Aminiya:
2025-10-13@17:10:07 GMT

APC ta sa ranar taron Majalisar Zartarwa bayan murabus ɗin Ganduje

Published: 30th, June 2025 GMT

Jam’iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tsayar da 24 ga watan Yulin bana a matsayin ranar da za ta gudanar da taronta na Majalisar Zartarwa.

Mataimakin Sakataren jam’iyyar, Barista Fetus Fuanter ne ya tabbatar wa manema labarai hakan a yau Litinin a Abuja.

Magidanci ya kashe matarsa da adda a Yobe Jami’an tsaro sun hana taron kwamitin amintattun PDP

Fuanter ya ce kusoshin jam’iyyar za su gana kafin gudanar da taron Majalisar Zartarwar.

Taron da za a gudanar shi ne na biyu ta fuskar girma a cikin jerin tarukan da jam’iyya ke zaman yanke shawara da daukar wasu muhimman matakai bayan babban taronta na kasa.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba cece-kuce tun bayan murabus ɗin shugaban jam’iyyar na ƙasa ya yi a makon jiya.

A makon da ya gabata ne shugaban jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar, Abdullahi Ganduje, ya ajiye mulki a wani abu da masana ke cewa na da alaƙa da lisaafin da manyan ’yan siyasar ke yi gabanin Zaɓen 2027.

APC ta ce tuni Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci Ali Bukar Dalori ya maye gurbin Ganduje a matsayin shugaba na riƙo kafin kwamatin zaɓaɓɓu su gana game da batun.

Jami’in yaɗa labarai na APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa babban dalilin da Ganduje ya bayar game da murabus ɗin nasa shi ne batun ƙoshin lafiyarsa.

Sai dai wata majiya daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Ganduje ya ajiye muƙamin ne bayan da fadar shugaban ta umarce shi da yin hakan.

Da ma tun lokacin aka bai wa Ganduje shugabancin jam’iyyar wasu ‘yan jam’iyyar, musamman daga yankin Arewa maso Gabas, suka riƙa gunaguni cewa su ya kamata a bai wa.

Zuwa yanzu babu tabbas game da wanda fadar shugaban ke son ya karɓi shugabancin jam’iyyar.

Daga cikin waɗanda ake raɗe-raɗin za su maye gurbin Ganduje akwai tsohon Gwamnan Nasarawa, Umar Tanko Al-Makura da Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Abdullahi Umar Ganduje Majalisar Zartarwa

এছাড়াও পড়ুন:

An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe

An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya.

Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse.

Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben.

Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka wajen samun nasarar shirin.

Ya lura cewar akwai abin damuwa bisa karancin fitowa wajen karbar katin zabe a Arewa, idan an kwatanta da alkaluman karbar katin zaben a ikko da sauran jihohin kudu maso kudu da kudu maso gabashin kasar nan duk da cewar Arewa ta fi yawan jama’a.

Magaji Da’u Aliyu ya ce yana da cikakken bayani kan gudummawar da shugabannin kananan hukumomin Birnin Kudu da Buji su ke bayarwa ga aikin bada Katin Zabe amma duk da haka akwai bukatar rubanya kokari domin cimma gagarumar nasara.

Daga nan sai ya yi kira ga matasan da su ka cika shekarun yin zabe da wadanda su ka canja wurin zama da wadanda katin zaben su ya lalace ko ya bata, da su je domin sake karbar wani katin zaben.

A cewar sa, yin haka shine zai basu damar zaben dan takarar da ya kwanta musu a rai ko kuma fidda baragurbin ‘yan siyasa daga madafun iko.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
  • Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh
  • An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe
  • Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza a Masar ranar Litinin  
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Ka Tattauna Batun Falasdinu
  • Sin Ta Mayar Da Martani Game Da Takunkumin Da Amurka Ta Sanyawa Masana’antunta 
  • An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
  • Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya