Magajin Garin Birnin Tehran Ya Karyata Da’awar ‘Yan Sahayoniyya
Published: 1st, July 2025 GMT
Magajin garin birnin Tehran ya bayyana cewa: Karyar ‘yan sahayoniyya ya tonu na cewa ba su kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran ba
Magajin garin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran Ali-Ridha Zakani ya tabbatar da cewa: Karairayi da ‘yan sahayoniyya suke yadawa dangane da rashin kai hare-hare kan fararen hula a yakin da suka kaddamar kan Iran a fili yake karara.
A cikin bayanansa, Zakani ya ce: Dalilai kan wadannan karairayi su ne kaburbura gawawwaki da suka hada da fili mai lamba ta 42 a makabartar Al-Jannar – Zahra da ke babban birnin Tehran. Ya bayyana cewa, duk wanda ya ga jerin sunayen wadanda suka yi shahada a lokacin yakin zai iya ganin karara irin karyar da ‘yan sahayoniyya suka shirga, kamar yadda kowa zai iya ganin gine-ginen da aka kai musu hare-hare a birnin Tehran.
Zakani ya kuma yi ishara da hare-haren baya- bayan nan da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya suka kai kan wuraren fararen hula da suka hada da cibiyoyin kiwon lafiya, inda ya kara da cewa, gwamnatin ‘yan sahayoniyya sun kai hare-hare kan motocin daukar marasa lafiya da asibitoci da ba su bukatar wata shaida wajen tabbatar da karairayin ‘yan sahayoniyya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan sahayoniyya birnin Tehran
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane A Fadin Duniya Sun Soki Ayyukan Neman ‘Yancin Kan Taiwan
Wasu jerin shirye-shiryen neman ‘yancin kan Taiwan da hukumomin yankin suka gudanar a baya bayan nan, sun sha suka sosai daga al’ummomin kasa da kasa. Wani nazari da kafar CGTN ta Sin ta gudanar ya nuna cewa adadin mai rinjaye na wadanda suka shiga nazarin, watau kimanin kaso 89.8 sun yi ammana cewa, manufar kasar Sin daya tak ta zama wata matsaya da kasashen duniya suka amince da ita, inda suka soki hukumomin yankin Taiwan bisa shirinsu na neman ‘yanci da takala.
Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne cikin harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Larabci da Rashanci, inda mutane 13,650 suka bayar da amsa cikin sa’o’i 24. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA