Sojoji Sun Kashe Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda Yellow Danbokolo A Zamfara
Published: 1st, July 2025 GMT
Ya samu munanan raunuka a harin da aka kai masa, wanda daga baya ya mutu.
Janar Kangye ya ƙara da cewa Danbokolo ya fi Bello Turji tsabibanci, shi ne ya jagoranci harin watan Disamban 2021 a ƙaramar hukumar Shinkafi ta Jihar Zamfara, inda ya ƙone fasinjoji da ransu a cikin mota.
Hakazalika, ya bayyana cewa Danbokolo na amfani da wata ƙwaya mai suna ‘pentazocine’ domin ci gaba da aikata miyagun laifuka.
Yanzu haka, sojojin Operation FASAN YAMA suna ci gaba da neman Bello Turji wanda ya ɓuya.
Janar Kangye ya tabbatar da cewa rundunar sojin Nijeriya tana da ƙwarin gwiwar samar da zaman lafiya a dukkanin sassan ƙasar nan.
Ya kuma roƙi haɗin kan ‘yan Nijeriya don cimma wannan buri.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 a Borno
Hedikwatar Tsaron Nijeriya (DHQ) ta ce dakarun tsaro na rundunar “Operation Hadin kai” sun kashe mayaƙan Boko Haram 10 yayin wata arangama a yankin Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno.
Daraktan watsa labarai na hedikwatar tsaron, Manjo Janar Markus Kangye ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Gwamnan Bauchi zai ƙirƙiro sabbin masarautu Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a MadinaManjo Janar Markus Kangye ya ce aikin kawar da ‘yan ta’addan da aka aiwatar ranar Litinin ya faru ne bayan rundunar ta lashi takobin kawar da sauran ‘yan Boko Haram/ISWAP da ke ɓuya a yankin Tafkin Chadi.
“Arangamar ta faru ne a lokacin wani aiki na haɗaka wanda aka shirya kuma aka aiwatar cikin dabara domin kawar da sauran ‘yan ta’addan Boko Haram/ISAWP da ke aika-aika a garuruwan da ke kan iyaka,” in ji Janar Kangye.
“Dakaraun da suka yi aiki bisa bayanan sirri sun danna cikin maɓuyar mayaƙan tsakanin Rann da Gamboru, inda suka yi ba-ta-kashi sannan suka kashe ‘yan ta’adda 10,” in ji sanarwar.
Ya ƙara da cewa bayan arangamar an samu makamai da yawa daga wurin, ciki har da bindigogin harbo jiragen sama.
Aikin wani ɓangare ne na dabarun karɓe iko da kudancin Tafkin Chadi da kuma hana zirga-zirgar ‘yan Boko Haram ta kan iyaka, a cewarsa.
“Ana nazari kan makaman da aka ƙwace yayin da ake ƙoƙarin gano waɗanda suka tsere da kuma sauran maɓoyar ’yan ta’adda a yankin,” in ji sanarwar.
Ya ƙara da cewa dakarun sojin Nijeriya, da haɗin gwiwar rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF da kuma sauran jami’an tsaro sun zafafa ayyukansu a yankin Tafkin Chadi da sauran ɓangarori na arewacin Borno domin kakkaɓe sauran ‘yan Boko Haram a yankin