NAJERIYA A YAU: Halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ambaliya
Published: 1st, July 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Tun bayan da ambaliyar ruwa ya ci wasu sassan garin Mokwa al’ummar yankin suka faɗa halin neman taimako.
Duk da cewa Gwamnatin Tarayya da wasu ɗaiɗakun mutane sun tallafa wa waɗanda abin ya shafa da kuɗi da ma wasu abubuwa, amma mazauna yankin suna bayyana rashin jin daɗinsu bisa yadda al’amura ke gudana a garin.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya yi nazari ne a kan halin da al’ummar Mokwa ke ciki wata guda bayan ibtila’in ambaliyar.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Mokwa
এছাড়াও পড়ুন:
Har Yanzu Ba Mu San Inda Za A Binne Dantata Ba — Sakatarensa
Mustapha ya ce idan lokaci ya ƙure kuma ba a samu amincewa daga Madina ba, za su dawo da gawar zuwa Kano domin a yi masa sutura.
Don haka, har yanzu ba su yanke shawarar ainihin inda za a binne shi ba.
Alhaji Aminu Alhassan Ɗantata ya rasu yana da shekaru 94, kuma mutane da dama sun aike da saƙon ta’aziyyarsu, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Alhaji Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso da wasu shugabanni da dama.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp