Za a birne Aminu Ɗantata a Madina – Iyalansa
Published: 28th, June 2025 GMT
Iyalan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu, sun bayyana cewa ya bar wasiyyar cewa a birne shi a Birnin Madina na ƙasar Saudiyya.
Majiyoyi daga cikin iyalansa sun bayyana cewa marigayin ya buƙaci a birne shi kusa da uwargidansa a Madina a duk lokacin da ya rasu.
Mangu: Gwamnatin Filato ba ta aiko da wakilai don yin ta’aziyya ba — Sarkin Zazzau ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’A gefe guda kuma, Majalisar Malamai ta Jihar Kano ta yi wa marigayin sallar Ga’ib a Masallacin Aliyu bin Abu Talib da ke unguwar Dangi.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, majalisar ta bayyana cewa za a yi masa sallar ne duk d gawarsa na Birnin Dubai, na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
An gudanar da sallar a cikin birnin Kano, da misalin ƙarfe 2 na rana.
Sanarwar ta buƙaci al’umma da su halarta domin yin sallar da kuma yi wa marigayin addu’o’i.
Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94 bayan fama da rashin lafiya.
Ya rasu yana da ’ya’ya bakwai da jikoki da dama.
Babban sakatarensa, Mustapha Abdullahi Junaid, ne ya sanar da rasuwar a safiyar Asabar.
Ɗaya daga cikin attajirai mafiya arziƙi a Nahiyar Afirka, ya rasu ne a ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE.)
Alhaji Aminu Ɗantata shi ne mai kamfanin mai na Express Petroleum & Gas, kuma a matsayin uba yake ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Ɗangote.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗantata Rashin lafiya rasuwa Saudiyya Aminu Ɗantata
এছাড়াও পড়ুন:
Me Ya Sa Jaruman Masana’antar Kannywood Ke Auren Sirri?
Haka zalika, sun ki bayyana takamaiman wajen da za a daura auren, har sai bayan an kammala, inda suka bayyana yin hakan a matsayin wata hanya ta kawar da cece-kuce daga al’umma.
Kazalika a ‘yan watannin da suka gabata kuma, an sake daura auren jaruma a masana’antar Kannywood, Rahama Sadau tare da angonta Ibrahim Garba, a wani biki wanda za a iya kira da na sirri da aka gudanar a birnin Kaduna, daura auren shahararriyar jarumar Kannywood din, Rahma Sadau da mijinta Ibrahim Garba, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya yi matukar bai wa mutane mamaki, duba da cewa; kafin daurin auren babu wata alama ko sanarwa da aka fitar daga makusantan mijin ko matar.
An yi bikin da safe, a Masallacin Atiku Auwal da ke Unguwar Rimi, inda ‘yan’uwa da abokan arziki suka halarta, Rahma yayin da take magana da manema labarai ta bayyana cewa; ta zabi yin bikin cikin natsuwa ne, domin kauce wa hayaniya, bayan labarin ya bayyana a kafafen sada zumunta, ta tabbatar da daura auren nata.
Rahma ta shahara a fina-finan Kannywood da kuma wasu daga cikin fina-finan Nollywood, bayan da aka daura auren, masoyanta da abokan aikinta, suka tura mata sakwannin taya murna daga sassa daban-daban na Nijeriya, wannan aure ya zo ne watanni kadan bayan rasuwar mahaifinta, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Haka yasa ake saka alamar tambaya a kan jaruman masana’antar ta Kannywood, a kan cewa; me ya sa suke daura aurensu a sirrance? Yayin da wasu ke ganin yin hakan a matsayin wata hanya ce da jaruman ke bi wajen kauce wa bakin mutane, wasu kuma na ganin wannan a matsayin wata hanya ta nuna girman kai ko isa da jaruman ke bi, domin nuna wa duniya cewa; su ba kamar sauran al’umma ba ne.
Koma dai mene ne, akwai bukatar jaruman su tuna cewa; suna da dimbin mutane da ke kiran kansu a matsayin masoyan jaruman, wanda ko babu komai dai, bai dace a ce masoyinka ba shi da labarin wani abin alherin da ya same ka ba, musamman harka ta aure, wadda ka iya zama silar daina fitowa a fina-finai ga jarumai mata da mazajensu, ba su amince su ci gaba da harkar fim ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA