Iran: An Kama Wani Dan Leken Asirin “Mosad” A Tehran A Jiya Lahadi
Published: 30th, June 2025 GMT
‘Yan sandan Tehran sun sanar da kama wani dan leken asirin kungiyar leken asirin Isra’ila ta “Mosad” a cikin daya daga tasoshin jiragen kasa na birnin Tehran.
Dan leken asirin wanda aka watsa furucin da ya yi, ya bayyana cewa aikinsa shi ne kera jiragen sama marasa matuki da kuma ‘yan kananan jirage, a yammacin Tehran bisa umarnin wadanda su ka dauke shi aiki masu alaka da Mosad.
Haka nan kuma ya ce, ya tattara bayanai akan wasu muhimman wurare da cibiyoyi,musamman wadanda su ka shafi yadda naurorin kariyar samaniyar saman Iran suke aiki, tare da aikewa da su zuwa kasashen waje.
Majiyar ‘yan sandan ta ce, an kama mutumin ne bayan da aka dade ana bin diddiginsa da kuma tantance ayyukan da yake yi,da hakan ya taimaka wajen dakile wasu hare-hare.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Kama Hakimi Kan Zargin Yi Wa ‘Yar Shekara 12 Fyaɗe A Gombe
An ce ya amsa cewa an aikata fashi da makami sau biyu da shi, kuma yanzu hakan ana shari’arsu a kotun jihar Gombe.
An miƙa shi tare da kayan da aka gano ga Sashen Yaƙi da Tashin Hankali domin ƙara gudanar da bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp