2025-10-13@19:37:47 GMT
إجمالي نتائج البحث: 4873
«ne wanda ya»:
Ya ƙara da cewa hukumar ta ƙara himma wajen aikin al’umma (CSR), tana taimakawa hukumomi masu ruwa da tsaki da al’ummomi domin karfafa zaman lafiya da tattalin arziki. A cewar Issa-Onilu, wannan nasara da aka samu a watan Satumba na nuna cewa hukumar Customs ba wai kawai tana cigaba da gyara ba ce, har tana kafa sabon ma’auni na kwarewa da ingantaccen aiki a tsarin gwamnati. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano October 13, 2025 Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa...
Ya kuma ce matakan takaita fitar da ma’adanan farin karfe da Sin ta dauka a baya bayan nan, ba su da alaka da kasar Pakistan. Yana cewa matakai ne da gwamnatin Sin ta dauka bisa doka da oda da nufin inganta tsarinta na fitar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Hada-Hadar Cinikayyar Waje Ta Sin Ta Karu Da Kaso 4% Cikin Watanni Tara Na Farkon Bana October 13, 2025 Daga Birnin Sin Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Da Shawarwari Hudu A Taron Kolin Mata Na Duniya October 13, 2025 Daga Birnin Sin Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina October 12, 2025
Ɗan Majalisar Tarayya mai Wakiltar Sabon Gari Daga Jihar Kaduna, Sadiq Ango Abdullahi, ya fice daga Jam’iyyarsa ta PDP. Honorabul Abdullahi wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kwamishinan Hukumar Kula da Hanyoyi (FERMA) ya alaƙanta ficewarsa da rikicin cikin gida da rabuwar kai da ya ki ci ya ƙi cinyewa a jam’iyyar. A ranar Litinin ya aike da wasikar ta ficewa ga Shugaban PDP na Mazabar Hanwa da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Gari, yana mai cewa rikicin ya hana shi taɓukawa matsayin zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya. Ya cewa saboda haka yana dacewar ficewarsa daga jam’iyyar ba tare da la’akari da siyasa ba, domin amfanin ɗauƙacin al’ummar mazabar. Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph Zaben Kamaru: Issa Tchiroma Bakary...
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar. ‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron...
Ministan Ilimi, Dokta Tunji Alausa, ya caccaki matakin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta dauka na fara yajin aiki na tsawon makonni biyu, yana mai bayyana matakin a matsayin wanda bai kamata ba kuma bai dace ba ganin irin kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na biyan kusan dukkanin bukatun kungiyar. Da yake magana a wani shiri na gidan Talabijin na Channels, ‘The Morning Brief’ a ranar Litinin, Alausa ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin da ASUU ta dauka na tsunduma yajin aiki duk da kokarin da gwamnatin ke yi akansu. “A cikin shekaru biyun da suka gabata, babu wani batun yajin aikin ASUU, saboda kokarin da gwamnati ke yi akan biyan duk bukatunsu. “A cikin sa’o’i 24 da...
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar. Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta. Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako. Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista...
“Shekaru goma da suka wuce, gudummawar da ma’adanai ke bayarwa ga GDP na kasarmu bai wuce 0.5% ba, amma a yau ya karu zuwa 1.8% – alkalumman NBS suka nuna a cikin rabi na biyu na 2025 wanda ba a taba ganin irinsa ba”. Da yake tsokaci kan ci gaban fannin, Ministan ya bayyana cewa, makon hako ma’adanai na Nijeriya ya yi nuni da yadda masana’antar ke sauya tunani zuwa tsari mai kyau, da sabbin abubuwa, da ke lalubo masu zuba jari na kasa da kasa. Ya bayyana cewa, sauye-sauyen sun tattara ne a kan gaskiya, rage haɗari, da inganta masana’antar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27...
Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 9 tare da kwato kudi fansa kimanin Naira miliyan 5 a yankunan Magumeri da Gajiram a jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), Laftanar Kanar Sani Uba , ya ce sojojin da suke sintiri a yankunan ne suka hallakan mayakan bayan sahihan bayanan sirri kan zirga-zirgar ’yan ta’addan a kusa da Goni Dunari a Karamar Hukumar Magumeri. Sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025 ta ce, “Dakarun mu sun yi gaggawar daukar matakin dakile barazanar bayan da suka ga yadda ’yan ta’addan suka kona gidaje tare da tsoratar da mutanen yankin.” Ya bayyana cewa sojoji sun yi artabu da ’yan ta’addan ne bayan sun shafe sa’o’i hudu suna...
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa. Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ta’addanci: Ana Fuskantar Ƙarancin Man Fetur A Mali Sakamakon Datse Hanyoyin Shiga Bamako October 13, 2025 Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin...
Wani soja mai muƙamin Las Kofur ya ɗirka wa matarsa harbi har lahira sannan ya kashe kansa a Jihar Neja. Las Kofur Akenleye Femi da ke aiki a Bataliya ta 221, ya yi wannan aika-aika ne a Barikin Sojoji na Wawa da ke Ƙaramar Hukumar Borgu a Jihar Neja. Muƙaddashin Daraktan Hulda da Jama’a na Rundunar Soja ta 22 da ke Ilorin, Kyaftin Stephen Nwankwo, ne ya tabbatar da lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce abin ya faru ne a ranar 11 ga Oktoba, 2025. Ya ce mutuwar sojan da matarsa ta haifar da tashin hankali a cikin sansanin soja, inda mazauna wurin suka shiga ɗimuwa da mamaki kan abin da zai iya jawo irin wannan...
An kammala kada ƙuri’a da yammacin Lahadi a zaɓen shugaban ƙasa na Kamaru, inda shugaban ƙasa mai shekaru 92, Paul Biya — wanda shi ne tsohon shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya — yake neman wa’adi na takwas a mulki. Biya, wanda ya shafe shekaru 43 yana mulkin ƙasar, ya fafata da ’yan takara 11, ciki har da tsoffin muƙarrabansa. Ɗaya daga cikinsu shi ne Issa Tchiroma Bakary, tsohon ministan ma’aikata wanda ya yi murabus daga gwamnati a watan Yuni bayan fiye da shekaru 20 yana aiki tare da Biya. Bakary, mai shekaru 79, ya zama babban abokin hamayyar Biya bayan Kotun Tsarin Mulki ta ƙi amincewa da takarar fitaccen ɗan adawa Maurice Kamto — matakin da ƙungiyoyin kare haƙƙin...
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan yadda shugaba Bola Tinubu ya yi wa wasu mutane afuwa, ciki har da waɗanda suka aikata manyan laifuka. A cikin saƙon da Atiku ya wallafa a shafinsa na X, ya ce ana yin afuwa ne ga waɗanda aka yi wa rashin adalci ko waɗanda suka nema gafara bayan sun shafe wani lokaci a gidan yari. Yajin Aikin ASUU: Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna Ya ce a wannan karon an yi wa masu safarar ƙwayoyi, masu garkuwa da mutane, masu kisan kai, da kuma masu cin hanci da rashawa afuwa. Atiku,...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Tinubu Ya Isa Birnin Rome Don Halartar Taron Tsaro Na Aqaba October 12, 2025 Manyan Labarai An Sauya Kwamishinan Ƴansandan Abuja Saboda Rashin Tsaro October 12, 2025 Tsaro Sojoji Sun Kashe Kwamandan IPOB ‘Alhaji’, Da Wasu 26, Sun Kama 22 October 12, 2025
Gwamnatin Tarayya, ta gargaɗi Ƙungiyar Malaman Kami’o’i ta Ƙasa (ASUU), cewa za ta aiwatar da dokar “babu aiki, babu albashi” idan malaman suka ci gaba da yajin aikin da ka iya zai kawo cikas ga harkokin karatu. A wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar da yammacin ranar Lahadi, Ministan Ilimi, Maruf Tunji Alausa, da Ƙaramar Ministan Ilimi, Suwaiba Sa’id Ahmed, sun ce gwamnati tana da niyyar magance ƙorafe-ƙorafen ASUU ta hanyar tattaunawa cikin lumana. Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja “Gwamnati ta nuna gaskiya, haƙuri da kyakkyawar niyya a tattaunawarta da ƙungiyar,” in ji sanarwar. Ministocin sun bayyana cewa yawancin buƙatun ASUU, kamar ƙarin kuɗin...
Sufeton ƴansanda na Ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, ya maye gurbin Kwamishinan ƴansandan birnin tarayya, CP Ajao Adewale, sakamakon ƙaruwar matsalolin tsaro a Abuja. Wannan mataki ya biyo bayan matsin lamba da yake fuskanta saboda rashin gamsuwa da aikinsa tun bayan karɓar ragama daga CP Benneth Igwe. Majiyoyi daga cikin rundunar sun bayyana cewa sauya shi ya shafi yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a Abuja, musamman bayan harin fashi da makami da ya yi sanadin mutuwar mai gabatar da shirye-shiryen gidan talabijin ɗin ARISE, Somtochukwu Maduagwu, da mai gadi Barnabas Danlami, a Katampe, ranar 29 ga Satumba, 2025. Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna NAFDAC Ta Rufe Manyan Shaguna 2 Na...
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Sharhi:...
Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da ta danganta da na karya da Amurka ke yi wa kasar cewa ta na da hannu a yakin da ake yi a Ukraine, tana mai daukar wadannan zarge-zarge a matsayin wani makirci na siyasa da nuna kiyayya. A cewar ma’aikatar harkokin wajen Cuba, hukumomi “ba su da wani takamaiman bayani kan ‘yan kasar Cuba” da suka shiga ko kuma suke shiga cikin rikicin “da kansu” a cikin “dakarun sojan bangarorin biyu da ke rikici da juna” tsakanin Rasha da Ukraine. Tsakanin shekarar 2023 zuwa 2025, kotunan kasar Cuba sun saurari kararrakin laifuka tara da suka shafi ayyukan sojan haya, inda suka yanke wa wadanda ake tuhuma 26 hukuncin zaman gidan yari tsakanin...
Sai dai duk da cewa Ousmane Dembele na kungiyar kwallon kafa ta PSG ne ya lashe gasar- Yamal ya samu nasarar kyautar gwarzon matashin dan wasa na Ballon d’Or karo na biyu a jere. Lamine Yamal, ya kasance daya daga cikin fitattun ‘yanwasa mafiya farin jini tsakanin masoya kwallon kafa, musamman ma matasa saboda karancin shekarunsa da kuma yadda yake buga wasa cikin raha. Shekara da shekaru, duniya ta dauka cewa zama fitacce a fagen kwallon kafa na bukatar jajircewa da sadaukarwa. Saboda kafin dan wasa ya iya lashe wannan kyauta sai ya yi aiki tukuru. Sai dai duk da nuna kuruciyarsa, hakan bai hana Yamal cimma burinsa a fagen kwallon kafa ba. A baya ya bayyana...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5. An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje. ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda. Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa. Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya...
Kasashe hudu da suka fi kokari a cikin wadanda suka kare a mataki na hudu za su fafata wasannin raba-gardama, sai wadanda suka samu nasara su sake raba-gardama da wasu kasashen na waje. A yanzu daI manyan kasashen nahiyar ta Afirka irin su Kamaru da Nijeriya suke fuskantar barazanar rasa gurbi, duk da haka suna da wasu damarmakin da idan suka yi sa’a za su iya tsintar kansu a gasar a badi. Kasar Masar ta wuce Burkina Faso da maki biyar, sannan idan ta samu nasara a kan Djibouti shikenan ta samu tikiti. Ita kuma kasar Djibouti tana can karshen teburi ne, domin maki daya tak take da shi a wasa takwas da ta buga. Idan ma...
A zahiri, zamanin da kasashen yammacin duniya ke ba da umarni ga kasashe masu tasowa ya riga ya wuce. An taba bin tsare-tsaren da kasashen yamma suka tanada, amma ba a samu nasarar da aka sa ran samu ba, wannan sakamako ya sa kasashe masu tasowa daina amincewa da huldar kasa da kasa da kasashen yamma suka tsara. Sai dai, ko wace irin sabuwar dangantakar sassan kasa da kasa muke bukata a zamanin yau? A matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, kasar Sin ta sha yin kira da a kafa sabon nau’in huldar kasa da kasa bisa tushen mutunta juna, da adalci, da hadin gwiwa don tabbatar da moriyar juna. Wannan tunani shi ma ya bayyana sarai...
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU), ta sanar da fara yajin aikin gargaɗi na tsawon mako biyu a dukkanin jami’o’in gwamnati da ke Najeriya. Shugaban ASUU, Farfesa Chris Piwuna ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja. Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Ya ce yajin aikin zai fara ne da tsakar daren ranar Litinin, 13 ga watan Oktoba, 2025. ASUU, ta riga ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 14 wanda ya ƙare a ranar 28 ga watan Satumba, 2025. A cewar Farfesa Piwuna, babu wani abu da aka yi don dakatar da...
Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya sauke Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, Ajao Adewale, daga muƙaminsa. Ko da yake ba a bayyana cikakken dalilin da ya sa aka sauke shi ba, majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa hakan ya faru ne sakamakon yadda rundunar Abuja, ta tafiyar da lamarin sanya gilishin mota mai duhu da kuma mutuwar ’yar jaridar gidan talabijin na Arise News. Tinubu ya tafi Rome don halartar taro kan sha’anin tsaro Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ɗaya daga cikin majiyoyin ta bayyana cewa waɗannan matsalolin guda biyu ne suka janyo sauya masa wajen aiki. Ta ƙara da cewa za a tura Adewale wani waje daban, inda za a...
Wata kungiya mai zaman kanta ta tantance mutane 60 wadanda za’a yiwa aikin ido kyauta a wasu kananan hukumomi 2 dake jihar Jigawa. Shugaban kungiyar mai zaman kanta, Alhaji Umar Saidu Yelleman Jambola ya bayyana cewar za’a gudanar da aikin ne kyauta ga mutane 60 a kananan hukumomin Malam madori da kaugama. A cewar sa wadanda za su ci moriyar aikin an zabi su ne daga dukkanin mazabu da ke kananan hukumomin. Sa’idu Yalleman ya kara da cewa yara da manya ne za su amfana da aikin idon kyauta wanda kungiyar ta dau nauyi. Da yake jawabi ga manema labarai, Dr Abubakar Adamu yace wadanda aka tantance kuma suke da yanar ido za’a kai su asibitin...
Irabor ya ce, littafin nasa na ƙoƙarin kawo tarihin “tasirin Boko Haram a Nijeriya ta fannoni daban-daban” da kuma “hakikanin gaskiya a kan Boko Haram, wanda na samo a lokacin ina matsayin kwamandan soji na yankin Arewa maso Gabashin Nijeriya.” Tsohon babban hafsan tsaron ya ce, babban abinda ya fi tayar da hankali a yaki da Boko Haram shi ne yawan rayukan da aka rasa. A cewarsa, “irin rayukan mutanen da aka kashe a rikicin Boko Haram yana da yawa kuma ana iya kwatanta shi da annoba.” ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamna Sani Ya Gana Da Ministan Ayyuka Domin Ganin An Kammala Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna October 12, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Yi...
Daga cikin wadanda shugaban kasar ta Nigeria ya yi wa afuwa da kawai Maryam Sanda ‘yar shekaru 37 wacce aka yankewa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunta da kashe mijinta da wuka a 2017. Mai Magana da yawun shugaban kasa Bayo Onangua ya saki bayanin afuwar da shugaban kasar ya yi, wacce kuma ta hadad a Faruka Lawan tsohon dan majalisa da aka samu da laifin cin hanci da rashawa a 2021. Sai kuma Ken Saro-wiwa wanda dan fafutuka ne mai rajin kare muhalli a yankin Ogoni da aka zartarwa hukuncin kisa a 1995. Har ila yau afuwar ta shugaba Tunibu ta shafi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka zartarwa da hukuncin kisa a 1986 saboda juyin Mulki....
Gwamna Uba Sani ya jaddada cewa wannan titin ba na yankin Arewa kadai ba ne, ya bayyana shi a matsayin jijiyar ƙasa da ƙasa ne wadda ke haɗa yankuna daban-daban tare da ƙarfafa haɗin kai da bunƙasar tattalin arziki. Ya kara da cewa titin Abuja- Kaduna da Kano na ɗaya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin Manufar Sabon Fata na (Renewed Hope Agenda), wadda ke nufin sabunta manyan gine-ginen ƙasa da inganta tattalin arziki. Yace “Wannan titi ba hanya ce kawai ba inda yace wata hanya ce ta tattalin arziki wadda ke haɗa mutane, kasuwanni, da dama a fadin Arewacin Nijeriya da ma bayan haka,” A nasa jawabin, Sanata Umahi ya yaba...
Ba abin mamaki ba ne cewa tsaro shi ne babban ƙalubalen da jihar Zamfara ta daɗe tana fama da shi. Daga Maradun zuwa Shinkafi, daga Anka zuwa Zurmi, matsalar ‘yan bindiga ta yi ƙatutu na tsawon shekaru. Da yake karɓar mulki, Gwamna Dauda Lawal ya sanar da cewa “ba za a iya gina tattalin arziki ba idan tsoro ya mamaye ƙasa.” Tun daga farkon watannin mulkinsa, ya kafa Kwamitin Tsaro na Musamman, wanda ke haɗa jami’an soja, ‘yan sanda, NSCDC da ‘yan sa-kai. Gwamnatin ta samar da motocin sintiri sama da 500, da kayan aikin zamani ga jami’an tsaro. Har ila yau, an kafa Command and Control Centre a Gusau domin sa ido kan al’amuran tsaro...
Al’ummomin dake garin Warwade da kewaye a karamar hukumar Dutse ta jihar Jigawa sun yi kira ga gwamnatin jihar da ta yashe madatsar ruwa ta Warwade wanda ta kasance daya daga cikin hanyar samun aikin dogaro da kai ga Mazauna yankin. Wakilinmu Usman Mohammed Zaria ya ziyarci al’ummomin da ke zaune a kusa da mmadatsr ruwan wanda aka gina ta sama da shekaru hamsin da suka gabata. Madatsar ruwan ta Warwade ta kasance hanyar samun sana’o’in dogaro da kai ga mazauna yankin, wadanda suke kamun kifi da noman rani domin samun na yau da kullum. Malam Umar Sani, wanda masunci ne a Warwade, yace da abin da yake samu daga kamun kifi yake kula da iyalan shi da kuma sauran...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello. Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa. Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye. Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta samu nasarar ceto mutum 10 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su tsawon watanni huɗu da suka gabata a Ƙaramar Hukumar Kagarko. A cikin sanarwar da kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka ceto har da yara masu shekaru ɗaya, uku da kuma 13. Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro DSP Mansir, ya ce ’yan bindigar sun kai farmaki ƙauyen Kushe Makaranta, inda suka sace mutanen daga gidajensu sannan suka kai su dajin da ke kusa da Rijana. Rundunar, ta ce aikin ceto mutanen ya samu ne ta haɗin gwiwar...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello. Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa. Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye. Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya...
Bayanan da suka fito daga kasar Indunusiya sun nuna cewa gwammnatin kasar ta ki bada visa ga tawagar wasan jiminastik din HKI da aka shirya za’a yi wasa a birnin Jakarta a wannan watan, domin nuna rashin amincewa da kisan kare dangi da HKI ke yi a yankin Gaza. Wannan matakin yana kara nuna irin yadda batun kisan kiyanshin gaza yayi tasiri sosai hatta a harkar wasanni, kasar dake da yawan musulmi tana aikewa da sako na siyasa ne ta hanyar takawa yan wasan isra’ila birki, da kuma neman goyon bayan duniya ga alummar falasdinu. An tsara cewa tawagar wasan Jemanastik din HKI ta za shiga gasar jiminastik na duniya da za’a yi a Jakarta daga ranar 19-25 ga wannan...
Shugabannin masana’antu sun kuma yi kira ga gwamnati da ta daidaita tattalin arziki, inganta saukin gudanar da harkokin kasuwanci, da aiwatar da shirye-shiryen tallafi ga masana’antu na cikin gida. Bugu da kari, masana sun nuna cewa rikicin kudin waje da rashin daidaito a kimar musayar kudi su ne manyan matsaloli ga kamfanoni masu zaman kansu daga kasashen waje, inda kalubalen samun damar mayar da ribar kamfani zuwa kasashen waje da samun kudin waje ke rage amincewar masu zuba jari sosai kuma yana karfafa su su bar kasar. Binciken da LEADERSHIP Sunday ta gudanar ya nuna cewa yanayin tattalin arzikin Nijeriya ya sha wahala tun daga shekarar 2020, inda wasu kamfanoni suka rufe ayyukansu, ko suka yi kaura, ko...
Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayar da kyautar motoci ƙirar Hilux guda shida da babura 30 domin taimaka wa sojoji wajen yaƙi da ’yan bindiga a faɗin jihar. Gwamnan, ya miƙa motocin da baburan ga Kanal Hussaini Rabi’u Toro na rundunar sojoji ta takwas a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi. ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Ya ce wannan kyauta na cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da walwalar al’umma. “Tsaro shi ne babban abin da gwamnatina ta mayar da hankali a kai. Ba za mu yi wasa da harkar tsaro ba. “Za mu ci gaba da tallafa wa jami’an...
Baya ga Maryam Sanda, Shugaba Tinubu ya kuma yafe wa wasu mutane da dama, ciki har da Janar Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, da Faruku Lawan, wanda tsohon ɗan majalisar tarayya ne daga Jihar Kano. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025
Li ya ce kasar Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga jam’iyyar WPK, don ta bayar da jagoranci ga al’ummun kasar Koriya ta Arewa, wajen neman ci gaba bisa halin da kasar take ciki. A sa’i daya kuma, kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, kamar aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, tare da kara musayar manyan jami’ai, da mu’amala kan manyan tsare-tsare, ta yadda za a inganta fahimtar siyasa a tsakanin kasashen biyu, tare da cimma sakamako mai kyau bisa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Koriya ta Arewa. (Mai Fassara: Maryam Yang) ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Ma’aikatar Wajen...
Rahotanni sun tabbatar da rasuwar wasu sojoji huɗu, bayan ’yan ta’adda sun kai hari yankin Ngamdu na Jihar Borno. Jihar Borno ta daɗe tana fama da hare-haren ta’addanci, musamman daga ƙungiyar Boko Haram. Sojoji sun hallaka ’yan ta’adda 5 a Borno An yi jana’izar sojojin da ’yan bindiga suka kashe a Kebbi Ko da yake wasu mazauna yankin sun ce sojoji 10 ne suka mutu, sai dai mai magana da yawun rundunar Operation Haɗin Kai, Laftanar Kanar Sani Uba, bai tabbatar da hakan ba cikin sanarwar ya fitar a ranar Juma’a. Amma rahotanni sun bayyana cewa sojoji huɗu ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata a yayin harin. A cewar Kanar Sani, ’yan ta’addan sun yi amfani da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP October 11, 2025 Siyasa Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025 Labarai Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas October 2, 2025
Tukur Muhammad Fakum, daya daga cikin jagororin al’ummar ya shaida wa BBC cewa an riga an kai makura, don haka a yanzu fatan su kawai bai wuce neman wa kai mafita ba. Ya ce ”Mu yanzu muna nan muna gangami, mai ‘yar karamar gona ya sayar, mai dan karamin gida ya sayar, in muka sayi bindigogi a ba matasa su ma su yi kokari su kare mu. ”Gwamnati ta ba mu kariya, idan kuma ba ta iyawa to ta bamu makamai a ba matasa, su matasa na iya kare rayukansu da garuruwan su,” in ji Tukur Muhammad Fakum. Dangane da halin da irin barnar da ‘yan bindigar suka yi masu kuwa, Tukur Muhammad Fakum ya ce ”Babu dai...
Rundunar sojin Najeriya, ta bayyana cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar a wani samame da suka kai yankin Magumeri da Gajiram, a Jihar Borno. Kakakin rundunar Operation Haɗin Kai, Kanar Sani Uba, ya ce dakarun sun yi arangama da wasu ’yan ta’adda 24 da ke tafe a ƙafa a ranar Juma’a. Mutane 2 sun rasu a rikicin manoma da makiyaya a Kebbi Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina A cewar sanarwar da ya fitar, sojojin sun yi nasarar kashe biyar daga cikinsu tare da ƙwato kuɗi Naira miliyan biyar. “An hangi ’yan ta’addan suna ƙone gidaje da kuma kai wa mutane hari, sai dakarun suka fara bin su, inda suka tsere zuwa ƙauyen Damjiyakiri,”...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Ƴansanda Sun Ceto Mutane Uku Da Aka Sace A Kano October 10, 2025 Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025
Ya bayyana cewa an riga an hada wadanda aka ceto da iyalansu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike da aikin ceton domin gano wadanda suka aikata laifin da kuma kubutar da sauran wadanda ake tsare da su, idan suna nan. A halin da ake ciki kuma, kwamandan Runduna ta 6 ta Sojan Nijeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya yaba da saurin daukar mataki da hadin kai tsakanin sojoji da ‘yansanda wanda ya kai ga nasarar aikin ceton. Ya sake jaddada kudirin rundunar wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Jihar Taraba. Sai dai, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bai wa sojoji da sauran hukumomin tsaro goyon baya ta hanyar...
Mataimakin shugaban kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, batun kifar da gwamnatin JMI bayan yakin kwanaki 12 ya kuma fita daga abinda makiya zasu iya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar yanakalto mataimakin shugaban kasa na farko yana fadar haka a ranar Alhamis da ta gabata, ya kuma kara da cewa a cikin yakin kwanaki 12 wanda kasashen Amurka da HKI suka dorawa kasar sun so su kifar da gwamnatin JMI a cikin kwanaki 3 zuwa 4 amma suka kasa. Ya ce hatta babban sakataren MDD Antonio Guterres ya tabbatar da haka a wata tattaunawa da shi dangane daha. Ya kuma tabbatar da cewa makiyan JMI ba zasu iya tumbuke tsarin ba. Yasashen yamma musamman Amurka suna kokarin...
Masu zanga-zanga a nan Iran a jiya jumma’a a manya-manyan garuruwan kasar bayan sallar Jumma’a sun bayyana goyon bayansu ga al-ummar Falasdinu a Gaza, sannan sun bukaci HKI ta aiwatar da yarjeniyar da ta cimma da kungiyoyi masu gwagwarmaya. Har’ila yau sun bukaci a gaggauta shigo da abinci da magungunacikin zirin Gaza. Tashar talabijin talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto masu zanga zangar wadanda suka hada da mata da maza, malaman addini, daliban jami’o’i da sauransu suna tattaki daga dandalin inkilab zuwa dandalin azadi. Har’ila yau sun rera wakoki na goyon bayan masu gwagwarmayar, dauke da hotunan shahidai da kuma shuwagabannin kawancen masu gwagwarmaya a yankin. An gudanar da jerin gwanon a cikin manya manyan biranen...
Aƙalla mutane biyu ne suka mutu a rikicin da ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a unguwar Dambo, wani kauye da ke da tazarar ’yan kilomita daga Birnin Kebbi, babban birnin Jihar Kebbi. Wani mazaunin yankin mai suna Ɗanladi Usman ya ce rikicin ya fara ne bayan an kashe wani mutum mai suna Sule yayin da yake aiki a gonarsa. “Kashe Sule ya tayar da hankulan al’umma, inda manoma suka ɗauki fansa suka kashe wani makiyayi da har yanzu ba a gano sunansa ba,” in ji shi. Ya ƙara da cewa makiyayan sun sha faɗa da manoma a kwanakin baya bayan sun aike musu da sako cewa su hanzarta girbe amfanin gonakinsu domin za su riƙa wucewa da shanunsu ta...
Wadanda suka amfana da horon, an ba su horon ne a fannoni daban-daban da suka hada da yin noma da takin gargajiya da kuma yin noman kayan lambu da sauransu. Kajin gidan gona da tare da kuma tallafa masu da kayan aikin noma. Bisa tsarin wannan haron, kowace mace daya da ta amfana da horon, an ba su tallafin Naira Naira 50,000. Kazalika, Adeleke ya danganta wannan tallafin kudin a matsayin mayar da hankalin gwamnatinsa na taimaka wa matan jihar. Gwamnan ya kuma jaddada muhimmcin tallafa wa mata, wanda ya sanar da cewa; hakan na da muhimanci domin inganta gobensu. Shi kuma shugaban gidauniyar, Dakta Deji Adeleke a nasa jawabin ya bayyana cewa, shirin wanda...
A cewarta, shirin ya taimaka wajen noman shinkafa da ta kai kimanin tan 99,452, wacce kuma kudinta ya kai kimanin Naira biliyan 13.527 tare kuma da noman rogo da ya kai kimanin tan 87,237, wanda kudinsa ya kai Naira biliyan 3.925, musamman domin a kara samar da wadataccen abinci da kuma kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar. Sai dai, ta bayyana cewa; har yanzu a jihar ba a samar da wani cikakken tsari a hukumance ba, a kan tsarin na shirin na CAF wanda hakan ke haifar wa da shirin koma baya a jihar. Ta yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki a fannin bunkasa aikin noma, domin samun riba a jihar da su bayar da hadin...
Duk da Najeriya na cikin yanayin damina, wanda ake ganin a lokacin ta fi samar da wutar lantarki ga ’yan ƙasarta, amma jama’a a jihohin Kaduna da Kano na ci gaba da kokawa kan ƙarancin wutar. A duk shekara jama’a na more wutar lantarki a Nijeriya a lokacin damina saboda tashoshin ruwa na samar da wutar lantarki suna aiki da cikakken ƙarfinsu. Amma, wasu masana a ɓangaren wutar sun shaida wa wakilinmu cewa duk da matsalolin masu nasaba da lalata kayan aiki da kuma ƙin biyan kuɗin wuta da wasu masu amfani da ita ke yi, kamfanonin rarraba wutar (DisCos) suna yin iya bakin ƙoƙarinsu wajen cike giɓin. Masu ruwa da tsaki sun bayyana cewa ana ƙoƙarin daidaita rarraba wuta...

Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya
Kasar Venezuela ta yi kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya da ya tabbatar da cewa Amurka tana yin barazana zaman lafiyar duniya Kasar Venezuela ta yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince cewa; Lallai Amurka tana yin barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa, saboda yadda sojojin Amurka suke shisshigi a tekun Caribbean, wannan batu ya zo ne a yayin zaman gaggawa na majalisar a jiya Juma’a. Wakilin dindindin na Venezuela a Majalisar Dinkin Duniya, Samuel Moncada, ya ce: “Suna ba da shawarar ayyuka uku ga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya: Na farko, amincewa da barazanar zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa da sojojin Amurka suka haifar a cikin...
Ministar wadda ta je kamfanin domin daukar sabuwar motarta ta alfarma kirar Nord Demir SUB da kamfanin ya hada nataimakin Shugaban jami’ar na sashen kula da ilimi da gudanar da bincike Farfesa Bola Oboh da kuma Shugaban kamfanin Mista Oluwatobi Ajayi ne, suka karbi bakuncinta. A jawabin da ta gabatar a lokacin ziyarar ministar ta bayyana cewa,Duba da yarjejeniyar hada-hadar kasuwanci wajen fitar da kaya zuwa ketare kamfanin zai iya yin amfani da wannan samar waken fitar da motocinsa zuwa ketare. Ta kara da cewa, Nijeriya na da gurare biyu ne da ake hada motoci da suka hada da, na wannan jami’ar da kuma na EPs, inda ta yi nuni da cewa, karfin da kamfanin ya ke da...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa October 10, 2025 Daga Birnin Sin Sin Za Ta Fara Cajin Kudi Na Musamman Ga Jiragen Ruwan Amurka October 10, 2025 Daga Birnin Sin Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata October 10, 2025
Hukumar Tsaro ta Sibil Difens a Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a Ƙaramar Hukumar Doguwa. Hukumar ta miƙa su ga Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), domin ci gaba da bincike da gurfanar da su a kotu. ’Yan bindiga sun kashe Civilian JTF 8 a Zamfara Sojoji sun mutu yayin da Boko Haram ta kai hari sansanin soji a Borno Kwamandan hukumar na Jihar Kano, Bala Bawa Bodinga ne, ya bayyana hakan yayin da yake magana da ’yan jarida a hedikwatar hukumar a ranar Juma’a. Ya ce an kama mutanen ne da sanyin safiyar ranar Talata, 7 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihin bayaai. Jami’an hukumar daga...
“Ta yaya Jonathan zai zama barazana? Mun doke shi a baya lokacin da PDP take kan mulki. “Idan mutum yana ganin cewa PDP ita ce kololuwar jam’iyya a Nijeriya, kuma ya sha kaye a lokacin da yake ganiyarsa, ina ganin sai makiyinsa ne kawai zai tilasta masa ya kara tsayawa takara a zaben 2027,” in ji shi. Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce a yanzu haka Jonathan ya kasance dan siyasa mai daraja, yana mai cewa komawa fagen siyasa na iya rage masa kima da kuma zubar masa da darajar da yake da shi a idon duniya. Ya jaddada cewa Jonathan ya samu damar nuna cewa mulki bai tsole masa ido ba, domin haka ne...

Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba. Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar. Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin...
Wani Likitan ƙwaƙwalwa a Asibitin Neuropsychiatric Aro, a Abeokuta, Jihar Ogun, Dokta Emmanuel Abayomi ya ce kimanin mutane miliyan 60 ne ke fama da taɓin hankali a halin yanzu. Ya yi wannan jawabin ne a ranar Juma’a a Abeokuta a wajen wani taron ƙarawa juna sani da Ƙungiyar likitoci ta NAS ƙarƙashin Ƙungiyar masu ruwa da tsaki ta ƙasa ta shirya domin tunawa da ranar kiwon lafiyar ƙwaƙwalwa ta duniya ta bana. Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Shirin da Ash Montana Deck tare da haɗin gwiwar Atlantis, Americana 1 da Longhorn Deck suka yi wanda ya ja hankalin ‘yan sanda da...
A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka. Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa. ’Yan sanda sun ceto mutum 3 da aka sace a Kano da Kaduna Kwastam ta kama buhunan lalatacciyar fulawa 10,000 ana ƙoƙarin shigo da ita Najeriya Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar...
Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar. “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem. A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki. “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta samu nasarar ceto wasu mutum uku da aka sace, bayan wani samame da ta kai a jihohin Kano da Kaduna. Wannan na daga cikin ƙoƙarin da rundunar ke yi domin yaƙi da laifuka da tabbatar da tsaron jama’a. ’Yan sanda sun manta hularsu a motar dalibi bayan karɓar ‘cin hancin’ N99,000 NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya bayyana cewa an gudanar da samamen ne tsakanin ranar 7 zuwa 9 ga watan Oktoba, 2025, bisa umarnin Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori. A cewar Kiyawa, samamen farko ya gudana ne a ranar...
“Akwai da yawa malamai marasa cancanta a cikin aikin. Muna da wadanda ke koyarwa a ajujuwa amma ba su da takardun shaidar koyarwa, musamman a makarantu masu zaman kansu,” in ji ta. Ta bayyana cewa, yayin da wasu mutane ke da sha’awar koyarwa da gaske, rashin horo na hukuma ya hana su shiga aikin koyarwa. Dr. Soyombo ta bayyana cewa TRCN a halin yanzu na da malamai masu rijista kusan miliyan 1.4, tare da shirin kara wannan adadi zuwa miliyan 20 cikin shekaru biyu masu zuwa ta hanyar dijital da saurin rajista. “Mun zamanantar da tsarinmu domin mutane da yawa su sami damar yin rijista,” in ji ta. “Kowane malami yana da bai wa ta musamman...
Hukumar Kwastam shiyyar bodar Najeriya ta Seme da ke jihar Legas ta ce ta cafke motoci biyar da ke maƙare da buhuna 10,000 na lalatacciyar fulawa da darajarsu ta kai Naira biliyan 1.2. Rundunar ta kuma ce ta tara jimillar kuɗin shigar da ya kai Naira biliyan daya da rabi a watan Satumba, wanda hakan ya nuna kari da kaso 182 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira miliyan 531 da aka tara a watan Agustan da ya gabata. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Gaban Sabon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Kwamandan rundunar a shiyyar, Wale Adenuga, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai na...
Kazalika, tarihin Dimokiradiyyar kasar ya sha cin karo da kwam gaba kwam baya kusan za a iya cewa, tun bayan dawowar mulkin Demokaradiyya a 1979 da kuma sake dora kasar a wata turbar ta Demokiradiyyar a 1999. Alal misali, jamhuriyya ta hudu ta kasance ta jima sosai, amma kusan babu wasu ayyukan na inganta rayuwar ‘yan kasar da za a bigi Kirji a ce gasu an gani a kasar a zahiri. Idan aka dubi bangaren samar da hasken wutar lantarki kusan za a iya cewa, karni da dama da suka bace, har zuwa yau Nijeriya ta gaza samar da karfin wutar da kuma rabar da ita da ta kai karfin Megawatts 5,000 musamman duba da cewa, wannan adadin...
Rahotanni daga Gaza na cewa Isra’ila ta fara janye sojojinta daga wasu yankuna na zirin Gaza. Wannan dai na zuwa ne bayan da gwamantin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta dake kunshe a shirin zaman lafiya na Trump da ta cimma da kungiyar Hamas. Daraktan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa da Hadin Kan Kasa da Kasa ta Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Gaza Mohammad Al-Moughayyir, ya ce sojojin Isra’ila sun janye daga yankuna da dama a cikin birnin Gaza da arewacin zirin da kuma wasu yankunan kudancin yankin. A Khan Younis da ke kudancin zirin Gaza, Motocin Isra’ila sun janye daga kudancin birnin da tsakiyar birnin zuwa yankunan gabashi. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of...
Cibiyar Kula da Harkokin kasuwanci ta kasa ta bayyana kafa Cibiyar Gudanar da taron Kasuwanci na Najeriya a wani bangare na ganin ba a samarda cibiyoyi da ke da aiki iri ɗaya ba. Babban magatakardar Cibiyar Mista Victor Olannye, ne ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da takardar a yayin taron jin ra’ayin jama’a na kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kasuwanci a Abuja. Mista Victor Olannye ya ce kudurin dokar da ke neman kafa sabuwar cibiyar ya ci karo da ayyukan Cibiyar Gudanarwa ta kasa da tuni Majalisar Tarayya ta 9 ta amince da ita wadda Shugaban kasar na wancan lokacin ya amince da shi. Ya yi nuni da cewa, babban makasudin kafa Cibiyar Kula...
Yawan mace-mace ta hanyar cutar kwalarar, na faruwa ne duk da biliyoyin Nairori da aka ce gwamnati da abokan huldar kasa da kasa suna kashewa, domin kokarin ganin an dakile ta. Wadannan kudade sun hada da kason kasafin kudi na shekara-shekara, wanda ya kunshi miliyoyin Nairori; akwai dala miliyan 700 da bankin duniya ya bayar domin samar da tsaftataccen ruwa sha, tsaftar muhalli a fadin kasa baki-daya, tallafin dala miliyan 2 daga Majalisar Dinkin Duniya, dubban daruruwan allurar rigakafin cutar kwalara da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka bayar da sauran makamantansu. Alkaluman da aka samu daga cibiyar NCDC, sun nuna cewa a cikin 2020, kasar ta samu rahoton...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama mutum 26 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne tare da kwato makamai da kudade daga hannunsu. Daga cikin abubuwan da aka samu nasarar kwatowar har da bindigogi na gida guda huɗu, makamai masu hatsari da kuma tsabar kuɗi Naira 546,000 da ake zargin wani ɓangare ne na kuɗin fansa. Tinubu ya yi wa Mamman Vatsa, Farouk Lawan da wasu mutum 173 afuwa Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC An kama waɗanda ake zargin ne a cikin jerin samame da aka gudanar daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, a sassa daban-daban na jihar. Samamen ya haɗa jami’ai daga sashen ’yan sanda na Anchau, Hukumar Kula da Tsaro...
Dare ya jaddada cewa Nijeriya kasa ce mai addinai da dama, wacce aka gina bisa juriya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin mabambantan addinai, al’ummomin da ya ce Tinubu ya shugabanta. Dare ya ambaci maganar Shugaban Kasa inda ya jaddada cewa Nijeriya “kasa ce mai cikakken ‘yanci da girma, wadda aka gina bisa bangaskiya da juriyar jama’arta,” ya kara da cewa “Babu wani addini da ake zalunta, kuma babu wata al’umma da aka ware.” Yana nuna misali da rayuwar Shugaban Kasa a matsayin shaida ta juriya da fahimtar addinai, Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu, Musulmi ne da yake auren fasto mai bin addinin Kirista. Ya kuma ruwaito Shugaban yana cewa, “Gaba da kiyayya ba su da gurbi...
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci dukkanin bangarorin da su yi aiki da kuma mutunta yarjejeniyar da shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da kuma yin amfani da wannan damar. Da yake jawabi a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya, Guterres ya bayyana cewa, “Ina kira ga dukkan bangarorin da su mutunta ka’idojin yarjejeniyar, da kuma rungumar damar da tke cikinta.” Duk da cewa dai a cikin kalaman nasa yafi nuna damuwa a kan fursunonin Isra’ila da ake tsare da su a Gaza, duk da irin mummunan kisan kiyashi da Isra’ila take yi a Gaza, amma mya ce Majalisar Dinkin Duniya ta shirya tsaf domin ba da cikakken goyon bayanta ga aiwatar da yarjejeniyar. A halin da...
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwar Shugaban Kasa ga mutane 175. Daga ciki har da wadanda aka yi wa afuwar bayan mutuwa ga marigayi Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa da ɗan gwagwarmayar kwato ’yancin kan Najeriya, Herbert Macaulay. An dauki wannan mataki ne bayan amincewa da shawarwarin da Majalisar Tsofaffin Shugabannin Ƙasa ta bayar a taronta da aka gudanar a ranar Alhamis a Abuja. Gwamnatin Kano ta shirya ɗaurin auren ma’aurata 2,000 Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC A cewar sanarwar da mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin bayanai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma yi afuwa ga tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan da wasu mutum uku, Misis Anastasia...

An Yi Tafiye-tafiye Miliyan 16.34 Da Suka Shafi Shiga Da Fita Daga Kasar Sin Yayin Hutun Kwanaki 8 Na Kasar
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Duniya Ta Kara Ganin Bunkasuwar Sin a Lokacin Hutun Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar October 9, 2025 Daga Birnin Sin An Samu Karuwar Sayayya Yayin Hutun Bikin Kafuwar Kasar Sin October 9, 2025 Daga Birnin Sin Adadin Biyan Kudade Ta Intanet Yayin Hutun Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin Ya Kai Yuan Tiriliyan 13.26 October 9, 2025
Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
A bana, bikin Tsakiyar Kaka da Ranar Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Sin sun hadu, inda suka haifar da hutun tsawon kwanaki takwas. An yi hasashen cewa, adadin mutanen da suka yi tafiya a yankuna daban daban na kasar zai kai biliyan 2.432, tare da karuwar kashi 6.2% a kowace rana idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Adadin ribar da aka samu a manyan kantuna da gidajen abinci a cikin kwanaki hudu na farkon hutun ta karu da kashi 3.3% idan aka kwatanta da na bara, kuma har zuwa karfe 4:00 na yammacin ranar 8 ga watan, kudin shiga da aka samu daga kallon fina-finai yayin wannan biki ya wuce RMB Yuan biliyan 1.8 kwatankwacin fiye da dala miliyan 252....
Rahotanni sun bayyana cewa, karar mai lamba FHC/OS/194/2024, ta nemi umarnin tilastawa INEC da shugabanta na lokacin da su sanya sunayen wasu jami’an Jam’iyyar AA a shafin hukumar na yanar gizo bayan an cire su. Sai dai Udeze ya ci gaba da cewa, babu irin wannan hukunci ko umarnin kama shi (Yakubu), yana mai tabbatar da cewa, rahotannin ƙage ne kawai. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC October 9, 2025 Labarai SSANU Da NASU Sun Yi Zanga-Zanga A Abuja Kan Rashin Cika Alƙawarin Gwamnati October 9, 2025 Labarai An Umurci Manyan Makarantu Su Mayar Da Kuɗaɗen TETFund Da Ba Su Kashe Ba October 9, 2025
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta kama wasu mutane 26 da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ƙwato bindigogi guda 4, da muggan makamai da dama. Ta kuma kama wani ɓangare na kuɗin fansa da ake zargin an biya masu garkuwa da mutane a wasu hari daban-daban a jihar. Nasarar kamen dai ya biyo bayan wasu jerin samame da jami’an ’yan sanda da na ’yan banga suka yi a tsakanin ranakun 3 zuwa 5 ga watan Oktoban 2025, inda suka yi ta kai farmaki kan gungun masu garkuwa da mutane da ke kai hari a ƙananan hukumomin Anchau, Ikara da kuma Makarfi. Tinubu ya naɗa Amupitan a matsayin Shugaban INEC Ma’aikatan jami’a sun yi zanga-zanga a Jami’ar...
Shugaban ƙaramar hukumar Oredo, Hon. Gabriel Iduseri, ya ziyarci kasuwar da safiyar ranar Alhamis.Yayin ziyararsa, Iduseri, ya bayyana lamarin a matsayin babban iftila’i ga ‘yan kasuwa, tare da alƙawarin cewa za su ba su tallafi.“Wannan lokaci ne na matuƙar baƙin ciki ga mutanenmu, musamman ma ‘yan kasuwar da suka dogara da wannan waje don samun abincin yau da kullum. Ba za mu bar su su fuskanci wannan asara su kaɗai ba,” in ji shi.ShareTweetSendShareMASU ALAKA SiyasaNi Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu October 9, 2025Manyan LabaraiTattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya October 9, 2025Manyan LabaraiTinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A...
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi, za su fuskanci martani mai tsanani Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi a mashigar tekun Farisa, da mashigar Hormuz da tsibirin Iran, za su fuskanci hukunci mai tsauri, nan take, murkushewa, da kuma nadama. A cikin sakon taya murnar zagayowar ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Pakpour ya bayyana cewa: “A jajibirin ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, yana mika sakon taya murna ga babban matsayi na kwamandoji da mayakan da suka yi...
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kaddamar da sabuwar cibiyar taro ta Ahmadu Bello da aka gina a Bauchi, inda ya bayyana ta a matsayin alamar ci gaba a gwamnatin Gwamna Bala Mohammed. Da yake jawabi a wajen taron, Obasanjo ya jaddada muhimmancin dunkulewar duniya, inda ya ce babu wata al’umma da za ta iya rayuwa a ware ba tare da yin hulda mai ma’ana da sauran kasashen duniya ba. Ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed bisa ayyukan raya kasa, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa, wanda a cewarsa hakan zai karawa Bauchi damar karbar bakuncin taron kasa da kasa da kuma jawo hankalin masu zuba jari. Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa irin wadannan...
An shawarci mata a karamar hukumar Kirikasamma da ke jihar jigawa da su kawo ‘ya’yansu domin yi musu rigakafin cutar shan inna, kyanda, da Gaida da sauran cututtuka masu ban tsoro. Uwargidan Shugaban Karamar Hukumar, Hajiya Fatima Maji Marma ta ba da wannan shawarar a lokacin kaddamar da shirin rigakafin cutar kyanda da na rigakafi na yau da kullum a fadar Hakimin Marma. Ta kuma jaddada aniyar karamar hukumar na bayar da tallafin da ake bukata domin samun nasarar gudanar da aikin rigakafin. Hajiya Fatima ta kuma yabawa gwamnatin jihar Jigawa bisa bullo da inshorar lafiya ga marasa galihu a matakin unguwanni a kananan hukumomin jihar 27. A nasa jawabin manajan hukumar kula da lafiya matakin...
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana shirinta na yin hadin gwiwa da kungiyar injiniyoyin ma’adanai ta Najeriya a matakin jiha da tarayya domin tabbatar da aiwatar da kudurorin da aka cimma a karshen taron kasa da kasa karo na ashirin da hudu. Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake bayyana bude taron shekara-shekara da taron kasa da kasa na shekara ashirin da hudu da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja. Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata Injiniya Idris Abubakar ya bayyana cewa hakan ya zama dole domin dorewa da aikin hakar ma’adanai na da matukar muhimmanci wajen kare shirin makamashi maras illa a matsayin Jigon gwamnatin sa. A nasa...
Gwamna AbdulRazaq ya yabawa Shugaba Tinubu yayin da Sojoji suka tura cikakken birgediya domin fatattakar masu garkuwa da mutane daga dazukan Kwara. Hedkwatar sojojin Najeriya ta aika da cikakken birgediya da manyan kayan aiki a sassa daban-daban na Kwara ta Kudu, domin rage matsalolin tsaro a yankin. Wata sanarwa da sakataren yada labarai gwamnan, Rafiu Ajakaye ya fitar ta ce Tuni dai sojojin suka yi ta luguden wuta ta cikin kauyukan Oke Ode da Babanla, dukkansu a karamar hukumar Ifelodun. Har ila yau, rundunar ta kara da cewa, aikin ya zarce zuwa Edu da Patigi domin ratsa dazuzzukan da masu garkuwa da mutane suka fara kai hare-hare na matsorata a kan al’ummomi daban-daban tare da yin...
Majalisar Wakilai, ta yi watsi da zargin da Ƙasar Amurka, ta yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Wannan martani na zuwa ne bayan wani Sanatan na Amurka, Ted Cruz, ya gabatar da ƙudirin doka a Majalisar Dattawan ƙasar, inda ya ce ana yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya. Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin Duniya Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya A yayin gabatar da ƙudirin ya buƙaci a ƙaƙaba wa wasu jami’an Najeriya takunkumi. Cruz ya ce: “ Ana kashe Kiristocin Najeriya saboda addininsu… lokaci ya yi da za a ɗauki mataki na gaske kan jami’an Najeriya da ke taimaka wa...
Cristiano Ronaldo ya zama biloniya na farko tsakanin ƴan wasan kwallon kafa a duniya Bloomberg mai sharhi da kididdiga tarin dukiya tsakanin attajiran duniya, ta fayyace tarin kudin da mai shekara 40 dan kwallon tawagar Portugal mai taka leda a Al-Nassr ta Saudiya ke da shi. Ta ce yana da dalar Amurka biliyan daya da miliyan 400 daga kudin da yake samu na albashi da ladan wasa da tallace-tallace da zuba hannun jari. Ya samu albashin sama da dalar Amurka miliyan 550 tsakanin 2002 zuwa 2023 da kwantiragin da ya kai dalar Amurka miliya 18. Lokacin da Ronaldo ya koma Al-Nassr ta Saudiyya a 2022, ya zama wanda ke kan gaba da ake biya albashi mafi tsoka a tarihi. da...
Bankin Duniya ya ce har yanzu talauci na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya duk da sauye-sauyen tattalin arziƙi da Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin daidaita tattalin arziƙin ƙasar. A wajen ƙaddamar da rahoton ci gaban da aka samu a Abuja, Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Verghis, ya bayyana cewa aƙalla mutum miliyan 139 ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci a shekarar 2025. Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙaryata rahoton Bankin Duniya kan yawan talakawa a Najeriya NAJERIYA A YAU: Abin Da Dokar Kasa Ta Ce Kan Nada Shugaban Hukumar Zabe Ya ce duk da cewa tattalin arziƙin Najeriya ya ɗan bunƙasa, kuma gwamnati tana samun ƙarin kuɗaɗen shiga, yawancin jama’a har yanzu na fama da tsadar...
Fadar Shugaban Ƙasa ta yi fatali da sabon rahoton tattalin arziki da Bankin Duniya ya fitar, wanda ya kiyasta cewa mutane miliyan 139 na rayuwa cikin talauci. Fadar ta bayyana adadin a matsayin wanda ya saba da zahiri kuma ya kauce wa hakikanin halin tattalin arzikin ƙasar. SSANU da NASU za su yi wa gwamnati zanga-zanga kan rashin cika musu alƙawari 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu Mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana a shafinsa na X a ranar Laraba cewa dole ne a rahoton bai duba yanayin tsarin auna talauci na duniya ba. “Duk da cewa Najeriya na daraja...
Ƙungiyar Ma’aikatan Manyan Makarantun Najeriya (SSANU) da Ƙungiyar Ma’aikatan Ilimi (NASU), sun shirya gudanar da zanga-zangar gargaɗi ta rana ɗaya a yau Alhamis saboda Gwamnatin Tarayya ta gaza cika musu alƙawuran da ta ɗauka. Ƙungiyoyin, ƙarƙashin jagoranci Joint Action Committee (JAC), sun gudanar da taron gaggawa a ranar Laraba don shirya zanga-zangar. 2027: Atiku, Jonathan da Obi ba za su iya kayar da Tinubu ba — Kalu ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Sun ce za su gudanar da tattaki a cikin jami’o’i, tare da ɗaukar kwalaye masu rubuce-rubuce, sannan za su yi wa manema labarai jawabi domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu. Sun zargi gwamnati da rashin adalci wajen rabon Naira biliyan 50 na alawus-alawus, ƙin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A tsarin mulkin Najeriya, an bai wa Shugaban Ƙasa ikon naɗa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) tare da sauran mambobinta. Wannan iko yana daga cikin muhimman nauyukan da ke hannun shugaban ƙasa domin tabbatar da cewa ana gudanar da zaɓe cikin tsari, gaskiya da adalci. Sai dai, kafin wanda shugaban ƙasa ya naɗa ya fara aiki, dole ne a nemi amincewar Majalisar Dattawa, domin tabbatar da cewa wanda aka zaɓa ya cancanci rike wannan muhimmiyar kujera. Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa hukumar zaɓe ta kasance mai zaman kanta, ba ta karkata ga wani ɓangare na siyasa ba, kuma tana iya gudanar da aikinta cikin gaskiya...
Kakakin majalisar wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada buƙatar ɗaukar ƙwararan matakai na kafa tsarin ‘yansandan jihohi a kasar nan domin magance kalubalen tsaro da ake fuskanta.Abbas ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin dokar hukumar leken asiri da binciken sirri ta shekarar 2024, wanda kwamitin majalisar kan harkokin tsaro da leken asiri ya shirya a harabar majalisar dokokin kasar da ke Abuja ranar Laraba.Kakakin majalisar wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazabar Ilorin ta Yamma/Asa, Honarabul Muktar Shagaya, ya ce, kawo sauye-sauye a fannin tsaro ya zama abinda aka fi mayar da hankali, kuma yanzu dole a tashi daga rubutu kawai zuwa aiwatar da cikakken tsari.Shugaban majalisar ya ce kafa ‘yansandan jihohi ta...
An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato. Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba. ’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo. Ya ce ’yan bindigar sun buɗe...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru. Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai. Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa. Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe. An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata...
ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, sun tare hanyar Gusau zuwa Gummi a Jihar Zamfara, inda suka sace mutane da dama. Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun tare motoci sannan suka yi awon gava da fasinjojin da ke ciki. Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a Bauchi Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Wani shaida ya ce ’yan bindigar sun ɗauki lokaci suna sharafinsu kafin daga bisani suka tafi da mutanen da suka kama. Daga cikin waɗanda suka sace akwai Malam Sadis Isa, shugaban Majalisar Malamai ta Ƙaramar Hukumar Gummi, abin da ya jefa al’umma cikin tsoro da damuwa. “Da yammacin ranar Talata, ’yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ƙaddamar da sabon ginin Cibiyar Taron Ƙasa da Ƙasa, wadda aka sanya wa sunan Sir Ahmadu Bello a Jihar Bauchi. An ƙaddamar da cibiyar ne kafin babban taron zuba jari da nufin bunkasa kasuwanci da masana’antu a jihar. Ban yi murabus don ina da laifi ba — Nnaji Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERC A jawabinsa, Obasanjo ya yaba wa Gwamna Bala Mohammed, bisa irin ayyukan raya ƙasa da yake aiwatarwa, waɗanda ke inganta rayuwar jama’a. “Na yi farin ciki da abin da na gani da kuma abin da na ji. Ban zata cewa zan dawo Bauchi cikin ƙanƙanin lokaci don buɗe irin wannan katafaren waje...
Hukumar da ke Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) ta ce kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 sun tara Naira biliyan 546.71 daga hannun abokan cinikinsu a cikin zango na biyu na shekarar 2025. Sai dai hukumar ta ce wannan adadi bai kai kaso 60 cikin 100 na wutar da aka tura musu daga babbar hanyar rarraba wuta ba, sakamakon matsalolin lissafin wutar da suka karɓa da kuma yadda aka raba wutar ga rukunan abokan ciniki daban-daban. Zulum ya ba ma’aikaciyar lafiya ’yar kabilar Igbo kyautar gida, ya ba danta aiki Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Hakan, a cewar hukumar, ya haifar da gibin biyan kuɗi na naira biliyan 167.25. kazalika, NERC ta ce...
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bai wa wata ma’aikaciyar lafiya ’yar ƙabilar Igbo kuma ‘yar asalin jihar Anambra, Marbel Ijeoma Duaka, kyautar gida mai dakuna biyu. Gwamnan ya kuma ba ɗan ma’aikaciyar aikin yi na dinidindin saboda jajircewarta da sadaukarwa wajen hidimtawa jihar na sama da shekara 20. Matar aure mai ’ya’ya huɗu ta rataye kanta a Jigawa Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin rabon gidaje 72 ga malamai da ma’aikatan lafiya a ƙaramar hukumar Mafa. Zulum ya ce Marbel ta shafe fiye da shekaru 24 tana aiki a cibiyar kula da lafiya ta matakin farko da ke Mafa, kuma ba ta taɓa barin wurin ba ko...
“Yanzu muna kammala sabbin sharuɗan aikin da ASUU ta gabatar, kuma za mu bayyana amsar gwamnati nan ba da jimawa ba,” in ji shi.“Shugaba Tinubu yana da niyyar kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”Ya roƙi ASUU da ta ci gaba da tattaunawa maimakon fara yajin aiki, yana mai tabbatar da cewa gwamnati na da niyyar gaskiya da jajircewa wajen warware matsalar.LEADERSHIP ta ruwaito cewa ASUU ta fara shirin tursasa wa mambobinta fara yajin aikin gargadi, yayin da wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati zai ƙare a ranar Lahadi mai zuwa.ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan LabaraiBoko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung October 8, 2025Labarai‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato...
Al’umma a kauyen Sumore da ke Ƙaramar Hukumar Dutse a Jihar Jigawa sun shiga cikin alhini bayan mutuwar wata mata mai shekaru 30, Adama Hannafi, wacce ake zargin ta rataye kanta. Lamarin, wanda ya faru a ranar Talata, ya tayar da hankulan mazauna kan ƙalubalen da ke tattare da rashin lafiyar kwakwalwa a cikin al’umma, musamman a yankunan karkara. ‘Akwai ɗaliban da ke yin digiri yanzu ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ba saboda AI’ Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Lawan Shi’isu Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an samu gawar matar a rataye a jikin wata bishiya a kauyen. “Mun samu kiran...
Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI. Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba. Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC “Muna da daliban da ke yin rajista...
Ya buƙaci jama’a suke bambanta “gaskiya da siyasa.”ShareTweetSendShareMASU ALAKA Manyan Labarai‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio October 8, 2025Manyan LabaraiDa Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo October 7, 2025Manyan LabaraiYa Kamata Nijeriya Ta Ayyana Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda — Tsohon Hafsan Sojin Ƙasa October 7, 2025
Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata daina samar da magungunan da take yi ta hanyar fasahar makamashin nukiliya ba Kakakin Kwamitin Tsaro da Harkokin Waje na Majalisar Shawarar Musulunci (wato Majalisar Dokoki) Ibrahim Reza’ei, ya tabbatar da cewa ana ci gaba da samar da magungunan ta hanyar fasahar makamashin nukiliya a Iran, kuma ba a taba dainawa ba, kuma za a ci gaba da gudanarwa. Reza’i ya bayyana cewa: Kwamitin tsaron kasar ya gudanar da zaman hadin gwiwa tare da shugaban hukumar makamashin nukiliya ta Iran (AEOI), Mohammad Eslami, da wasu jami’an kungiyar. Islami ya gabatar da wani rahoto kan ci gaban da aka samu a fannin makamashin nukiliya, da hasarar da aka samu...