2025-11-27@22:28:44 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2793
«kera makamin nukiliya»:
Rundunar ’yan sandan Jihar Anambra ta gano gawar wasu mata uku ’yan ƙasar Kamaru da ake zargin waɗanda suka yi garkuwa da su domin neman kuɗin fansa sun kashe su. Haka kuma, rundunar ta ce ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, Nonso Augustine Akpeh da Kingsley Akpeh, waɗanda ake zargin suna cikin gungun masu garkuwar da suka sace matan. Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC Tun dai a ranar Litinin, 10 ga watan Nuwamban nan ne aka sace matan a garin Anam da ke Jihar Anambra, inda suka saba zuwa sayen kayayyakin kasuwanci. Jami’an rundunar na sashen yaki da masu garkuwa da mutane da...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya sauka sheƙa daga jam’iyyar SDP zuwa jami’yyar haɗaka ta ADC. Komawar El-Rufai jam’iyyar ADC a hukumance wani mataki ne da ake ganin zai kawo sabon salo a siyasar adawa wajen ƙalubalantar jam’iyyar APC mai mulki a Zaɓen 2027. An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos A wannan Alhamis ɗin ce El-Rufai ya kammala rajistar zama mamba na jam’iyyar ADC a mazaɓarsa ta Unguwar Sarki da ke birnin Kaduna, inda ya yi alƙawarin amfani da jam’iyyar ADC wajen fuskantar abin da ya kira rashin ƙwarewa a jagorancin gwamnatin jihar. “Ina da cikakkiyar rajista a jam’iyyar African Democratic...
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana jimaminsa kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi, lamarin da ya ce ya kaɗu matuƙa da ya samu labarin. Tinubu ya ce jagoran na ɗarikar Tijjaniya mutum ne mai daraja da ƙima, sannan ya bayyana shi a matsayin madubi wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa. Rasuwarsa za ta ba babban giɓi a Najeriya,” in ji shugaban. Shi ma Tsohon ɗan takarar shugabancin Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana rasuwar Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a matsayin rashi babba ga al’ummar Musulmi na Najeriya da ma Afirka baki ɗaya. A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukansa na sada zumunta, ya bayyana marigayin da babban malami wanda ya koyar da addini...
Iran ta yi Allah wadai da matakin gwamnatin Ostiraliya na ayyana Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) a matsayin “mai tallafawa ta’addanci,” “Matakin da gwamnatin Ostiraliya ta dauka wani abu ne mai laifi ne mai hadari, wanda aka tsara a karkashin gwamnatin Sahayoniya don karkatar da hankalin jama’a daga kisan kare dangi da aka yi a Gaza,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis. Gwamnatin Ostiraliya ta sanya IRGC a matsayin “mai tallafawa ta’addanci” bisa zarge-zargen da ba su da tushe na cewa IRGC ta shirya kai hare-hare kan Al’ummar Yahudawa na Ostiraliya. Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta yi Allah wadai da wannan shawarar da babbar murya, tana mai Allah...
Ɗan wasan gaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid, Kyalian Mbappe ya samu nasarar zura kwallaye huɗu rigis a ragar Olympiacos a wasan mako na biyar na kofin zakarun nahiyyar turai da suka buga a yammacin jiya Laraba. Real Madrid dai caskara Olympiacos 4-3 ne a wasan, lamarin da ya ba ta damar haɗa maki 12 cikin fafatawa biyar. Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji Kawo yanzu dai Mbappe ya shiga gaban Victor Osimhen na Galatasaray wajen yawan zura ƙwallaye a raga a gasar ta kakar nan, inda Mbappe ya ke da 9, yayin da Osimhen wanda ke fama da rauni...
Daga Usman Muhammad Zaria Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu a Jihar Jigawa, Dr. Builder Muhammad Uba, ya aiwatar da wani aiki na da naira miliyan biyar domin tallafa wa aiwatar da Shirin Tallafawa Yara Mata (AGILE) a yankin. Aikin ya hada da gyaran ajujuwa biyu da samar da muhimman kayan aiki, ciki har da injunan dinki, injin yin surfani wato (monogram) da shirin AGILE ya bayar kyauta wanda Dr. Uba ya shirya, ya taimaka wajen ganin an fara amfani da shi, tare da samar da janareta da tabarmi domin inganta koyarwa da horo. Wannan ci gaban ya biyo bayan wani bincike da tawagar AGILE ta jihar Jigawa ta gudanar a baya, inda ta bayyana cewa wuraren koyon sana’o’in na...
Kwamandan rundunar soja ta “Sayyidush-shuhada” dake Tehran Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya bayyana cewa; makamai masu linzami da Iran take da su ne, da kuma jiragen sama marasa matuki suke takawa makiya birki.” Janar Qurbani Muhammad Wali Zadeh ya kuma ce; Albarkacin sadaukar da jinanai da shahidai su ka yi ne da kuma kwazon kwararrun masana, su ka sa Iran samun wannan karfin da take da shi. Wali Zadeh wanda ya halarci taron girmama rundunar sa-kai ta Basiji da kudancin birnin Tehran, ya kara da cewa, Iran ta samu matsayin da take da shi ne a wannan lokacin daga jihadin shahidai da tsayin dakar al’ummar Iran, sannan kuma ya kara da cewa; A halin yanzu karfin Iran a fagen...
Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Bauchi, a matsayin babban rashi ga al’umma. Gwamnan ya bayyana malamin a matsayin jagoran haɗin kai, zaman lafiya, da fahimtar juna tsakanin Musulmi da mabiya addinai daban-daban. ’Yan sanda sun gano harsasai 210 a kan titin Zariya-Funtuwa Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa A cikin saƙon ta’aziyya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mukhtar Gidado, ya sanya wa hannu, gwamnan ya ce Gwamnatin Jihar Bauchi tana alhinin rasuwar malamin. Dahiru Bauchi, ya rasu da safiyar ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a Bauchi, yana da shekara 102. Gwamnan, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi babban malami ne na addinin...
Bayan an zabi kasar Iran a matsayin mamba a kwamitin zartarwa na hukumar yaki da makaman guba ta duniya, wato ‘ the Chemical Weapons Convention (CWC)’ da kuriun jimillar yan majalisar, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa Iran zata yi amfani da damar da ta samu na bin hakkin mutanen kasar Iran dangane da makaman guba wadanda Sadam Husain ya yi amfani da su a kan mutanen kasar a yakin shekaru 8 (1980-88). Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a taron CWC a birnin Hague a ranar Talatan da ta gabata. Ya kuma kara da cewa Iran zata bukaci a hukunta kasashen da suka taimakawa Sadam Husain a wajen...
An kulle Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House tare da wasu gine-ginen gwamnati da dama, sakamakon harbin ɗan bindigar da ya raunata sojoji biyu a kusa da fadar. A yayin, an harbe masu tsaron fadar biyu har lahira. Gwamna Patrick Morrisey da farko ya ce an kashe sojojin, amma daga baya ya ce yana samun “rahotanni masu karo da juna” game da halin da suke ciki, yana mai da cewa za a fitar da ƙarin bayani idan an tabbatar. A cikin wani rubutu a shafin X, ya ce, “Yanzu muna samun rahotanni masu cin karo da juna game da halin sojojin biyu, kuma za mu bayar da ƙarin bayani idan mun samu cikakken rahoto. “Addu’o’inmu suna tare da waɗannan...
’Yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Mata, Super Falcons, sun yi barazanar ƙaurace wa wasannin sada zumunta da Najeriya za ta buga a watan Disamba mai kamawa. ’Yan wasan sun ce za su ƙaurace wa wasannin ne idan har Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) ta ci gaba da jinkirta biyan kuɗaɗen alawus-alawus da suke biyo tun na Gasar Olympics da aka yi a birnin Paris a 2024. Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniya Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro Wasu majiyoyi daga ƙungiyar sun tabbatar cewa ’yan wasan na ci gaba da jiran a biya su haƙƙoƙinsu na wasannin da suka buga, ciki har da alawus na nasarar da suka samu a gasar...
Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta bukaci maniyyatan aikin hajjin 2026 da su gaggauta biyan kudin kujerun su kafin ranar 24 ga watan gobe. Darekta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taro da shugabannin sassa na hukumar da shugabannin shiyya da sauran ma’aikatan hukumar a Dutse babban birnin jihar. Yana mai cewar, hukumar aikin hajji ta kasa wato NAHCON ta bayyana ranar 5 ga watan Disamba da ta kayyade a matsayin ranar rufe biyan kudin kujerun aikin Hajjin 2026 a fadin kasar nan. Ya bayyana cewar ranar itace ranar karshe da hukumar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta kayyade na biyan kudin kujerun...
A yammacin nan ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid za ta kece raini da Olympiacos a ci gaba da Gasar Zakarun Turai, duk da rashin wasu manyan ’yan wasanta biyu. Babban mai tsaron ragar Madrid, Thibaut Courtois, da ɗan wasan baya Dean Huijsen, na fama da jinya, lamarin da zai hana su buga wannan muhimmin wasa. Sojoji sun yi juyin mulki a Guinea-Bissau Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu Yanzu haka jerin ’yan wasan Madrid da ke jinya sun haɗa da: Thibaut Courtois, Dean Huijsen, Antonio Rüdiger, David Alaba, Franco Mastantuono, da Éder Militão. Tun bayan zuwan sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso, Courtois ya riƙe ragamar tsaron raga a dukkan wasanni 17 da suka buga a...
Jakadan kasar Aljeriya a kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi tir da abin da ya kira zalunci isra’ila da kuma ci gaba da kai hare-hare kan mutane kasashen labanon, Syria, da Gaza da kuma gabar yammacin kogin jodan , yayi kira ga majalisar dinkin duniya da ta dauki mataken gaggawa wajen dakatar da wadannan hare haren, kuma akwai dubban laifuffukan da Isra’ila ta aikata da ba’a manta ba kuma ba’a dauki wani mataki a kai ba. Aljeriya ta yi wannan bayanin ne bayan karuwar sukar da ake yi a kwamitin tsaro game da mataken da isra’ila ke dauka a daidai lokacin da ake cikin matsala game da isar da taimakon agaji ga alummar gaza. A taron da kwamitin tsaro...
Babban sakataren tsaron kasar Iran Dr Ali Larijani a shafinsa na X ya soki siyasar Amurka a lokacin ziyararsa a kasar Pakistan kuma ya jaddada cewa Tehran tana son ayi gaskiya a duk tattaunawa da za’a yi. Kalaman na larijani yana nuna matsayar iran ne kan diplomasiyar iyakoki, yace yanci da mallaka wasu abubuwa ne da babu sulhu a kansu, don haka duk wata tattaunawa da Amurka dole ne ta zama cikin yanci da daidaito, za’a iya tattaunawa amma ta gudana ba tare da nuna fifiko ba. Amurka tana kokarin nuna kanta a matsayin wadda za ta kawo sauyi a kowanne lamari na duniya, amma wannan wani nau’i ne na yaudarar kai, don haka mun yarda da tattaunawa ta gaskiya...
Hukumar tsaro ta DSS ta zargi dan jarida kuma mai shiga tsakani da ’yan ta’addar da suka sace fasinjojin jrigin kasan Kaduna-Abuja a shekarar 2022, Tukur Mamu, da karbar Naira miliyan 50 daga kudin fansar fasinjojin. Ana zargin Tukur Mamu da karbar kudin ne daga jagoran ’yan bindigar da ake kira da “Shugaba”. Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000 Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi Mamu na fuskantar tuhumar laifukan ta’addanci, ciki har da karɓar kuɗin fansa daga iyalan waɗanda aka yi garkuwa da su a harin jirgin Kaduna na ranar 28 ga Maris, 2022, hulɗa da kuɗaɗen ’yan ta’adda, hana...
Pars Today – Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, yana mai jaddada muhimmancin Pakistan a yankin, ya ce haɗin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad a fannoni daban-daban yana taimakawa wajen kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya a yankin Ali Larijani, Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, ya ce da sanyin safiyar Talata da ya isa Islamabad cewa Pakistan muhimmiyar ƙasa ce a yankin kuma tana da matsayi mai kyau wajen tasiri ga yanayin tsaro na yankin. A cewar Pars Today, ya ƙara da cewa a matsayinta na maƙwabciyar gabas ta Iran, Pakistan ma tana taka rawa a al’adu, kuma dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu ta daɗe tana da zurfi kuma ta tarihi. Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Jamhuriyar Musulunci...
Babbar Kotun Jihar Oyo da ke Ibadan, babban birnin jihar, a ranar Litinin ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum biyar da ta samu da laifin kashe wani direban tasi. Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin kashe direban mai suna Akeem Shittu a lokacin mummunan rikici a shekarar 2024. DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane? An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a Kebbi Yayin yanke hukunci, alkalin kotun, Mai Shari’a Oyeyemi Ajayi ya bayyana cewa Segun Taiwo (36), Kehinde Ademola (46), Yahaya Adeniyi (45), Chinonso Samson (41), da Opadotun Michael (32) sun yi tarayya wajen yin hadin baki da kuma kisan Shittu. “Na yi la’akari...
Shugaban kungiyar Ansar Allah a Yemen, Sayyed Abdul-Malik al-Houthi, ya aika da sakon ta’aziyya ga Sakatare Janar na Hezbollah, Sheikh Naim Qassem, kan shahadar babban kwamandan dakarun kungiyar Haitham Ali al-Tabtabai da abokansa. Huthi ya jaddada cewa laifin da aka aikata a kansu, tare da hare-haren da ake kai wa Lebanon da Zirin Gaza, yana nuna irin girman kai da Isra’ila ke da shi ne. Sayyed al-Houthi ya kara da cewa shahid al-Tabtabai ya yi kokari matuka wajen cimma manyan-manyan nasarori, kuma ya ba da gudummawa ga hanyar gwagwarmaya don taimakon gaskiya da wadanda aka zalunta, ya kara da cewa tasirin rawar da ya taka a cikin gwagwarmaya zai ci gaba da wanzuwa a cikin lamirin gwagwarmaya da zaluncin Isra’ila...
Daga Bello Wakili Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa dawowar ’yan mata 24 da ’yan ta’adda suka sace a Maga, Jihar Kebbi. ’Yan ta’addan sun kai hari makarantar ranar 17 ga wantan Nuwamban 2026, inda suka yi awon gaba da ’yan matan, jim kaɗan bayan wata rundunar soji ta bar harabar makarantar. Lamarin Kebbi ya haifar da wasu sace-sace makamanta a Eruku da ke Jihar Kwara da kuma Papiri a Jihar Neja. An sako dukkan mutune 38 da aka sace a Eruku ranar Lahadi, inda a wannan ranar ce shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Jihar Neja ya ce an samu yara 50 daga cikin ɗaliban makarantar Katolika da suka ɓace a gidajen iyayensu. Shugaba Tinubu ya...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya gabatar da kasafin kuɗi na shekarar 2026 na sama da naira biliyan 900 ga Majalisar Dokokin jihar. Yayin gabatar da kasafin da aka lakaba wa suna “Kasafin Kirkire-kirkire da Sauyi Don Cigaban Jigawa II,” Gwamna Namadi ya ce za a ware sama da naira biliyan 693.4, wanda ya kai kimanin kashi 76 cikin 100, don ayyukan raya kasa. Gwamnan ya kuma ce sama da naira biliyan 208 za su tafi ne ga ayyukan yau da kullum. A cewarsa, an ware sama da naira biliyan 310 ga bangaren ilimi da lafiya, yayin da kimanin naira biliyan 186 za su tafi ga hanyoyi da sufuri. Malam Umar Namadi ya ƙara...
’Yan Majalisar Tarayya daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
Gwamnatin kasar ta Gambia ta sanar da bai wa jagoran ‘yan hamayyar kasar ta Kamaru Isa Chiroma mafaka bisa dalilai na “‘yan adamtaka”. A wani bayani da ma’aikatar harkokin waje ta kasar Gambia ta fitar, ta bayyana cewa; Chiroma dan shekaru 76 ya isa babban birnin kasar Panjul a ranar 27 ga watan Febrairu a karkashin wata yarjejeniya da aka cimmawa a tsakanin kasashen yankin domin lalubo hanyar warware takaddamar siyasar da kasar Kamaru take fama da ita. Tun bayan da Chiroma ya fice daga kasar ta Kamaru, ya nufi kasar Najeriya, mahukunta a kasar tasa suke kiran da a kama shi. Sai dai maimakon haka, gwamnatin kasar ta Najeriya ta cimma matsaya da mahukuntan kasar Gambia akan a bai...
Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Arakci wanda yake ziyarar aiki a kasar Oman ya gana da manzon musamman na MDD a kasar Yemen Hans Grundberg a jiya Litinin ya yi tir da yadda Haramtacciyar Kasar Isra’ila take keta dokoki tana kai wa kasashen wannan yankin hare-hare. Haka nan kuma ministan harkokin wajen na Iran ya kuma nuna kin amincewar jamhuyriyar musulunci ta Iran da yadda ake ci gaba da killace kasar Yemen, yana mai yin gargadi akan sakamakon da zai biyo bayan keta doka da ‘yan Sahayoniya suke yi da shi ne ci gaba da hargitsi da fadace-fadace a wannan yankin. A nashi gefen manzon musamman na MDD a kasar Yemen ya bukaci ganin Iran ta...
’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu sun yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi wa jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, afuwa bayan da kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai. Kungiyar ’Yan Majalisar Wakilai daga yankin Kudu maso Gabas ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya yi amfani da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi, wajen yi wa Nnamdi Kanu afuwa wanda kotu ta same shi da laifin ta’addanci. Alƙali James Omotosho na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ne ya yanke hukuncin, inda ya same shi da laifi a kan tuhumar da ake masa guda bakwai, sannan ya yanke masa hukuncin daurin rai da rai. Tuni aka tura Nnamdi Kanu...
Ana zargin wata amarya da yi wa angonta yankan rago kwana uku bayan ɗaurin aurensu a Jihar Katsina. Angon mai suna Abubakar Abdulkarim da aka fi sani da Dan Gaske, ana zargin ya rasa ransa bayan da amaryar ta yi amfani da wuƙa wajen halaka shi. Shaidu sun ce ta yi masa mummunan rauni a wuya wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Angon da amaryarsa suka daura aure ne a ranar Alhamis, 18 ga Nuwamba, 2025, amma farin cikin aure ya rikide zuwa makoki a ranar Lahadi da rana lokacin da lamarin ya faru. Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta Wani ɗan uwansa mai suna Aminu...
Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s). Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iran inda suka yi shahada a yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. (1980-1988). Ya zuwa yanzu dai an gano gawakin shahidai fiye da 45,000, sannan akwai wasu fiye da 2000 wadanda ake neman inda suke a cikin kasar ta Iraki. Labarin ya kara da cewa a nan Tehran kadai an yi jana’izar shahidai 100....
Manzon musamman na majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen yayi kira ga kasar iran ta ci gaba da nuna goyon bayan kokarin da duniya ke yi wajen ganin zaman lafiya ya ci gaba da wanzuwa a kasar Yamen Han Grungdbag wakilin majalisar dinkin duniya yayi wannan kira ne a lokacin ganawarsa da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi a birnin muscat na kasar Oman. Grundberg ya bayyanawa Araqchi ci gaban da aka samu kan batun kasar yamen kana yayi kira Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View...
Fitaccen jarumin masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood, Dharmendra Deol da aka fi sani da Dharam Ji, ya mutu yau Litinin yana da shekaru 89 a duniya. Dharam ya riga mu gidan gaskiya ne kwanaki gabani cika shekaru 90 bayan fama da doguwar jinya mai alaƙa da numfashi kamar yadda kafofin labarai suka ruwaito. Slot na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus a Liverpool Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere A watan Nuwambar nan ne labaran ƙanzan kurege suka riƙa yaɗuwa cewa jarumin ya mutu a daidai lokacin da ake jinyar sa a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar ta Indiya. Bayanai sun ce tun dai cikin watan Oktoban da ya gabata,...
Kociyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool, Arne Slot, na fuskantar matsin lamba saboda rashin kataɓus da ƙungiyar ke fama da shi a bayan nan. A yammacin jiya Lahadi ne Nottingham Forest ta je har filin wasa na Anfield, inda ta lallasa Liverpool da ci 3-0 a wasan mako na 12 na gasar Firimiyar Ingila. Mayaƙan Boko Haram sun file kan mata 2 a Borno Ɗaya daga cikin ’yan matan da ISWAP ta sace a Borno ta tsere Forest ta samu nasarar ce ta hannun Murillo a minti na 33, sai Nicolo Savona a minti na 46, sannan Morgan Gibbs-White ya ƙara na uku a minti na 78. Sakamakon wannan rashin nasarar, Liverpool ta sauka zuwa mataki na 11 da maki 18,...
Yundunar ’Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da cewa ɗaya daga cikin ’yan mata 14 da ƙungiyar ISWAP ta sace a Ƙaramar Hukumar Askira-Uba ta kuɓuta, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin gano sauran 13. A sanarwar da ya fitar dangane da irin ƙoƙarin da Jami’an tsaron ke yi na ceto sauran ‘yan matan 13 da ke hannun ‘yan ta’addan, kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce, shugaban gundumar Huyum ya bayar da rahoto a ranar Asabar 22 ga Nuwamba cewa waxanda ake zargin mayaƙan Ƙungiyar ISWAP ne suka sace ‘yan matan, yayin da suke aiki a wata gona a gundumar Mussa. Tawagar ’yan sanda, sojoji, Sibiliyan JTF, da mafarauta da ’yan banga nan da nan suka fara...
Ma’aikatar lafiya a Lebanon ta ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu a wani sabon harin Isra’ila a Kudancin babban birnin Kasar, inda kuma ta raunata kimanin fararen hula 28. A cewar ofishin Firayim Minista Benjamin Netanyahu, harin an kai shi kan “babban hafsan sojojin Hezbollah,” Ali Tabataba’i, wanda Isra’ila ke zarginsa da “jagorantar ƙarfafawa da kuma ba da makamai” ga kungiyar. Shugaban Lebanon Michel Aoun ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa ya nuna rashin halin ko kula da gwamnatin Tel Aviv ke yi wa kiraye-kirayen kasashen duniya na dakatar da keta haddi a kasar Lebanon. Ita ma kungiyar Jihadin Musulunci ta Falasdinu ta yi Allah wadai da harin, tana mai daukar alhakin al’ummar duniya. An ruwaito...
Rundunar Sojin Najeriya, ta ce barin jama’a da aka yi don su kare kansu ne ke rura wutar rikici a Jihar Filato. Birgediya Janar MA Etsy-Ndagi, Shugaban Hulɗar Sojoji Da Fararen Hula ne, ya bayyana haka a lokacin da yake hira da ’yan jarida a Jos. An rufe duk makarantu a Kebbi Ma’aikatan lantarki na shirin shiga yajin aiki a faɗin Najeriya Ya ce barin al’umma domin su kare kansu bai haifar da ɗai mai ido ba, illa ƙara tsananta rikice-rikice. Jihar Filato na fama da rikice-rikice tun daga shekarar 2001, inda mutane da dama suka rasu, wasu kuma suka jikkata. Wasu ƙungiyoyi a jihar sun yi kiran da a bar jama’a su kare kansu saboda yawan hare-hare da suke...
Taron na kasar Brazil akan muhalli wanda shi ne karo na 30 ya amince da bayar da tallafin kudade ga kasashe masu karancin kudaden shiga domin fuskantar matsalar dumamar yanayin duniya. Mahalarta taron da su ka fito daga kasashen duniya mabanbanta, wadanda suke fafutukar ganin an shawo kan matsalar da ake fuskanta a duniya ta sauyin yanayi. Sai dai kuma bayanin da aka fitar bai yi Ishara da tasirin makamashin man fetur da dangoginsa a matsayin wadanda suke taka rawa wajen gurbata yanayin duniya. Sabanin da aka sami a tsakanin tarayyar turai da kuma kasashen larabawa masu arzikin man fetur ne ya sa aka jinkirta yin magana man fetur din da dangoginsa. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya soki hukuncin da kotu ta yanke wa jagoran ’yan awaren ƙungiyar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu. Obi ya bayyana hukuncin matsayin “abun takaici” kuma alamar gazawar jagoranci. Sace ɗalibai: An rufe makarantu a Katsina da Taraba Gobara ta lalata gidaje 40 a sansanin ’yan gudun a Borno A ranar Alhamis ne wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai bayan samun sa da laifukan ta’addanci. Sai dai Obi ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi kuskure tun daga farko wajen tafiyar da lamarin, kuma bai kamata ya kai wannan mataki ba. Ya ce Najeriya na fuskantar matsaloli da dama ciki har da...
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyar mu a yau. Shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata wadanda suka shafi siyasa, tattalin, arziki, zamantakewa tsaro da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu nay au /////… Madalla, masu sauraro zamu fara shirimmu da labarimmu na farko wanda yake cewa majalisar gwamnoni a hukumar IAEA ta amince da wani kuduri na takurawa JMI a taron da ta yi a ranar Alhamis 22 ga watan Nuwamban da muke ciki. Kuduri wanda kasashen E3 ko Traiko na...
Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar. Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a a wani taro na mayakan sa kai a nan birnin Tehran a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, da wannan dalilin ne gwamnatin kasar ta ke karfafa kira ga mutanen kasar su kiyaye hadin kan da suke da shi, su kara dankon zumunci da ke tsakanin kabilu da bangarorin kasar don hana makiya cimma manufofinsu a wannan yakin da ke yi da kasar. Yayi...
Wani tsohon ma’aikacin hukumar leken asiri ta CIA ta kasar Amurka John Kiriakou ba ce a yakin kwanaki 12 tsakanin HKI da JMI, Isra’ila ta yi barazanar jefawa JMI makaman Nukliya idan har Amurka bata kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, ya nakalto Mr John Kiriakou yana fadar haka a cikin makon da ya gabata. Ya kuma kara da cewa saboda wannan barazanar ce gwamnatin shugaba Trump ta kaiwa cibiyoyin makamashin Nukliya na kasar Iran wadanda suke Fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ya ce shugaban yana ganin hare-haren da ya kaiwa cibiyoyin yafi sauki idan an kwatanta da makaman nukliya wadanda HKI ta yi barazanar zata yi amfani da...
A ranar Alhamis da ta gabata ce karamin kwamiti mai kula da al-amuran nahiyar afirka a majalisar dokokin kasar Amurka ya bude tattaunawa dangane da zargin da shugaban kasar Donal Trump yake yin a cewa ana kashe kiristoci a tarayyar Najeriya fiye da duk wata kasa a duniya. Wanda hakan ya say a yi barazanar daukar matakan soje idan akwai bukatar haka don kawo karshen kissan. Jaridar Premium times ta nakalto Chris Smith dan majalisan da ya jagoranci taron yana fadar cewa zargin Trump gaskiya ne kuma shi a karan kansa ya kai ziyara tarayyar Najeriya har sau uku a baya inda sakamakon ya tabbatar da hakan. Sannan Bishop Wilfred Anagbe daga jihar Benue wanda ya halarci taron ta kafar...
’Yan bindigar da suka yi garkuwa da masu ibada a cocin Christ Apostolic Church da ke Eruku, a jihar Kwara, sun nemi Naira miliyan 100 a matsayin kudin fansar kowanne mutum da suka kama. A cewar Faston cocin, Lawrence Bamidele, tsakanin mutane 30 zuwa 35 aka yi garkuwa da su a daren Talata lokacin da aka kai musu mummunan hari suna tsaka da ibada a cocin. Sace ɗalibai: Tinubu ya bai wa Ministan Tsaro umarnin tarewa a Kebbi Muna roƙon Tinubu ya ƙawo ƙarshen taƙaddamar gwamnati da ASUU — Ɗalibai Majiyoyi daga iyalai da shugabannin al’umma sun tabbatar a ranar Alhamis cewa masu garkuwar sun fara kiran ’yan uwan waɗanda aka sace ta hanyar amfani da wayoyinsu. Sakataren cocin, Josiah...
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, da ya koma jihar Kebbi da aiki sakamakon sace ɗalibai ’yan mata 25 da wasu ’yan bindiga suka yi a jihar. Tinubu ya umurci Matawalle, wanda tsohon Gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a Kebbi domin sa ido kan dukkan matakan tsaro da ake ɗauka domin kuɓutar da ɗaliban da aka sace. Babu wani addini da matsalar tsaron Nijeriya ta ƙyale — Fafaroma Za a aurar da marayu 200 a Zamfara ’Yan bindiga sun sace ɗalibai 25 a Makarantar Sakandiren Mata da ke garin Maga na Jihar Kebbi da misalin ƙarfe 4 na Asubahin ranar Litinin. A cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Bayo Onanuga wanda...
Daga Bello Wakili Shugaba Bola Tinubu ya umurci Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle, da ya koma Jihar Kebbi biyo bayan sace dalibai ’yan mata 24 a jihar. An umurci Matawalle, wanda tsohon gwamnan Jihar Zamfara ne, da ya zauna a jihar domin sa ido kan ƙoƙarin da ake yi na kubutar da ɗaliban da aka sace. ’Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 24 na Makarantar Sakandare ta ’Yan Mata da ke garin Maga, Jihar Kebbi, da misalin ƙarfe 4 na asubar ranar Litinin. Matawalle, wanda ake sa ran zai isa Birnin Kebbi a ranar Juma’a, ya samu ƙwarewa wajen fuskantar matsalar ’yan fashi da garkuwa da mutane a lokacin da yake gwamnan Jihar Zamfara daga shekarar 2019 zuwa 2023. Idan...
Daga Usman Muhammad Zaria Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da fitar da Naira Biliyan 3 a matsayin tallafin hadin gwiwa na kowace shekara domin inganta ilimi a matakin farko, wato UBEC 2025 Matching Grant. A wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya fitar ya bayyana cewa za a yi amfani da kudaden ne wajen gina sabbin azuzuwa, gyare-gyare, haka rijiyoyin burtsatse da kuma samar da kayan koyo da koyarwa ga dalibai da malamai. Ya ce, majalisar ta kuma amince da sama da Naira Miliyan 289 domin gina sabbin ofisoshin gudanarwa da gyare-gyare a kananan hukumomi 9 na jihar. A cewarsa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gina ofisoshin...
Iyalan Waɗanda Aka Kashe Yayin Zanga-zangar Bangladesh Sun Yi Maraba Da hukuncin Kisan Tsohuwar Firaminstar
Iyalai da ‘yan uwan wadanda aka kashe a lokacin zanga-zangar da ta kawo karshen gwamnatin tsohuwar Firaminstar Bangaledash Sheikh Hasina a bara, sun yi maraba da hukuncin kisa da wata kotun birnin Dhaka ta yanke mata. An samu Sheikh Hasina da laifin cin zarafin bil adama tare da ba ‘yan sanda umurnin kashe masu zanga-zanga, inda aka yanke mata hukuncin a bayan idonta. Gwamnatin Bangaledash ta bukaci Indiya da ta tasa keyar Hasina da ke gudun hijira a can domin ta fuskanci hukuncin. Wakiliyar BBC ta ce Hukumomin Indiya na cewa suna ci gaba da bibiyar lamarin tsakanin Sheikh Hasina da mahukuntan Bangaledash kuma hakan na nufin Indiya na neman wata hanyar diflomasiyya akan lamarin. BBC
Shugaban kasar rasha vladmir putin ya bayyana cewa ba zamu ja baya daga ayyukan soji da muke yi a kasar Ukrain ba, bayan rahoton da fadar kremlin ta fitar dake nuna cewa dakarunta sun kutsa cikin kasar ukrain suna kusa da birnin Kupiansk mafi mahumimmanci a kasar A loakcin ziyara da babban kwamanda kasar rasha ya kai a wajen da ke cikin yakin Ukrain putin yace yanzu haka dakarun rasha sun kewaye rundunoni 15 na kasar Ukrain a garin Kupiansk, za su bada dama ga sojojin kasar su mika makamansu kuma su yi saranda Kakakin fadar kremlin Dmitry peskov ya fadi cewa putin ya karbi rahoto game da karbe kula da ikon garin Kuoansk . Wannan bayani yazo ne bayan...
Rahotanni sun bayyana cewa a zaman da kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya yayi a baya bayan nan yayi kira a dauki matakin gaggawa don kawo kareshen yaduwa ayyukan ta’addanci a kasashen yammacin Afrika da kuma yankin sahel, yana gargadin cewa yankin na so ya zama cibiyar tsattsauran raayi da rikice- rikice Anasa bangaren babban sakatare janar din majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya bayyan cewa yanayin da yankin sahel da sauran kasahen dake makwabtaka da shi kullum yana kara yin tsananin sosai, kamar kai hare-haren ta’addanci da kuma matsalar da ta shafi mai a kasar mali suna mummunan tasiri a yankin. Haka zalika yayi gargadin cewa kungiyoyin masu iykirarin jihadi masu yankurin kafa daular musulunci a yankin sahara ISGS...
Kafofin yada labarai na duniya sun mayar da hankali kan taron majalisar shugabannin kasashe mambobin kungiyar Shanghai SCO na 24 da aka gudanar kwanan nan a birnin Moscow na kasar Rasha. Fira ministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kungiyar SCO da ta aiwatar da shawarar inganta tsarin shugabanci na duniya da kasar Sin ta gabatar, da karfafa kungiyar SCO a bangaren hadin kai da harkoki da kuma tasirinta. Shekaru 24 da suka wuce bayan kafuwar kungiyar SCO, a karkashin jagorancin ruhin Shanghai, an samu habakar abotan kungiyar, da kara ingancinta, shi ya sa ma ta zama kungiyar yanki mafi girma a duniya, wadda ta kare muradun kasashe mambobin kungiyar, ta kuma inganta zaman lafiya da ci gaban...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar iran Esmail Baghaei yayi tir da shigar isara’ila kasar Siriya ba bisa kaida ba, yayi gargadin cewa ci gaba da kai hare-hare da fadada siyasarta ta mamaya babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron yanki. Haka zalika tahren ta yi gargadin cewa matakin baya bayan nan da isra’ila ta dauka wani bangare ne na nuna tsangwama da kai hare hare da aka dade ana yi ta sama da kasa da kuma mamaye kudancin Syria da zai iya jefa yankin cikin mawuyacin hali. Fira ministan isra’ila banjamin na tanyaho da wasu manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan harkokin wajen da na yaki sun shiga cikin kasar siriya kuma sun zarta iyakar aka yi...
Kwamitin hukumar hana yaɗuwar makamin nukiliya IAEA a Majalisar Dinkin Duniya, ya buƙaci ƙasar Iran da ta bayyana yawan makamashin nukiliyar da ta mallaka. Wannan dai na zuwa ne bayan kwamitin ya amince da wani ƙuduri da zai tilasta wa Iran bayyana musu yawan makamashin nukiliyarta. An yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai Kotu ta sami Nnamdi Kanu da laifukan ta’addanci A cewar sabon ƙudurin da ƙasashe 19 suka yi na’am da shi, dole Tehran ta bayar da kai bori ya hau ta hanyar sallama duk wasu bayanai gamsassu, da kuma ba wa ƙwararrun jami’an IAEA damar shiga wuraren da take gudanar da shirinta na bunƙasa makamashi. Ƙudurin ya kuma ce dole ne Iran ta bayar da...
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, babban birnin Nijeriya, ta yanke wa fitaccen jagoran masu fafutukar kafa ƙasar Biafra Nnamdi Kanu, hukuncin ɗaurin rai-da-rai, bayan samunsa da aikata laifukan ta’addanci. Masu gabatar da ƙara sun buƙaci a yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin kisa, to amma Mai Shari’a James Omotosho, ya bayyana cewa a yanzu ba a amfani da hukuncin kisa, a maimakon haka ya yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya jagoranci manyan jami’an Gwamnatin Nijeriya zuwa Amurka don tattaunawa game da zargin kisan ƙare dangi da ake yi wa Kiristoci. Lamarin ya samo asali ne bayan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya goyi bayan kafa ƙasashe biyu na Isra’ila da Gaza. A farkon watan nan, Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi barazanar daukar matakin soji a kan Nijeriya, kuma ya bukaci ‘yan majalisar dokokin kasar, ciki har da dan majalisa Riley Moore, su binciki lamarin. Ko da yake Nijeriya ta karyata ikirarin, amma Amurka ta ci gaba da jadadda zargin kisan Kiristoci. A ranar Talata, mawakiyar Amurka, Nicki Minaj a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ta...
Gwamnatin Tarayya ta ɗora alhakin dawowar hare-haren ta’addanci, ciki har da sace dalibai mata a jihar Kebbi da kai hari a coci a jihar Kwara, kan kalaman da Amurka ta yi kwanan nan a kan Najeriya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya ce sakonnin da Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa, inda ya zargi Najeriya da “kisan kiyasin Kiristoci” tare da barazanar tura sojojin kasarsa, sun kara wa wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda kaimin kai hare-hare. Babu addinin da ake yi wa kisan ƙare dangi a Binuwai — Gwamna Alia Yadda maganin sauro ya yi ajalin magidanci da iyalinsa a Kano “Kalaman da Amurka ta yi kwanan nan sun kara wa wasu ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke son...
Bayan kwashe watanni da dama ana ta cece-kuce tsakanin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta najeriya da kuma kamfanin jiragen sama na kasar Qatar, daga karshe dai hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta najeriya ta ci tarar kamfanin naira miliyan 5 saboda kate dokokin da suka shafin fasinjojinta. An fitar da wannan sanarwa ce a shafin x na micheal achimugu daraktan kula da hulda da jama’a da kula da fasinjoji, ya kara da cewa wannan hukumci ya sanya adadin kamfanonin jiragen sama da aka ci tara sun kai guda 7 a wannan shekarar ta 2025 Hukumar NCAA ta zargi kamfanin jiragen sama na Qatar airways a watan satumban shekarar da muke ciki da take dokokin kula da...
Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Iran da malesiya sun cimma yaejejeniyar kara fadada dangantar yin aiki tare a bangaren Addinin da Ala’adu musamman a bangaren kimiyar alkur’ani bayan tarurruka da manyan jami’an gwamnati suka yi a birnin kuala Lumpur babban birnin kasar, Wannan yarjejeniyar za ta kara karfafa hadin guiwa tsakanin manyan kasashen musulmi adaidai lokacin da kasashen musulmi suke fuskantar matsalolin aladu da tasirin kasashen yamma a tsarin zaman takewarsu da tashe tashen hankula na siyasa musamman ma kan yankin falasdinu. Kasashen biyu suna da matsaya daya na dogon lokaci a bangaren abincin Halal, aladun musulunci da kuma ilimin Addinin, don haka wannan tattaunawar da aka yi an sake sabunta alakar ne bisa ababen girmama wa na musulunci da...
Wata Kotun Tarayya da ke Abuja, ta sanya ranar 15 ga watan Janairun 2026, don fara shari’ar shugabannin ƙungiyar ’yan ta’adda ta Ansaru; Mahmud Usman da Abubakar Abba. Ana zargin su da jagorantar ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, kuma Hukumar DSS ce ta kama su tare da gurfanar da su a kotu. Ribadu ya jagoranci tawaga zuwa Amurka don ƙaryata zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana An tsara faea sauraren shari’ar a ranar Laraba, amma aka ɗage bayan lauyoyin waɗanda ake tuhuma sun nemi a ƙara musu lokaci. Lauyansu, B.I. Bakum, ya bayyana cewa har yanzu suna jiran takardun zargi da wajen DSS. Haka kuma, ya nemi a mayar da...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa daftarin kudirin da kasar Canada ta gabatar yana cike da siyasa ne kawai hasali ma nuna kin jinin Iran ne. Mataimakin Wakilin Iran a Majalisar Dinkin Duniya, game da daftarin kudurin da Canada ta gabatar, ya ce: “Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta nuna adawarta ta musamman ga wannan daftarin, wanda aka yi shi bisa dalilai na siyasa, son rai, da kuma na neman haddasa barna.” Gholamhossein Darzi, Jakadan Iran kuma Mataimakin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya, ya bayyana a ranar Laraba, a lokacin zaman Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya na Uku kan kudurin kare hakkin dan adam na Canada kan Iran: Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada cewa: “Mun yi...
Kamfanonin labarai na Reuters da AFP sun rawaito cewa Amurka ta shawarci Ukraine ta amince da Crimea da sauran yankunan da Rasha ta mamaye mata da kuma rage girman sojojinta zuwa rabi kamar yadda yake kunshe a sabuwar shawarar da Amurka ta gabatar na samar da zaman lafiya tsakanin kasashen biyu. Ukraine ta sami sabuwar, wacce ke bukatar Kiev ta mika yankunan dake karkashin ikon Rasha da kuma rage yawan sojojinta zuwa 400,000 kamar yadda jami’an Amurka da aka sakaya sunansu suka shaida wa Reuters da kamfanin dillancin labarai na AFP. Shirin ya kuma tanadi Ukraine ta mika dukkan makamai masu kaiwa nesa. Bayanai sun ce da alama shirin ya maimaita sharuddan Rasha wadanda da Ukraine ta sha watsi da...
Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ya jagoranci wata tawagar gwamnati zuwa Amurka domin mayar da martani kan zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya. Wannan zargi ya samo asali ne bayan mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya nuna goyon bayansa wajen kafa ƙasashe biyu tsakanin Isra’ila da Gaza. Wardley ya zama zakaran damben boksin na duniya Hakimi ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon Afirka na bana A farkon wannan watan ne Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ayyana Najeriya cikin jerin ƙasashen matsala ta musamman. Sannan Trump ya umarci wasu ’yan majalisar Amurka, ciki har da Ɗan Majalisa Riley Moore da su binciki lamarin. Duk da ƙoƙarin da Najeriya ta yi na bayyana...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su tafi...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin 2026 na kuɗi Naira tiriliyan 1.36 tiriliyan a Majalisar Dokokin jihar. Kasafin wanda aka yi laƙabi da “Kasafin Gine-gine, Ci Gaban Kowa da Ɗorewar Ci Gaba.” Dukiyar sama da miliyan 500 ta kone a gobarar kasuwar katako ta Gombe Tinubu ya fasa zuwa taron G20 saboda matsalar tsaro a Najeriya Yayin jawabi da ya gabatar a zauren majalisar a ranar Laraba, gwamnan ya ce an tsara kasafin ne don samar da sauye-sauye, kammala manyan ayyuka, inganta ilimi da harkar kiwon lafiya. Ya bayyana cewa za a kashe Naira biliyan 934.6 (kashi 68) a manyan ayyuka kamar hanyoyi, gine-gine da sauran muhimman ayyuka. Sauran Naira biliyan 433.4 (kashi 32), za su...
Majalisar Dattawa ta shiga cikin jimami a ranar Laraba bayan mutuwar Sanata Okey Ezea, mai wakiltar mazabar Enugu ta Arewa. Bayanai sun nuna marigayin ya rasu ne a kasar Burtaniya inda yake jinya. ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ Mai taɓin hankali ya kashe soja a Legas Ezea, wanda aka zaɓe a ƙarƙashin jam’iyyar LP, shi ne kaɗai Sanatan da ya ci zabe daga Enugu karkashin jam’iyyar a Majalisar Dattawa ta 10. Rasuwarsa ta sa ya zama sanata na biyu daga yankin Kudu maso Gabas da ya rasu cikin shekaru biyu, bayan mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah daga Jihar Anambra, wanda shi ma ya rasu a Landan a watan Yuli 2024 yana da shekara 52. Da labarin...
Wani mutum da ake zargin yana fama da matsalar tabin hankali ya kai hari tare da kashe wani soja a yankin Imota da ke Ikorodu a jihar Legas. Lamarin, wanda ya faru a fili da rana tsaka a ranar Lahadi, ya sa makwabtan wurin da dama guduwa don neman tsira. Gobara ta laƙume kasuwar Katako a Gombe Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Shaidu sun bayyana cewa wanda ya kai harin, wanda ba shi da makami sai sanda ta itace, ya kusanci sojan ya dinga dukan shi da sandar. Sojan da ya rasu, wanda aka ce yana aiki a karkashin Operation AWASE, rundunar haɗin gwiwa ta musamman da ke yaki da laifuka...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa dole ne kudirin Amurka da MDD ta amince da shi ya tabbatar da kare hakki da yancin Falasdinawa a sahun gaba samar da kasar Falasdinu. Jakadan Iran kuma wakilin dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iraqini, ne ya bayyana haka, a matsayin martanin ga amincewar da kwamitin Tsaro ya yi da daftarin kudirin Shugaba Donald Trump na Amurka game da Gaza. Iran ta yi gargadi akan amfani da wannan kuduri a hanyar da za ta keta ko ta wargaza hakkokin al’ummar Falasdinawa ba, musamman ‘yancin cin gashin kai da kuma kafa kasar Falasdinawa mai cin gashin kanta. A Kudurin da aka amince dashi jiya Litinin, Iran ta jaddada damuwar da wasu membobin...
Wani harin Isra’ila ya kashe akalla mutane 15 a sansanin ‘yan gudun hijira na Falasdinawa mafi girma a Lebanon. An kuma kwantar da adadi mai yawa na mutane a asibitoci a birnin Sidon bayan harin na Ain al-Hilweh da ke can ranar Talata, in ji kamfanin dillancin labarai na kasar Lebanon (NNA). Sojojin Isra’ila sun yi ikirarin kai harin, kan abin suka kira, membobin kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas a sansanin. Saidai kungiyar ta yi watsi da zargin, tana mai cewa yawancin wadanda abin ya shafa yara ne. https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false https://hausatv.com/wp-login.php?adminpanel&redirect=false Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name*...
A ranar Alhamis, 20 ga watan Nuwamban 2025, ake sa ran Majalisar Wakilan Amurka za ta gudanar da zama na musamman domin bincikar zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Kwamitin Majalisar Wakilan kan Afirka ya sanya ranar domin bitar fasalin da Shugaba Donald Trump ya yi kwanan nan na sanya Nijeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido na musamman, CPC, kan zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan kiyashi. Gwamnan Taraba ya dakatar da ficewa daga PDP saboda sace ɗalibai a Kebbi Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a Kebbi Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa, an gayyaci mambobin Kwamitin Harkokin Waje na majalisar, wanda aka shirya za a yi tattaunawar da...
Ministan tsaron Iran Birgediya Janar Aziz Nasirzadeh ya kai ziyarar aiki a Hadaddiyar Daular Larabawa don inganta dangantakar soja da kuma huldar tsaro a yankin. Nasirzadeh ya jagoranci wata babbar tawaga, wadda ta isa Dubai a ranar Litinin bisa gayyatar takwaransa na Hadaddiyar Daular Larabawa. Ministan tsaron Iran yana shirin yin tattaunawa da jami’an Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma halartar taron Dubai Airshow na 2025, wanda aka shirya gudanarwa a tsakanin 17-21 ga Nuwamba. Ziyarar ta zo ne a karkashin tsarin diflomasiyyar tsaron Iran kuma tana da nufin inganta huldar yanki da kuma gano damar yin hadin gwiwa a fannoni daban-daban. A lokacin rangadin baje kolin, an shirya cewa ministan tsaron na Iran zai yi tarurruka da jami’an tsaro daga...
Hukumar ƙwallon ƙafar Afirka CAF, ta bayyana cewa bayan tankade da rairaya da ta yi, a yanzu ’yan wasa uku kacal ne suka rage a takarar gwarzon nahiyyar na bana. A wata sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana Achraf Hakimi da Mohamed Salah da Victor Osimhen, a matsayin sauran ukun da suka rage a takarar gwarzon dan ƙwallon ƙafar Afirka na bana. Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno Hakimi, kyaftin din Morocco, ya lashe kofuna daga ciki har da Champions League a PSG — na farko a tarihin ƙungiyar — da Ligue 1, da European Super Cup, da kuma kai wa zagayen ƙarshe...
Mataimakin shugaban kasar Iran na farko ya bayyana cewa: Iran tana da kyakkyawar alaƙa ta musamman da kuma al’adu da membobin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Shanghai Mataimakin Shugaban Kasa na Farko na Iran ya ce, “Iran tana da alaƙar haɗin gwiwa na musamman da al’adu da dukkan ƙasashe membobin Ƙungiyar Haɗin Kan Shanghai (SCO), kuma abin farin ciki, ƙasar Iran ta shiga ƙungiyar SCO a hukumance cikin shekaru biyu da suka gabata.” Da yake jawabi a Filin Jirgin Sama na Mehr-abad kafin ya tashi zuwa Rasha don halartar taron kolin kungiyar Shaanghai ta SCO, Mataimakin Shugaban Kasa na Farko Mohammad Reza Aref ya ce, “Ƙungiyar SCO ƙungiya ce mai tasowa amma mai ƙarfi da cikakken iko. Jimillar yawan al’ummar ƙasashe...
Na’ini: Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Da Kansa Ya Jagoranci Yaki Kwanaki 12 Da Aka Kaddamar Kan Iran
Jagoram juyin juya halin Musulunci da kan sa ya jagoranci yaki da harkokin al’umma a lokacin yakin wuce gona da iri na karshe kan Iran Kakakin Rundunar Tsaron kare Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC), Brigadier Janar Ali Mohammad Na’ini, ya tabbatar da cewa: Maƙiya ‘yan sahayoniyya ba su da yanayin sabon yaƙi, kuma abin da ake gabatarwa a yau shine yaƙin tunani da yaƙin da aka saba gani. A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Brigadier Janar Na’ini ya ba da labarin lokutan shaƙatawa da ba zato ba tsammani na barkewar yaƙin da kuma shahadar wasu manyan kwamandojin soja na ƙasar. Ya kuma lura da yadda aka sake gina sansanin umarni a cikin ɗan gajeren lokaci da kuma...
Hukumar ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta ce hauhawar farashin kayyayaki a ƙasar ya ragu zuwa kashi 16.05 cikin 100 a watan Oktoban 2025. Cikin rahoton wata wata da hukumar ke fitarwa, ta ce hauhawar farashin ya ragu ne da kashi 1.97 idan aka kwatanta da kashi 18.02 da aka samu a watan Satumba. ’Yan Majalisar Dokokin Taraba 16 sun sauya sheka daga PDP zuwa APC An ɗaura auren Sanata Kawu Sumaila da wata jami’ar soji a Kano A watanin baya-bayan an riƙa samun raguwar hauhawar farashin kayyaki a ƙasar. Aminiya ta ruwaito cewa, tun dai daga watan Yunin bana, hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da sauka a ƙasar har kawo yanzu. Ana iya tuna cewa, tun watanni kadan da...
Tawagar wasannin Wushu na kasar Iran ta nuna rawar gani sosai a gasar hadin kan kasashen musulmi da ake yi a kasar saudiya inda ta samu lambobin yabo guda 4 wato Azurfa 1 tagulla 1 da kuma zinariya 2 a ranar karshe na gasa a wannan bangaren. A bangaren mata kuma Sara shafi’I wacce ta fara fitowa a gasar kasa da kasa ta doke abokiyar hamayyarta daga kasashen kargyzstan da Turikiya ta kai ga wasan karshe , daga nan kuma ta yi galaba a kan abokiyar hammayarta ta kasar masar da ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagayen farko don samu lambar zinariya Haka zalika a bangaren mata masu nauyin kilograme 60 Sohaila Mansurian ta...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ba Mu Samu Labarin Kai Wa Laftanar Yerima Hari Ba – Ƴansanda November 17, 2025 Manyan Labarai Sarki Sanusi Ya Shawarci Unguwannin Da Suka Fuskanci Matsalar Tsaro Su Sa Idon November 17, 2025 Manyan Labarai Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja November 16, 2025
Asusun Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) ya bayyana cewa ya raba jimillar kuɗi Naira biliyan 116 domin tallafa wa dalibai a faɗin ƙasar nan wajen biyan kuɗin makaranta da kuma kula da rayuwarsu ta yau da kullum. Shugaban NELFUND, Akintunde Sawyerr ya bayyana a Abuja cewa, daga cikin kuɗin, an tura Naira biliyan 65 aka tura kai tsaye zuwa makarantu 239 na tarayya — jami’o’i, kwalejojin fasaha da kwalejojin ilimi — domin biyan kuɗin makarantar ɗaliban da aka amince da buƙatar lamuninsu. Sauran Naira biliyan 51 kuma an tura ne kai tsaye ga ɗaliban a matsayin tallafin kula da rayuwa na wata-wata. Ya ce: “Mun raba Naira biliyan 65 ga makarantu da kuma Naira biliyan 51 ga ɗaliban domin tallafin...
Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan idan Kwamitin Gwamnonin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ya amince da wani sabon kuduri da bai dace da Iran ba. Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kazem Gharibabadi, ne ya bayyana hakan, a gefen taron kasa da kasa mai taken ‘’yancin kasa da kasa na fuskantar barazana a martanin ga kungiyar tarayyar Turai a sahun gaba (Faransa, Burtaniya, da Jamus) da suka gabatar da wani sabon kuduri kan Iran a taron Kwamitin Gwamnonin IAEA na mako mai zuwa. “Ina fatan Tarayyar Turai za ta yi aiki da hankali kuma ba za ta gabatar da kudurin a hukumance ba, amma idan ta yi, Iran za ta yi gyara na...
Babban jirgin ruwan yaki mai dakon sojojin kasa da sauran kayan yaki da ake amfani da su a kan-tudu samfurin 076 irinsa na farko a kasar Sin mai suna Sichuan, ya koma tashar jiragen ruwa da ke birnin Shanghai da misalin karfe 5 na yamma a yau Lahadi, bayan kammala gwajinsa na farko a teku. Gwajin jirgin na kwanaki uku ya kunshi gwada ayyukan na’urar da ke sarrafa tafiyar jirgin da na’urorin lantarkinsa da sauran kayayyakin aiki, inda aka samu sakamakon da ake sa ran samu. Kasancewarsa sabon jirgin ruwan yaki na zamani na rundunar sojojin ruwa ta ‘yantar da jama’ar kasar Sin, jirgin ya kunshi sabbin fasahohin majaujawar mayen karfe mai aiki da lantarki, da fasahohin rike jiragen sama...
Richard A falk Tsohon mai bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka kan alummar Gaza da majalisar dinkin duniya ta nada ya fuskanci matsalar a kasar kanada inda aka tsare shi tare da yi masa tambayoyi a wata tafiya da yayi don halartar taron dake da alaka da yankin Gaza. Falka dan shekara 92 da haihuwa, hukumar kula da hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya ta nada shi a shekara ta 2008 na tsawon shekaru 6 a matsayin dan rahoton musamman don gudanar da bincike kan laifukan yaki da HKI ta tafka a yankin falasdinu. Falk ya bayyana cewa dalilin yin tambayoyi na tsawon lokaci ga manyan masana da ba sa yin wata barazanar tsaro a filin saukar...
An zaɓi tsohon Ministan Ayyuka na Musamman da Harkokin Gwamnati, Kabiru Tanimu Turaki, a matsayin sabon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa a yayin babban taron jam’iyyar da aka gudanar a birnin Ibadan na Jihar Oyo a ranar Asabar. PDP ta ce Barista Kabiru Tanimu Turaki, ya yi nasarar ce akan Sanata Lado Ɗan Marke da ƙuri’u sama da dubu ɗaya da ɗari biyar, da wakilai 3, 131 suka halarta. PDP za ta sake farɗaɗowa idan shugabanninta suka cire girman kai — Anenih Fintiri ya yi watsi da korar Wike daga PDP Hakan dai na zuwa ne yayin da jam’iyyar ta PDP ta dakatar da Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar, yayin da gwamnonin Adamawa da na Fulato suka ƙalubalanci matakin suna...
Iran ta yi gargadin cewa tsanantar ayyukan sojojin Amurka a yankin Caribbean da Latin Amurka na haifar da babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma ta yi kira da a girmama hurumi da cikakken yancin Venezuela. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmail Baghai, ya ce barazanar Amurka na amfani da karfi kan zababiyar gwamnatin Venezuela ya saba wa dokokin kasa da kasa. Ya kuma bayyana cewa irin wadannan ayyuka tamkar keta ka’idojin Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, musamman haramta amfani da karfi. A daya bangaren kuma, M. Baghai ya yi Allah wadai da hare-haren da Amurka ke kai wa jiragen kamun kifi na Venezuela a matsayin misalai na kisan gilla ba...
Gwamnatin Beirut ta ce za ta shigar da kara a kan Isra’ila gaban Majalisar Dinikin Duniya game da gida katangar siminti a kan iyakar Kudancin Lebanon. A cikin wata sanarwa data fitar fadar shugaban Lebanon ta sanar da cewa Beirut za ta shigar da kara a Majalisar Dinkin Duniya game da gina katangar. Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya umarci Ministan Harkokin Wajen kasar Youssef Radji da ya umurci tawagar Lebanon ta Dindindin a Majalisar Dinkin Duniya da ta shigar da karar gaggawa a kwamitin Tsaro kan gwamnatin Isra’ila saboda gina katangar siminti a kan iyakar kudancin Lebanon, wadda ta wuce ‘’Layi Shuɗi’’ da aka zana bayan janyewar Isra’ila a shekarar 2000. Hukumomin Lebanon sun ce katangar simintin da sojojin Isra’ila...
Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
Kalaman tayar da husuma na firaministar Japan Sanae Takaichi, dangane da batun yankin Taiwan na kasar Sin, na ci gaba da shan suka da Allah wadai daga sassan kasa da kasa. Wani sakamakon kuri’un jin ra’ayin al’umma da kafar CGTN ta gabatar ya nuna yadda akasarin masu bayyana mahanga suka amince da cewa, matakin na Takaichi tsoma baki ne cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, kuma akwai bukatar gaggauta sanya ido kan karuwar burikan wasu jagororin Japan masu tsattsauran ra’ayi, na ruguza odar kasa da kasa ta bayan yakin duniya na biyu. Kaso 91.1 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyin na ganin kamata ya yi Japan ta gyara tarihin ta’asar da ta aikata ta hanyar aiwatar da matakai na hakika,...
Jakadan kasar Sin a Japan Wu Jianghao, ya gana da mataimakin ministan harkokin wajen Japan Takehiro Funakoshi a jiya Juma’a, inda ya bayyana matukar adawar kasarsa, da korafi a hukumance, dangane da kalamai marasa dacewa da firaministar Japan Sanea Takaichi ta furta dangane da kasar Sin. Jakada Wu, ya ce munanan kalamai masu tayar da husuma na Takaichi, dangane da yankin Taiwan na Sin, wadanda aka jiyota tana yi kwanan baya, a majalissar dokokin kasarta sun sabawa hankali, sun tsallaka jan-layin kasar Sin, kana barazanar nuna karfi ne da neman takalar yaki. Kazalika, firaministar ta Japan ta ki amincewa da kuskurenta, ta ki janye kalaman, ko sassauta mummunan tasirinsu. Don haka matakin nata ya shaida matukar kaucewa gaskiya, da fankamar...
Rahotanni sun bayyana cewa jakadan iran a majalisar dinkin duniya Amir Saeid Iravani yayi gargadin cewa Tehran ba za ta taba mika wuya ga matsalin lmbar soji ba, ko ta siyasa ko kuma takunkumin tattalin Arziki, kuma ta yi tir da Amurka da Isra’ila game da harin da ta kai kan tashoshin nukiliyarta da ya sabama doka, da kuma yin fuska biyu a matakenta na kasa da kasa Wannan bayani na Iravani yana zuwa ne adaidai lokacin da zaman tankiya ke kara Kamari bayan hari da Amurka da isra’ila suka kai a watan yuni shekara ta 2025 da muke ciki, wanda iran tace wurare ne dake karkashin kulawar hukumar nukiliya ta Duniya IAEA. Kamalan nasa sun nuna cewa bisa mahangar...
’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla. “Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.” Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU Mutum ɗaya...
’Yan banga 16 sun kwanta dama a yayin da ’yan bindiga suka yi garkuwa da mutane 42 a wani hari na daban a Ƙaramar Hukumar Mashegu da ke Jihar Neja. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bindiga sun kai hare-haren ne daga ranar Alhamis zuwa Asabar, lamarin da ya sa mutane da dama yin ƙaura daga ƙauyuka Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa maharan sun fara kai farmaki ne a ƙauyen Dutsen Magaji, inda suka yunwa mutane 22 kisan gilla. “Da suka kawo hari, ’yan banga sun bi su, ɓangarorin suka yi musayar wuta, amma suka kashe ’yan Banda biyar, wasu uku na karɓar magani a Asibiti.” Gwamnati na jefa makomar ilimi cikin hatsari — ASUU Mutum ɗaya...
Kyaftin ɗin tawagar ƴan wasa matan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara 17 (Flamingos), Shakirat Moshood, na cikin jerin ƴan wasa uku da suka kai matakin ƙarshe domin lashe ƙyautar Matashiyar Ƴar Wasan CAF ta 2025. Sauran ƴan wasan da ke fafatawa da ita su ne Moha El Madani daga Morocco da Adji Ndiye ta Senegal. Moshood ta yi fice a manyan wasanninta a gasar cin kofin Duniya na mata ƴan ƙasa da shekara 17 ta FIFA a 2025, ko da yake tawagar da Bankole Olowookere ke jagoranta ta tsaya a zagaye na 16. A duk tsawon gasar, ta kasance ɗaya daga cikin fitattun ƴan wasan da suka yi ƙwazo a tawagar da kyakkyawan salon wasa. Wasu Mahara Sun Kashe Mata...
Iran ta bukaci kasashen duniya dasu gaggauta daukar mataki kan halin da ake ciki a Sudan musamman a yankin El Fasher don magance matsalar dake ta’azzara a arewacin Darfour. Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Ali Bahraini, ne ya bayyanan hakan a jawabinsa yayin zaman musamman na 38 kan yanayin kare hakkin dan adam a yankin El Fasher da kewaye a yayin rikicin da ke ci gaba da faruwa a Sudan. Mista Bahraini ya yi gargadi game da yunwa, yawan ‘yan gudun hijira da kuma tasirin tsoma bakin kasashen waje kan rikicin. Wadanan matsalolin sun haifar da daya daga cikin rikicin jin kai mafi muni a duniya, wanda ke bukatar kulawa nan take daga kasashen duniya,” in ji jakadan. Jami’in...
Da yake ƙarin haske kan muhimman sassan da aka fi bai wa fifiko, Gwamnan ya bayyana cewa, ɓangaren tattalin arziƙi da ci gaban al’umma ne suka samu kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin, inda aka ware sama da Naira biliyan 269 don sanya hannun jari a muhimman fannoni. Fannin ayyuka, gidaje da sufuri ne ke kan gaba da Naira Biliyan 135.9, sai ruwa, muhalli da gandun daji da aka warewa Naira Biliyan 88.4, yayin da noma, kiwo da ƙungiyoyin gama ya samu Naira biliyan 20.57. A fannin harkokin zamantakewa, an ware Naira biliyan 80 don samar da ayyukan ci gaba da gina jama’a, inda ilimi ya samu Naira biliyan 31.9, yayinda ilimi mai zurfi ya samu Naira biliyan 17.5. Ɓangaren...
An kashe wani da ake zargin ɗan bindiga ne, yayin wani artabu da ’yan sanda da ’yan sa-kai suka yi da wasu mahara a Jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ƙauyen Adekanbi, kusa da garin Bode Saadu. Kotu ta sake hana PDP gudanar da babban taronta na ƙasa Mutfwang ya musanta raɗe-raɗin sauya sheƙa zuwa YPP Rahotanni sun nuna cewa ’yan bindigar sun yada zango a saman wani dutse da ke kallon ƙauyen. Suna hangar jami’an tsaro sai suka fara harbi ba ƙaƙƙautawa. ’Yan sanda da jami’an sa-kai sun yi artabu tare da tarwatsa maharan, inda wasu daga cikinsu suka tsere da raunin harbin bindiga. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Adetoun Ejire Adeyemi, ta tabbatar da faruwar lamarin...
Wanda ya jagoranci sallar juma’a a Tehran Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya yi kira ga jami’an diplomasiyyar kasar Iran da su kai karar shugaban kasar Amurka Donald Trump a kotunan kasa da kasa, bayan da ya yi furuci da cewa shi ne ya jagroanci harin da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kawo wa Iran. Ayatullah Sayyid Ahmad Khatami ya kuma kara da cewa, ya kamata a fitar da bayani na yin tir da wannan maganar sannan kuma a kai kara a cibiyoyin duniya. Da ya koma yin Magana akan hijabi kuwa, limamin na Tehran ya bayyana cewa, sanya hijabi ga mata,hukunici ne da addini da kuma doka, sannan ya ambato wani marubuci dan Amurka da yake cewa: Idan har matan Iran...
An sanya ranar 25 ga watan Nuwamba a matsayin ranar da za a fara shari’arsa kan zargin karkatar da biliyoyin kuɗi da EFCC ta gabatar. Obiano ya yi gwamna a Jihar Anambra daga 2014 zuwa 2022. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Musulmin da Aka Kashe A Zamfara, Katsina Da Sokoto Sun Ninka Na Kiristoci A Tsakiyar Najeriya: MACBAN November 14, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Wa Mutum 4 Hukuncin Kisa Kan Kashe Wani Makanike A Kano November 14, 2025 Manyan Labarai Bayan Barazanar Amurka: Sultan Ya Nemi Hadin Kan ‘Yan Nijeriya Wajen Yaki Da Ta’addanci November 14, 2025
El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.” Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Rikicin...
Cibiyar dake kula da noman dabino ta kasa a Iran, ta ce kasar ta zamo ta farko wajen fitar da dabino a duniya, inda take samar da tan miliyan 1.5 a kowace shekara. Bayannin ya zayyana Kasashe goma mafiya samar da dabino a duniya wadanda su ne Masar, Saudiyya, Iran, Aljeriya, Pakistan, Iraki, Sudan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Oman, da Tunisiya, wanda ya nuna Iran na cikin kasashe na uku na farko. Kuma a yadda Iran ke fitar da tan 430,000 na dabino a kowace shekara, hakan ya sa ta kasance ta farko wajen fitar da dabino a duniya, sai Saudiyya da tan 390,000 sai kuma Hadaddiyar Daular Larabawa da tan 330,000. Fitar da dabino daga Iran an kiyasta yana samar...
Kasashen Iran da Turkiyye sun jaddada mahimmancin karfafa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Wannan bayyanin ya fito ne bayan tattaunawar wayar tarho data wakana tsakanin ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi, da takwaransu na Turkiyye Hakan Fidan, game da dangantakar dake a tsakanin kasashen biyu da kuma halin da ake ciki a yankin da ma duniya. A yayin tattaunawar ta wayar tarho, Ministocin Harkokin Wajen Iran da Turkiyya sun yi nazari kan dangantakar kasashen biyu kuma sun jaddada muhimmancin karfafawa da bunkasa dangantaka a dukkan fannoni masu amfani. Yayin da yake yaba wa kokarin rage tashin hankali tsakanin Pakistan da Afghanistan, Ministan Harkokin Wajen Iran ya jaddada muhimmancin karfafa shawarwari don kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a...
Haka zalika, ya buga misali da Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, da aka yi garkuwa da shi, kuma aka biya wadanda suka sace shi miliyoyin kudade kafin a sako shi, wanda ya bayyana hakan a matsayin babban abin takaici. Dangane da batun Shugaban Amurka Donald Trump, Sultan Sa’ad ya bukaci Nijeriya da kada ta bari wasu kasashe su raba kawunansu, ya kuma bayar da tabbacin cewa; duk da kalubalen da ake fuskanta, Nijeriya za ta ci gaba da kasancewa mai girma da kuma ci gaba da samun hadin kai. Har ila yau, Tsohon Babban Hafsan Sojin Kasa, Abubakar Danbazau, a jawabinsa ya bayar da shawarar cewa; dole ne a magance matsalar rashin tsaro, matsalolin fatara, sauyin yanayi, rashin aikin...
Wasu Yahudawa ’yan kama-wuri-zauna sun lalata tare da kona wani masallaci da ke gabar yammacin kogin Jodan da Isra’ila ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Falasɗinu (WAFA) ya ruwaito a ranar Alhamis. WAFA ya ce Yahudawan sun kuma yi rubuce-rubucen batanci a bangon masallacin da ke cikin wani ƙauye a arewa maso yammacin yankin, da safiyar ranar. HOTUNA: NDLEA ta ƙone tan dubu 52 na miyagun ƙwayoyi a Zariya NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Manoman Najeriya Noman Rani Wasu kafafen yaɗa labarai kuma sun ce rubuce-rubucen da aka fesa da fenti sun haɗa da cin mutuncin Annabi Muhammad (SAW) da harshen Ibrananci. Rundunar sojin Isra’ila ta ce tana gudanar da bincike kan zargin. Babu rahoton rauni...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk shekara bayan girbin damina, ana sa ran manoma su ci gaba da noma a lokacin rani domin tabbatar da wadatar abinci da bunkasar tattalin arziki. Sai dai hakan na fuskantar kalubale da dama da ke hana yawancin manoma shiga noman rani. Kamar yadda masana suka sha bayyanawa, akwai dalilai da dama dake hana manoma shiga noman rani a duk lokacin da aka ce damina ta tattara inata intat. Shin ko wadanne kalubale ne ke hana manoma shiga noman rani bayan damuna ta wuce? NAJERIYA A YAU: Yadda Raguwar Maniyyatan Najeriya Ke Tasiri Ga Aikin Hajji A Najeriya DAGA LARABA: Tasirin Da Tura Jami’an ‘Yan Sanda Kare Manyan Mutane Zai Haifar...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya yi kira ga kasar Japan da ta janye kalaman baya-bayan nan da firaministar kasar ta furta, dangane da yankin Taiwan na kasar Sin, in ba haka ba, ta shirya girbar sakamakon danyen aikinta. Lin Jian, ya yi kiran ne yayin taron ganawa da manema labarai na yau da kullum a yau Alhamis, lokacin da yake amsa tambayar da aka yi masa dangane da kalaman firaministar Japan Sanaen Takaichi, game da yankin Taiwan na kasar Sin, wadanda kuma ta ki ta janyewa. Lin, ya ce a baya-bayan nan Takaichi ta furta kalaman tayar da husuma, dangane da yankin na Taiwan, yayin da take tsokaci a majalisar dokokin kasarta, inda ta ambata yiwuwar...
Allah Ya yi wa Bebejin Katsina, Alhaji Nuhu Yashe, rasuwa a daren nan na Alhamis. Wakilimu ya ruwaito, basaraken ya amsa babban kiran ne a yayin da ake gudanar da sallar Isha’i. Kafin rasuwarsa, marigayin shi ne Hakimin Kusada, kuma suruki ne ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman. Haka kuma, shi ne kakan Magajin Garin Katsina, Alhaji Aminu Abdulmuminu Kabir. Ana sa ran za a bayyana lokacin da za a yi jana’izarsa nan gaba. Karin bayani zai biyo baya…