HausaTv:
2025-08-13@13:30:09 GMT

 Iran: Babu Wani Alfanu A Ci Gaba Da Bai Wa IAEA Hadin Kai

Published: 29th, June 2025 GMT

 Kwamitin koli na  tsaron kasa a cikin majalisar shawawar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; Saboda yadda hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa ( IAEA) take ci gaba da siyasarta na nuna wariya, ci gaba da aiki da ita ba shi da wani alfanu a wurin Iran.

 Shugaban kwamitin tsaron kasar a majalisar shawarar musulunci ta Iran Ibrahim Azizi ya bayyana cewa; Karkataccen rahoton da hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya gabatar ne ya zama abinda HKI ta fake da shi wajen kawo wa Iran hari na ta’addanci.

Azizi ya kara da cewa; Iran ta sha nanata cewa, shirinta na Nukiliya na zaman lafiya ne, kuma yana gudana ne a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya.

Ibrahim Azizi ya kuma kara da  cewa; A lokuta da dama Iran ta karbi bakuncin shugaban hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa Grossy, ya kuma ziyarci cibiyoyin makamashin Nukiliya; amma wannan hukumar ta daina aiki da ilimi da kwarewa ta koma abin wasa a hannun manyan kasashe.

Haka nan kuma ya ce; Saboda yadda hukumar ta koma aiki da siyasar nuna wa Iran wariya, ci gaba da yin aiki da ita ba shi da wani alfanu ga Iran.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

 

Lokacin da bukatun Afirka suka hadu da karfin Sin, muna da dalilin yin imani cewa, tare da tallafin dandalolin kamar su “dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC)” da shawarar “ziri daya da hanya daya”, hadin gwiwar AI tsakanin Sin da Afirka tabbas za ta samar da samako mai armashi nan gaba. (Mai zane da rubutu: MINA)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu Ya Nada Hukumar Gudanarwa Ta NCC Da Sauran su
  • Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
  • Sin Ta Gabatar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Taron Tattalin Arziki Da Cinikayya Tsakaninta Da Amurka A Stockholm
  • Fasahohin AI Sun Bude Sabon Babi Na Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
  • Tinubu Ya Sake Nada Dankaka A Matsayin Shugaban Hukumar Kula Da Da’ar Ma’aikata Ta Kasa
  • Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
  • Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Makoma Mai Haske In Ji Wani Kwararre 
  • Jiragen Saman NAF Sun Kai Hari Kan Taron ‘Yan Bindiga 400 A Zamfara
  • Iran: Babu wani abu da aka yanke game da tattaunawa da Washington
  • Ko Maƙiyina Ba Na Yi Masa Fatan Tsintar Kansa A Halin Da Na Samu Kaina – Ummi Nuhu