a lokacin wani harin Boko Haram shekara 12 da suka gabata a Jihar Borno. Jami’an tsaro da ke sintiri a kan iyakar Jihar Borno da Nijar ne suka gano kayan zinaren waɗanda suka haɗa...
    Daga Bello Wakili  Najeriya ta ƙarfafa ƙoƙarinta na kawar da cutar HIV nan da shekarar 2030, inda Uwargidar Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira ga ’yan Najeriya, shugabanni da jami’an lafiya su haɗa hannu wajen cimma wannan manufa. Yayin jawabi a bikin ranar Yaki da Cutar AIDS ta Duniya ta 2025 da aka...
    Daga Ali Muhammad Rabi’u  ’Yan bindiga kimanin guda huɗu dauke da makamai sun kai hari a garin Eruku da ke ƙaramar hukumar Ekiti a jihar Kwara, inda suka sace wani manomi mai suna Mista Aasaru. Rediyon Najeriya ya ruwaito  cewa wannan hari shi ne na biyu da aka kai wa garin Eruku cikin wata guda,...