Mata Ku Kula Da Masu Tallan Maganin Hana Kishiya
Published: 28th, June 2025 GMT
Mafi akasarin matan da suke irin wannan tallace-tallacen magungunan zawarawa ne, shin ita ba ta yi amfani da maganin bane ta mallake mijinta ta kasa fita daga gidan miji?.
Mu kiyaye, kuma mu ji taoron Allah, ke da aka kawo wa tallan maganin ki sani babu wani magani da zai sa ki mallake mijinki, tamkar ladabi da biyayya, da bin umarnin Allah subhanahu wa ta’ala.
Kuma masu yaho suna sayar da magungunan kuna cewa maganin mallake miji ko a hana kishiya shigowa a ji tsoron Allah, ku sani idan mata ne ku kun girma kun haifa ‘ya’yanku za su yi aure a wani gidan, idan ma baku haifa ba to, ku sani kannenku ko ‘yan’uwanku za su yi aure a wani gidan, abin da ka je ka yi wa ‘yar wani ka hana ta zaman gidan miji to, kai ma tana nan kamar sako ne ka bayar.
Idan wata matsala ki ke ciki tsakaninki da mijinki ina mai baki shawara addu’a ita ce maganin komai, domin garkuwa ce kuma takobi ce ga mumini, ba wani abu da addu’a ba za ta yanka shi ba, babu wani abu da addu’a ba za ta kare ka da shi ba.
Ki yi addu’a ki gayawa Allah (s.w), ki samu mijinki ke da shi ku yi magana da shi, ko shaidan ne mijinki idan ki ka kwantar da kai, ki ka yarda shi uba ne a gare ki, ki ka yi masa biyayya, ki ka yi masa ladabi, ki ka bi ta sanyin murya ki ka yi masa magana, in wani abu ne za ku sasanta tsakaninku, ba sai an tayaki da maganin mallakar miji ba.
Maganin mallakar miji har sai an baki labari?, ubangiji Allah ya zaunar da matan mu lafiya, da kannenmu da yayyenmu dukkaninsu Allah ya kara musu lafiya, wadanda ba su da miji ubangiji Allah ya mallaka musu, zawarawan ma da suke yaho suke irin wadanan barnace-barnacen son kai, da son zuciya da neman kudi, ubangiji Allah ya basu miji nagari kuma Allah ya shirye su.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari
Jami’an tsaron kasar Iraki sun sanar da gano wata kungiyar ‘yan ta’adda da ta yi niyyar kai wa masu ziyarar Arbaeen hare-hare, wanda aka shirya gudanarwa a kwanaki masu zuwa.
Ma’aikatar tsaron ta bayyana cewa, “tsarin da ‘yan ta’addan ke da shi sun hada da dasa ababen fashewa a kan hanyoyin da masu tattaki ke bi a yankin kudancin kasar da kuma saka guba a cikin kayan abinci da ake ba wa masu tattaki.
Har ila yau, bincike ya nuna cewa kungiyar ta’addanci ta ISIS ta yi amfani da hanyoyi daban-daban wajen daukar wadannan mambobi nata da aka wanke wa kwakwalwa domin aiwatar da wadannan ayyuka.
Ma’aikatar ta bayyana cewa, kungiyar na yin hakan ne ta hanyar yin amfani littafai da aka rubuta musamman domin tunzura masu irin wannan Akida ta kafirta musulmi da zubar da jinni, tare da yin amfani da wasu malamai masu irin waannan Akida domin gurbata tunanin matasa musulmi, da kuma saka su hanyar ta’addanci da sunan addini ko jihadi.
A ranar alhamis din da ta gabata ma karamar hukumar Karbala ta sanar da kame wasu mutane 22 da suke Shirin kai hare-haren ta’addancin da suka tsara a lokacin tarukan ziyarar Arbaeen na wannan shekara.
Ko a shekarun baya an yi ta samun irin wadannan matsaloli na ta’addanci daga kungiyoyi masu dauke da akidar takfir da suke kafirta al’ummar musulmi tare da halasta jininsu, inda suke Kallon dukkanin musulmi da ba su a cikinsu a matsayin ‘yan bidi’a mushrikai ko kafirai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chadi: An Daure Wani Dan Adawa Shekaru 20 A Gidan Kaso Da tara August 10, 2025 Dangantaka Tsakanin Iran da Saudiya Yana Taimakawa Zaman Lafiya A yankin August 10, 2025 Iran Zata Hana Amurka Samar da Hanya A yankin Caucasus Ko Rasha Bata taimaka ba August 10, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare A Kan Garuruwa Da Dama A Yankin Quneitra Na Kasar Siriya August 10, 2025 An Zabi Alkalan Wasa Biyu Daga Kasar Iran Don Alkalanci A gasar Kwallon Kafa ta Mata August 10, 2025 Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12 August 10, 2025 Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar August 10, 2025 Jefa Agajin Abinci Ta Sama A Zirin Gaza Ya Janyo Shahadan Falasdinawa 23 Tare Da Jikkata Wasu 124 August 10, 2025 Tehran Times: Mai Yiwuwa Iran da Amurka su koma Tattaunawa August 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci