2025-08-08@00:18:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7519
«shekaru biyu»:
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, ya bayyana haka yayin mika kayan kayan abincin na musamman da aka sayo ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF a shirin Child Nutrition Match Fund, wanda aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya (PHC) ta Karamar Hukumar Takai. Mista Rahma, wanda Daraktan Lafiya na UNICEF, Dakta Serekeberehan Seyoum Deres ya wakilta, ya ce kashi 51.9 bisa 100 na yaran Kano suna fama da mat girma...
Kudirin gyaran dokar fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari. Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya yi bayanin cewar, daga cikin shugabanin da suka rike mukaman siyasa da ya kamata su amfana da irin wannan fansho sun hada da Gwamna da Mataimakan Gwamna da Shugaban Majalisar Dokoki da Kuma alfarmar da ya kamata su ci gaba da samu bayan sun bar mulki. Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar, ya gudanar da...
Sun kara da cewa,”A cikin wannan lokaci, mataimakin kyaftin na yanzu, Ronald Araujo ne zai karbi aikin kyaftin din, Ter Stegen ya buga wa Barcelona wasanni sama da 400 tun lokacin da ya koma kungiyar daga Borussia Monchengladbach a shekara ta 2014, ya lashe manyan kofuna da suka hada da gasar zakarun Turai da kuma gasar La Liga shida a kungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12. Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce karkashin wannan tallafi, iyalai da yaransu za su ci gajiyarsa za su samu ragin kashe kudaden makaranta da yawansu ya kai kusan yuan biliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.8. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar. Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa Sowore. Mahaifin Ɗan Bello ya rasu Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano “Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ya saba wa ka’ida. Dole ne a yi tur da lamarin,” in ji Atiku. Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin shugabanci nagari da ake yi a Nijeriya. Wasu rahotanni...
Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce kamar: “Muna bukatar zaman lafiya a kauyukan Kaura-Namoda,” “Gwamna Dauda Lawal da Matawalle ku kawo mana dauki”, “Ana kashe mu kowace rana,” da dai sauransu. Tsoffin Kansilolin APC Sun Yi Zanga-zangar Nesanta Kansu Da Maganganun Abdullahi Abbas Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Jihohin Makwabta, Ya Kara Ta’azzarar Rashin Tsaro A Neja – Bago Da yake jawabi a gidan gwamnati, jagoran masu...

Cinikayyar Kayayyaki a Kasar Sin Ta Karu Da Kashi 3.5 Cikin 100 Cikin Watanni 7 Na Farkon Shekarar Nan
Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara. Daga cikin adadin, darajar mizanin fitar da kayayyaki ya kai yuan tiriliyan 15.31, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.1, adadin da ya karu da kashi 7.3 cikin 100, yayin da mizanin shigo da kayayyaki shi ma ya kai yuan tiriliyan 10.39, kwatankwacin dalar Amurka triliya 1.44, adadin da ya ragu da kashi 1.6 cikin 100. A watan Yuli, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta...
Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 “Innalillahi wa inna IlaiHi rajiun. Allah Ya yi wa Mahaifin Dokta Bello Galadanchi (Dan Bello) rasuwa yanzun nan. Allah Ya gafarta masa. Ameen,” a cewar saƙon da Abba Hikima ya wallafa. Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin rasuwar mahaifin Ɗan Bellon ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa marigayi ya...
Bugu da kari, a baya bayan nan ma jaridar Financial Times, ta bayyana yadda a yanzu haka adadin hajojin da ake shigarwa Amurka daga sassan duniya daban daban suka ragu zuwa kaso 13 bisa dari, sabanin kaso kusan 20 bisa dari da kasar ke shigowa da su a tsawon shekaru 20 da suka gabata. Kamar dai yadda kimar Amurka ke raguwa sakamakon matsin lamba da take yiwa sauran sassan duniya abokan cinikayyarta, haka ma wadannan manufofi na kakaba haraji ke fuskantar turjiya, da kyama har daga abokan kasar makusanta. (Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Wasu daga cikin tsoffin kansilolin da suka halarci tattakin sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Abba Kabir Yusuf. A nasa jawabin, Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila ya ce, shi ma yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta hana hakkinsu, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! “Sun ga gwamna Abba zai jikanmu ne shi ne suke neman bata mana ruwa”. Tun da farko, shugaban tawagar, ya tabbatar da cewa, mai girma Gwamna ya amince zai biya su hakkokinsu wanda gwamnatin baya ta kasa biyansu, kuma yace baya bukatar sakamakon komai daga gare su wai don su koma jam’iyyarsa, ya yi ne domin Allah. A karshe dubban tsoffin kansillolin wanda suka yi tattaki dauke da...
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta bayyana Sadiq a matsayin jarumi, ƙwararre, kuma mai kishin kasa a fannin kafafen sada zumunta. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato Gwamna Abba ya ce mutuwar Sadiq Gentle ta girgiza shi sosai, inda ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai kamun kai, haƙuri, da sadaukarwa ga ci gaban Jihar Kano....
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya biya Naira dubu 800 kafin a bar mazauna yankin su yi noma. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti “Kowanne ƙauye kuma zai sake biyan Naira dubu 800, don bai wa mazauna yankin damar girbe amfanin gonakinsu, wannan ita ce yarjejeniya da muka cimma da shugaban ’yan bindiga da ke kula...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Amurkawa sun yi kuskure idan suna tunanin cewa hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai canza matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Dole ne a fara wani sabon mataki na dangantaka tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA saboda gaba daya sabbin al’amura sun bullo. Dokokin majalisar Shawarar Musulunci da yanayin filin sun canza, kuma an kai hari da bama-bamai da kuma lalata cibiyoyin makamashin nukiliya da yawa. Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa, Amurkawa sun yi kuskure idan har suna tunanin kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai sauya matsayin Iran ko kuma ya...
Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da Israila ta dakatar da bude wuta da kawo karshen rikici da Gaza nan take. Sakamakon ya kuma nuna cewa, kaso 80.8 na wadanda suka amsa na ganin cewa mafita ga rikicin Palasdinu ya dogara ne da kafuwar kasashe biyu, inda suka yi kira da a dawo da halaltattun hakkokin kasar Palasdinu. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne a dandalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da...
Babban Hafsan Hafsoshin sojin Iran ya bayyana cewa; Martanin da Iran za ta mayar kan duk wani hari zai kasance murkushewa ne, kuma ba zata jira izinin kowa ba Babban hafsan hafsan sojin kasar Iran ya gargadi makiya, yana mai cewa: Suna yi wa shahidai alkawari cewa: Za su ci gaba da bin tafarkinsu, kuma duk wani sabon harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci azamar mayar da martani daban da na baya. Babban hafsan hafsoshin sojin kasar ta Iran Manjo Janar Abdulrahim Mousavi ya jaddada matsayin wadanda suka yi shahada a safiyar yau Alhamis a yayin bikin tunawa da ranar shahidan Iraniyawa a hare-haren wuce gona da iri, yana mai daukar su a matsayin ginshikan tabbatar da...
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaron Iran za ta fuskanci kakkausan martani mai zafi fiye da tunani Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwar cikan kwanaki 40 da shahadar shahidan Iran a lokacin wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya da Amurka, inda suka jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaro da yankin kasar Iran za ta fuskanci kakkausar martani da ya zarce tunanin makiya, kuma zasu kasance mafi tsanani fiye da abin da ya faru gamakiya da amsu kiran yaki a martanin alkawarin gaskiya na uku. A cikin wata sanarwa da Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka fitar a cikan kwanaki...
Falasdinawa masu yawa ne suka yi shahada a hare-haren da sojojin ‘yan sahayoniyya suka kai kan tantuna da gidaje da ‘yan gudun hijira a Gaza Falasdinawa da dama ne suka yi shahada tare da jikkatan wasu masu yawa da sanyin safiyar yau Alhamis a wasu munanan hare-hare da jiragen yakin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai kan wasu yankuna na zirin Gaza, inda suka kai harin kan gidajen fararen hula da kuma tantunan ‘yan gudun hijira. Jiragen saman sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wani tanti na ‘yan gudun hijira a yankin Tal, kudu maso yammacin birnin Deir al-Balah da ke tsakiyar zirin Gaza, inda suka kashe Falasdinawa akalla biyar tare da raunata wasu. A yammacin sansanin ‘yan...
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam ta Human Rights Watch ta tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun rusa makarantu sama da 500 a Gaza A cikin wani sabon rahoton da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar, kungiyar ta zargi sojojin mamayar Isra’ila da kai hare-hare ba bisa ka’ida ba kan makarantun da ke suka zame mafakar ‘yan gudun hijira a zirin Gaza tun daga watan Oktoban shekarar 2023, inda suka kashe daruruwan Falasdinawa fararen hula. A cikin rahotonta da ta fitar yau Alhamis, kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ta bayyana wadannan hare-haren a matsayin nuna wariyar al’umma, kuma kan iya kai wa ga laifukan yaki. An yi nuni da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila suna yin amfani...
Waɗannan bayanai duk suna ƙunshe ne a cikin jawaban da aka gudanar a gangamin wayar da kai game da wannan cuta, wanda ya gudana a Kaduna. Lokacin da ta ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan wannan gangami, Dr. Maimuna Lawal Garba, ƙwararriyar Likita a fannin hanci, kunni da maƙogwaro, ta fara bayanin ta ne da bayyana abubuwan da suke haddasa wannan cuta ta Kansar Maƙogwaro. Ta ce, “Muna bai wa mutane shawara su kiyayi shan tabar sigari, barasa (giya). Haka kuma akwai yanayin aikin mutane, misali, masu aiki a wurin yankan katako, wannan ƙurar ta katako tana daga cikin abubuwan da za su iya sabbaba ma mutum kamuwa da wannan cuta. “Haka kuma akwai (radiation),...

Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama
Kasar Sin ta sanar a yau Alhamis cewa ta yi nasarar kammala cikakken gwajin sauka da tashin kumbun binciken a duniyar wata mai dauke da bil adama, a wani yankin gwaji dake gundumar Huailai ta lardin Hebei. Gwajin da aka kammala ranar Laraba na nuni da wani muhimmin ci gaban da Sin ta samu a bangaren shirinta na binciken duniyar wata, kuma shi ne karon farko da Sin ta gudanar da gwajin sauka da tashin kumbu mai dauke da dan adama, a wajen duniyar dan adam. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
’Yan bindiga ɗauke da makamai sun shiga ƙauyen Bimasa a Ƙaramar Hukumar Tureta a Jihar Sakkwato sun kashe mutum huɗu sun jikkata wasu da dama a daren ranar Laraba. Ɗaya daga cikin jagorori a ƙauyen ya yi wa Aminiya ƙarin bayani ya ce, a daren ranar Laraba da ƙarfe 12:40 na tsakar dare ɓarayi suka shigo ƙauyen akan babura suna da yawa sun fi mutum 10 a nan take suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi kai tsaye suka harbe mutum biyar, huɗu suka rasu an kai ɗaya asibiti. ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara “A haka suka rika harbi ta ko’ina, sun...
“An kashe da dama, kuma wasu da yawa sun sami munanan raunuka.” In ji Kaftin Adewusi Bayan farmakin ta sama, sojojin kasa na Birget 1 dake karkashin sashe na 2 na OPFY sun kaddamar da wani samame ta kasa a ranar 5 ga watan Agusta, inda suka yi nasarar dakile wani harin kwantan bauna kan hanyar zuwa kauyen Yankuzo, inda rahotanni suka ce an kai ‘yan ta’addan da suka jikkata domin yi musu magani. A cewar majiyoyi da bayanan sirri daga Kauyen, an kashe ‘yan ta’adda fiye da 30 a yayin samamen. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
A yau Alhamis aka yi bikin bude gasar wasanni ta duniya ta 2025 a birnin Chengdu na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki. Onanuga ya bayyana cewa waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba...
Manoma sama da 500 daga gundumomi 15 na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu horo kan kiwon awaki na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi, a wani yunƙuri na rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar al’ummar karkara. An gudanar da wannan horo a Idofian karkashin haɗin gwiwar karamar hukumar Ifelodun da shirin Livestock Productivity and Resilience Support Project (L-PRES). Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mista Kayode Alabi wanda Honarabul Ganiyu Afolabi, dan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Omupo ya wakilta, ya jaddada muhimmancin wannan shiri wajen magance matsalolin da manoman karkara ke fuskanta. Ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai rage rikici ba...
Da yake la’antar kisan a matsayin “mummuna, dabbanci, kuma lamarin da ba za a lamunta ba,” gwamnan ya yi alkawarin tabbatar da adalci. Ya umurci hukumomin tsaro da su dau mataki tare da kama wadanda ke da hannu a kisan nasa nan take. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta bayyana alhinita kan kisan gilla da aka yi wa Umar Abdullahi Hafizi, dalibi da ke matakin karatu na 3 a Sashen Ilimin Zamantakewa (Sociology), wanda wasu masu kwacen waya suka daba wa wuka har lahira a gidansa da ke unguwar Dorayi a ƙaramar hukumar Gwale. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Malam Lamara Garba, ya fitar, wacce aka rabawa manema labarai. A cewarsa, kodayake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’ar, shugabannin BUK sun jaddada cewa suna kokari wajen tabbatar da tsaron ɗalibansu. Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana wannan lamari a matsayin babban rashi da ya girgiza al’ummar jami’ar, tare...
Mun san cewa, ci gaban harkokin matasa na bukatar bunkasar sana’o’i. Cikin shekarun nan, aikin zuba jari ga kasashen Afirka da kasar Sin ke yi na samun ci gaba yadda ake bukata. Inda yawan kudin da Sin take zubawa kai tsaye a fannin samar da kayayyaki a kasashen Afirka, ya kai fiye da dalar Amurka miliyan 400 a duk shekara. Kana darajar hadin kan bangarorin Afirka da Sin ta fuskar gina kayayyakin more rayuwa, ta kai fiye da dala biliyan 37 a duk shekara. Hadin gwiwar bangarorin 2 ya shafi zirga-zirgar ababen hawa, da aikin gona, da makamashi, da tattalin arziki mai alaka da fasahohin zamani, da fasahohin bunkasa tattalin arziki ba tare da gurbata muhalli ba, da dai sauransu,...
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti ranar Litinin. An miƙa jaririn ga iyayensa, Mustapha Aliyu mai shekara 29 da kuma Salmatu Lawal mai shekara 22, bayan da jami’an ’yan sanda suka tsananta binciken lamarin. An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno A cewar Eribo, an samu nasarar ne bayan samun wani sahihin daga wani da ya ba da rahoto ya tuntuɓi wani babban jami’in ‘yan sanda, inda ya nuna shakku kan wata mata da ta yi imanin cewa tana da alaƙa da sace jaririyar da ta ji a cikin labarai....
Wasu ’yan bindiga sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da wasu mutum uku a Ƙauyen Ganmu da ke kusa da Babanla a Ƙaramar hukumar Ifelodun a Jihar Kwara. An samu rahoton cewa, harin ya faru ne a lokacin da waɗanda harin ya rutsa da su, ke kan hanyar Legas zuwa Babanla suka samu matsalar tayar motar a kusa da unguwar. ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore A yayin da suke ƙoƙarin gyaran tayar ne wasu ’yan bindiga biyar suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta. Waɗanda aka kashe sun rasa rayukansu a harin, an bayyana sunayen su da: Alhaji Abdulrazak Ewenla ɗan...
Gwamnatin Jihar Jigawa ta biya iyalai 14 da aikin sake gina Babban Masallacin Gumel ya shafa kudaden diyya da suka kai Naira miliyan 277 da dubu 44. An gudanar da bikin bayar da takardun cekin kudin ne a Fadar Mai Martaba Sarkin Gumel, Dr. Ahmad Muhammad Sani, tare da halartar masu rike da sarautu, da shugabannin al’umma da manyan jami’an gwamnati. Da yake jawabi yayin bikin, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, wanda Babban Sakataren Harkokin Gudanarwa da Kudi na Ofishinsa, Alhaji Abdullahi Sa’idu, ya wakilta, ya shawarci iyalan da su yi amfani da kudaden ta hanya mai amfani wajen gina sabbin gidajensu tare da rungumar sauyin wurin zama cikin hakuri da tawakkali. Malam Bala Ibrahim ya jaddada cewa...
Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya. Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su. An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna Ana zargin ‘yan sanda da karya hannun Sowore Majiyoyin da ke kauyen na sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa wadanda suka mutun sun hada da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu. Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce ya gano faruwar hakan...
Sayar da Nunez zai ba Liverpool damar siyan Alexander Isak daga Newcastle. Sai dai Newcastle ta ƙi karɓar tayin fam miliyan 110 daga Liverpool, saboda tana so ta siyar da Isak ne abkan fam miliyan 150. Liverpool ta riga ta siyo Florian Wirtz daga Bayer Leverkusen a kan fam miliyan 116 da kuma Hugo Ekitike daga Frankfurt a kan fam miliyan 79. Hakan ya sa Liverpool ta kashe kusan fam miliyan 250 a wannan kakar kasuwanni. Ta kuma siyar da Luis Diaz ga Bayern Munich ankan fam miliyan 65.5 da Tyler Morton ga Lyon a kan fam miliyan 15. Ɗan wasan Ingila Harvey Elliott ma na iya barin ƙungiyar a bana. A watan Janairu da ya wuce, Liverpool ta ƙi...
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya bada motocin aiki ga shugabannin hukumomi, jami’an tsaro da wasu manyan jami’an gwamnati a jihar. An gudanar da bikin mika motocin ne a Fadar Gwamnati da ke Minna. Gwamna Bago ya bayyana cewa wannan mataki na bayar da motocin aiki na da nufin tallafa wa harkokin sufuri da kara inganta gudanar da ayyuka yadda ya kamata. Ya yabawa kwazon wadanda suka amfana da motocin a aikin gwamnati tare da bukatar su yi amfani da su bisa gaskiya da amanar da aka dora musu domin cimma nasarorin da ake bukata. Cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin akwai Shugabannin Hukumar Kula da Ma’aikatan Kananan Hukumomi, Hukumar Majalisar Dokoki, Hukumar Ma’aikata da Hukumar Kula da Binciken...
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar da gudanar da tarurruka da kuma gangami da zanga zanga na goyon bayan Gaza a jami’ar. Labarin ya nakalto Dr Julio Frenk shugaban Jami’ar Calfonia a birnin Losangeles na 7th ya bayyana a jiya Laraba kan cewa rike wadannan kudin ba karami matsalace ga Jami’ar UCLA ba, ga kuma kasar Amurka kanta. Gwamnatin nTrump dai ta bayyana cewa Jami’ar LosAngeles a Califonia, da, Columbia University...
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar da gudanar da tarurruka da kuma gangami da zanga zanga na goyon bayan Gaza a jami’ar. Labarin ya nakalto Dr Julio Frenk shugaban Jami’ar Calfonia a birnin Losangeles na 7th ya bayyana a jiya Laraba kan cewa rike wadannan kudin ba karami matsalace ga Jami’ar UCLA ba, ga kuma kasar Amurka kanta. Gwamnatin nTrump dai ta bayyana cewa Jami’ar LosAngeles a Califonia, da, Columbia University...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ta kama wasu bama-bamai da ba su fashe ba da wasu tarin makamai da aka shigar da su jihar cikin kayan gwangwan daga jihar Borno. Lamarin dai ya jefa fargaba a zukatan mutane kan yadda kayayyaki ke yawo babu bincike daga jihohin da ke fama da rikici. Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Kakakin rundunar a jihar, DSP Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan, inda ya ce an kama kayan ne ranar Asabar bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu. Ya ce an samu kayan ne a cikin wani kamfanin da ke...
Jami’an tsaro a kasar Lebanon sun bayyana damuwarsu da yiyuwar sojojin HKI su farwa kasar da yaki da nufin kwace kasar da kuma sunan yaki da kungiyar Hizbullah. Jaridar da nation ta kasar amurka ta bayyana cewa, HKI ta jibje sojojin masu yawa da kuma tankunan yaki a kusa da Jabal sheikh da suka mamaye, don mai yuwa ta fadawa kasar Lebanon ta kuma mamaye gabaci da areawacin kasar kafi ta fuskan kungiyar Hiszullah wacce tafi bada karfinta a kudancin kasar. Wasu majiyoyin tsaro guda 2 a kasar ta Lebanon wadanda basa son a bayyana sunayen na fadar cewa sojojin HKI a kan iyakar kasar Lebanon da Siriya sun bayyana cewa a hankali a hankali sojojin HKI suna matsowa kusa...
Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Kasa sun kutsa inda ake tsare dan gwagwarmaya Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da karfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba. Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da karfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a kokarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba.. A jiya Laraba ne dai Sowore ya amsa gayyatar da ofishin Babban Sufeton ‘Yan sanda na kasa ya yi masa don ya amsa...
Ministan Harkokin wajen Masar Badr Abdelatty ya fara ayyukan diblomasiyya inda ya fara tattaunawa da Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi dangane da farfado da tattaunawa kan shirin Iran na makamashin Nukliya tare da shugaban hukumar, IAEA Rafael Grossi, da kum wakilin Amurka na musamman a gabas ta tsakiya Steve Witkoff,. Amma a yanzun ba tare da barazana ko kuma kaiwa hare-hare ba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wadannan bangarori biyu suna son Iran ta sake bada wata dama, don tattauna batun shiruin makamashin nukliya na kasar da kuma dangane da tashe tashen hankula a yankin yammacin Asia. A dai dai lokacinda al-amura suke ci gaba da tarbarbarewa a yankin kasar masar ta sanya...
“Ko da yake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’a, Hukumar Gudanarwa ta jami’ar na cikin jimami matuƙa da wannan mummunan lamari, kuma tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai,” in ji sanarwar. Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin a kama waɗanda suka aikata wannan laifi. An binne marigayin a garinsu da ke Zariya a Jihar Kaduna. Jami’ar ta buƙaci ɗalibai su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a tare da su. Haka kuma ta roƙi jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen gudanar da bincike. Daga kanmu,...
Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Qasa sun kutsa inda Hukumar ‘Yan sanda ta Qasa ke tsare xan gwagwarmayar neman haqqin bil’Adama Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da qarfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba. Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da qarfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a qoqarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba.. jiya Laraba ne dai Sowore ya masa...
Matasan Kauru Sun zargin Dan Majalisar Dokoki Barnabas Danmaigona da Rashin tabuka komai Wata kungiyar matasa, Kauru Youth Ambassadors (KYA) a karamar hukumar Kauru sun nuna matukar damuwa kan yadda Barnabas Danmaigona, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kauru a majalisar dokokin jihar Kaduna, ya gaza samar da ingantaccen wakilci tun bayan zaben sa. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar mai taken daga ‘Daga Fata zuwa Yaudara’ wanda kuma Junaidu Ishaq Maisalati, ya sanyawa hannu, kungiyar ta caccaki dan majalisar kan abin da ta bayyana a matsayin mai dimama kujera kuma ɗan siyasar da ya gaza wajen gudanar da ayukka a mazabar da kuma aikin da zai amfani al’umma. Sanarwar ta koka da yadda al’ummar Kauru suka sanya kyakkyawan...
Majiyoyi daga cikin jami’an tsaron sun bayyana cewa sojoji da ‘yan sa-kai sun fafata da ‘yan bindigar. Sun kashe ‘yan bindiga da dama, sannan suka ƙwato bindigogi AK-47 guda uku daga hannunsu. ‘Yan bindigar sun gudu, wasu daga cikinsu na da raunuka ko kuma an kashe su, sai dai adadin ba a tabbatar da shi ba tukuna. Bayan faɗan ta yi tsanani, an tura ƙarin sojoji zuwa yankin domin ci gaba da matsa wa ‘an bindigar da suka tsere lamba tare da hana su sake kai hari. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo. A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu. Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da rikicin da ya mayar da babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari daya daga cikin mafiya hatsari a Najeriya. Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Daga shekara ta 2015, mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da garkuwa da su, yayin da matafiya kuma...
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya. Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Ya ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne. “Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,”...
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba. A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya. Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC Ya ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne. “Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,”...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Shugaban Amurka, Donald Trump, yana shirin ƙara tsaurara wa Rasha takunkumi idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kafin ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta. Ko da yake Rasha ita ce ƙasar da aka fi ƙaƙaba wa takunkumi a duniya, har yanzu tana amfani da arziƙin man fetur da iskar gas da ta ke da su domin ɗaukar nauyin yaƙin da ta ke yi da Ukraine. Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma Trump ya bayyana cewa zai sanya sabbin takunkuman da za su hana Rasha cin gajiyar kasuwanci da wasu ƙasashe. Daga cikin matakan, akwai sanya haraji har kashi...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana bukatar samar da wata sabuwar hanyar yin mu’amala da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, inda ya bayyana cewa, ba a kayyade lokacin shiga wasu shawarwari da Amurka ba, ya kuma tabo batun muhimmancin dangantakar dake tsakanin Iran da kasashen Rasha, Sin da Masar. A cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabijin na Iran , Araqchi ya jaddada bukatar samar da sabon tsarin hadin gwiwa tare da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, yana mai nuni da cewa, abubuwan da suka faru wanda ya kai ga kaiwa kasar Iran hari bisa fakewa da rahotannin siyasa na huumar IAEA, yasa dole ne Iran ta...
Ministocin tsaro da muhalli na Ghana na daga cikin mutane takwas da suka rasa rayukansu a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar wannan Laraba, kamar yadda fadar shugaban kasar ta tabbatar, bayan da rundunar sojin kasar ta bayar da rahoton cewa jirgin ya fita daga tsarin tantacewa na na na’urar radar. Lamarin dai ya jefa al’ummar kasar cikin firgici tare da sanar da makoki a dukkanin fadin kasar a hukumance. Ministan tsaro Edward Omane Boamah ya hau kan mukaminsa ne bayan rantsar da Shugaba John Mahama a watan Janairu. Sai kuma Ministan Muhalli, Kimiyya da Fasaha Ibrahim Murtala Muhammed, wanda shi ma yana cikin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin. Shugaban ma’aikata Mahama Julius Debrah ya ce...
“Su dai kawai abin da suke alfahari da shi, shi ne dukiya, yawan gidaje da jirage. Ba su san cewa mutane na kallonsu a matsayin ɓarayi ba.” Sanusi II, ya ƙara da cewa ba shugaban ƙasa ko gwamna kaɗai ke da laifi ba, hatta shugabannin addini da sarakuna ma sun ɓaci a yanzu. “Yawancin shugabanninmu sun shiga ruɗani, babu wanda ya tsira,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Fiye da mashahuran mutane 160 ne da kuma ‘yan jarida suka shiga wani kamfen na neman gwamnatin Jamus da ta dakatar da fitar da makamai zuwa Isra’ila, inda ya zuwa wannan Laraba adadin wadanda suka sa hannu kan rakardar ya kai mutane 367. Daga cikin wadanda suka rattaba hannu, wanda kungiyar fafutuka Avaaz ta sanar, sun hada da fitattun jarumai irin su mawaka Nina Chuba da Clueso, da darektan cibiyar German – Turkey Fatih Akin, da fitaccen mai shirya fina-finai a Jamus wanda ya lashe lambar yabo ta Golden Globe, Ari Folman, da kuma fitacciyar jarumar sinima ta Jamus Sandra Hüller. Kungiyar ta kuma soki lamirin firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu kan aniyar mamaye yankin zirin Gaza gaba daya, tare da...
Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza a daren jiya ya yi sanadiyar shahadar Falasdinawa da dama tare da jikkata wasu masu tarin yawa, yayin da jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kaddadamar da munanan hare-hare a kan a yankuna da dama na Zirin da aka yi wa kawanya, da suka hada da gidajen farar hula da tantunan da aka kafa a mafaka ga iyalan da suka rasa matsugunansu. A cewar wakilin Al Mayadeen, akalla Falasdinawa biyar ne suka yi shahada, wasu kuma suka jikkata bayan da jiragen saman Isra’ila suka yi ruwan bama-bamai a wani tanti da ke a yankin Tal, kudu maso yammacin Deir al-Balah a tsakiyar Gaza. A sansanin Nuseirat na yammacin Gaza,...
Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba. Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba. Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki An fara kula da lafiyarsa a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, daga baya aka kai shi ƙasar Masar domin ci gaba da jinya. Gwamna Agbu Kefas, ya naɗa Emmanuel Lawson, ɗaya daga cikin mataimakansa, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan. A wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jiha ya...
Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba. Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba. Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki An fara kula da lafiyarsa a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, daga baya aka kai shi ƙasar Masar domin ci gaba da jinya. Gwamna Agbu Kefas, ya naɗa Emmanuel Lawson, ɗaya daga cikin mataimakansa, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan. A wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jiha ya...
Ofishin jakadancin kasar Sin a Birtaniya, ya yi tir da kausasan kalamai kan rahotannin dake cewa tsohon firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ziyarci yankin Taiwan na Sin da kiran da ya yi wa kasashen yamma su kulla huldar tattalin arziki da yankin. Wani kakakin ofishin jakadancin ya bayyana a jiya cewa, suna adawa matuka da duk wata ziyara da wani dan siyasar Birtaniya zai kai Taiwan bisa ko wane dalili. Kakakin ya kuma nanata cewa, Taiwan bangaren kasar Sin ne da ba zai iya ballewa ba, kana batutuwan da suka shafi yankin, batutuwa ne na cikin gidan Sin da ba sa bukatar katsalandan daga waje. Bugu da kari, ofishin jakadancin ya ce babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar Zirin...
Majalisar Dokokin Bauchi ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a fadin jihar domin haɓaka ci gaba, inganta shugabanci, da kawo sauƙin gudanar da mulki. Wannan na ƙunshe ne a wani ƙudiri da dan majalisar mai wakiltar mazabar Disina, Sale Hodi Jibir, ya gabatar a yayin zaman da Kakakin Majalisar, Abubakar Y. Sulaiman, ya jagoranta. Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama A cewar Jibir, ƙudurin yana dogaro ne da tanadin kundin tsarin mulki na 1999 wanda ya bai wa majalisun dokokin jihohi damar fara shirin ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi, matuƙar an cika wasu sharuɗa da suka haɗa da goyon bayan kashi biyu...
Kwanturola na shiyyar, Kwanturola AM Alkali, ya yaba wa jami’an bisa yadda suka nuna kwarewa a yayin gudanar da aikinsu. Kwanturolan ya kuma yabawa muhimmiyar rawar da jama’a ke takawa, inda ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su marawa hukumar kwastam baya a yakin da take yi da zagon kasa ga tattalin arziki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Za a fara watsa shirin talabijin na musamman mai mai taken “Karfin Al’adu – Tushe da Aikace-Aikacen Tunanin Al’adu na Xi Jinping a Zhejiang”, ta kafar tashar telabijin ta CCTV-1 ta kamfanin CMG, daga yau Laraba 6 ga watan Agustan nan. Za a rika watsa shiri daya duk rana, daga shirin mai jimillar kaso hudu. A lokacin da Xi Jinping ya yi aiki a Zhejiang, kafin ya zama shugaban kasar Sin daga bisani, ya jagoranci ci gaban bangaren al’adun yankin, ta yadda aka samu nasarori masu ma’anar tarihi. Wadannan nasarori sun ba da gudummawar gaske ga habaka tunanin al’adu na Xi Jinping, ta fuskar ka’idoji da kuma aikace-aikace. Shirin ya mayar da hankali kan wannan tsari na tarihi, wanda ke...
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da kyautar fuloti da kuɗi naira miliyan biyar ga kowane ɗaya daga cikin iyalan tawagar ’yan wasan nan na Kano 22 da suka rasu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni. Mai bai wa gwamnan shawara kan yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya tabbatar da wannan kyauta cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook a wannan Larabar. Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina “Mai girma Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bai wa iyalan ’yan wasan da suka rasu fuloti ɗaya da kuma naira miliyan biyar kowannensu,” in ji sanarwar. Aminiya ta ruwaito cewa, tawagar ’yan wasan...
Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa; Dole ne kasashen musulmi su hana ci gaba da aikata laifuka a Gaza Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim, ya jaddada bukatar kasashen musulmi su dauki matakin hana ci gaba da bala’in jin kai a Gaza ta hanyar diflomasiyya da kuma matsin lamba na siyasa. A safiyar yau Laraba ne shugaba Pezeshkian ya tattauna da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa: “Aikin ta’addancin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aiwatar a Gaza ba abin da za a amince da shi ba ne ga kowane mai ‘yanci,” yana mai bayyana fatansa na ganin “kasashen Musulmi za su yi aiki...
Ya kuma bayyana cewa, tuni aka mika wanda ake zargin ga hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) domin gudanar da bincike tare da daukar matakin da ya dace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Taya Ali Larijani Murnar Nada Shi Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasa Abbas Araqchi, ministan harkokin wajen kasar Iran, ya taya Ali Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sakataren majalisar koli ta tsaron kasar. A cikin sakon taya murna, Araqchi ya taya Larijani murnar nadin da aka yi masa a matsayin sabon sakataren majalisar koli ta tsaron kasar, tare da yi masa fatan samun nasara a sabon mukamin nasa. A cikin sakon taya murnarsa, Araqchi ya bayyana cewa, shi da takwarorinsa na ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a shirye suke su ba da hadin kai sosai ga Larijani wajen gudanar da muhimman ayyukansa, musamman a fannonin diflomasiyya...

An Fara Gudanar Da Juyayin Cikan Shekaru 80 Da Harin Amurka Da Makamin Nukiliya Kan Hiroshima Na Kasar Japan
Birnin Hiroshima na kasar Japan ya yi juyayin cika shekaru 80 da harin makamin nukiliyar Amurka Birnin na Hiroshima ya gudanar da bikin juyayin cika shekaru 80 da kai harin makamin nukiliyar Amurka ta yi a yau Laraba tare da halartar kasashe fiye da 100, inda mahalarta taron suka yi shiru na dan wani lokaci. Kafin a fara yin shiru, a daidai lokacin da bam din nukiliyar Amurka ya fado a kudancin kasar Japan, da dama daga cikin mahalarta taron sun ajiye furanni a wurin taron tunawa da wadanda harin ya rutsa da su. A wajen bikin juyayin, Hiroshima ta sake yin kira ga shugabannin kasashen duniya da su dauki matakin kawar da makaman kare dangi. Wakilai daga kasashe da...
Fararen hula 14 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata a wani hari da dakarun kai daukin gaggawa suka kai El Fasher na Sudan Wata kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Sudan ta sanar da cewa: kungiyar Rapid Support Forces ta kasar Sudan ta Dakarun kai daukin gaggawa ta kashe akalla fararen hula 14 a lokacin da take yunkurin tserewa wani yanki da aka killace a yankin Darfur, bayan shafe sama da watanni 27 ana yaki tsakanin dakarun ‘yan tawaye da sojojin Sudan. Kungiyar lauyoyin gaggawa da ke tattara bayanan cin zarafi da aka yi a yakin, ta kuma watsa rahoton cewa: “An samu raunuka da dama, kana an kama wasu fararen hula da ba a san...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba. Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar. Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku. Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa. Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya. Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban...
“Bari in yi bayani a fili: ba za mu yarda da duk wata dabi’a wacce za ta ruguza dabi’un da muke tsaye a kai ba. Dole ne kowane jami’in gwamnati ya kasance mai lura da al’amuransa, ba wai kawai ofishin ku kuke wakilta ba, har da mutuncin gwamnati baki daya.” In ji Gwamna Abba Kabir Gwamna Yusuf, a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya jaddada cewa, duk wanda aka samu yana taimakawa ko aikata laifuka to zai fuskanci cikakken fushin doka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
Da safiyar Larabar nan ne kwamitin tsaron MDD ya gudanar da taron tattaunawa game da batun rikicin Isra’ila da Falasdinu, inda a jawabinsa game da aniyar Isra’ila ta tsananta hare-haren soji, da mamaye daukacin zirin Gaza, mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana matukar damuwa kan hakan, yana mai kira ga Isra’ila da ta kauracewa wannan mataki mai hadari, yana mai fatan daukacin sassan da lamarin ya shafa za su gaggauta kaiwa ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta mai tsorewa. Geng Shuang, ya kuma jaddada muhimmancin aiwatar da sahihin mataki na dakatar da bude wuta yadda ya kamata, ta yadda hakan zai kubutar da rayukan al’umma, tare da bayar da damar sakin wadanda ake tsare...
Shugaban ya kuma yabawa cibiyoyin koyon ilimi tare da bayyana cewa wadannan nasarorin da aka samu shaida ne na ingancin ilimin Nijeriya wanda ke kekkenshe yara masu basira a duniya. Tinubu ya yi imanin cewa, ilimi muhimmin abu ne ga ci gaban kasa; don haka, babbar hobbasar da gwamnatinsa ta yi a fannin, shi ne kawar da matsalolin kudi ga ‘yan Nijeriya marasa galihu da ke neman manyan makarantu ta hanyar ba su ba shi a ashirin Asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba. Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar. Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Ministan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku. Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa. Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya. Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban...
Gwamnatin kasar Sin ta samar da kudi har yuan biliyan 1.015, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 142 ga lardunan kasar daban daban, domin gudanar da ayyukan jin kai, sakamakon ibtila’in ambaliyar ruwa da ta shafi wasu sassan kasar. Rahotanni na cewa ma’aikatar kudin kasar, da ma’aikatar gona da raya karkara, da ma’aikatar albarkatun ruwa ne suka samar da kudaden, wadanda za a yi amfani da su a ayyuka daban daban na tallafawa yankunan da ambaliyar ta shafa, ciki har da birnin Beijing, da lardin Hebei, da Mongolia ta gida da Guangdong. Kana cikin kudin za a samar da tallafin sake shukar da ruwa ya lalata, da ma kayayyakin aikin gona da ambaliyar ta shafa. Kazalika, za a yi amfani da bangaren...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi maƙarrabansa cewa duk wanda ba zai iya sauke nauyin da aka ɗora masa, ya yi murabus. Wannan gargaɗi na zuwa ne bayan murabus ɗin Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya yi biyo bayan belin wani da ake zargin dilan miyagun ƙwayoyi, Sulaiman Danwawu. Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a Sakkwato Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Wannan lamari ya tayar da ƙura, wanda hakan ya sa Gwamna Abba, ya ɗauki mataki. A cewar sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, gwamnan ya bayyana rashin jin daɗinsa kan lamarin. Hakan ta sa ya jaddada buƙatar dukkanin mambobin majalisar da sauran manyan...
Manoma a Jihar Sakkwato sun koka game da takin da gwamnatin jihar ta ce za ta raba musu don noman damina cewa bai kai hannunsu ba. Duk da cewa an ƙaddamar da rabon takin kusan mako guda da ya gabata. Hatsarin Mota: Yadda hanyar Lambata ke laƙume rayuka a Neja Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna Gwamnan Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya ƙaddamar da shirin sayar da takin zamani da magungunan noma a farashi mai rahusa a Ƙaramar Hukumar Gwadabawa domin bunƙasa harkar noma a daminar 2025. Sama da buhu dubu 105 na NPK da UREA aka sayar a farashi mai rangwame. Hakazalika, an sayi maganin kashe ƙwari da keken noma don raba wa...
Jami’an Alhazai na shiyya-shiyya sun karrama Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa nasarorin da aka samu a aikin hajjin shekarar 2025. Shugaban jami’an alhazai na shiyya-shiyya, Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa ya tabbatar da hakan a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse Babban Birnin jihar. Ya ce karrama Ahmed Labbo, na da nasaba da gudunmawar da ya bayar da kuma samun nasarar aikin hajjin bana a gida da kuma kasar Saudi Arabia. Yace wadannan nasarorin sun sanya hukumar ta samu lambobin yabo da kyautuka da dama a kasa mai tsarki. Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa, yana mai cewar jami’an alhazai na shiyya-shiyya...
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta aiwatar da shirin bayar da kulawar lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke ƙarƙashin tsarin fansho na haɗin gwiwa (Contributory Pension Scheme – CPS), yana mai bayyana shirin a matsayin muhimmin bangare da zai taimaka wa rayuwarsu. A wata sanarwa da mai ba Shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma bada umarnin a gaggauta aiwatar da karin fansho da aka dade ana jiran shi, tare da kafa mafi ƙarancin adadin fansho domin kyautatawa tsofaffin ma’aikata mafi rauni a tsarin CPS. Wannan umarni ya biyo bayan bayani da Daraktar Janar ta Hukumar Kula da Fansho...
Mutum 22 sun gamu da ajalinsu, yayin da wasu 20 suka jikkata, bayan wata babbar mota da ta yi lodin mutane da dabbobi ta yi hatsari a kan hanyar Lambata zuwa Lapai da ke Jihar Neja. Hatsarin ya auku ne da safiyar ranar Litinin. Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Motar ta taso daga Kano zuwa Legas ne lokacin da hatarin ya auku da misalin ƙarfe 3 na safe, sakamakon gudun wuce ƙima. Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC), ta ce dukkanin fasinjojin da ke cikin motar maza ne. An kai gawarwakin Babban Asibitin Suleja, yayin da aka garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Asibitin Gwamnati...
Malaman jami’o’i sama da 100 daga Isra’ila sun bayyana cewar jan kafar da ƙasar Jamus ke yi wajen ɗaukar matakin matsin lamba ga gwamnatin Isra’ila na iya bai wa ƙasar damar ci gaba da aikata manyan laifuffuka a Gaza. Wata wasika da masanan suka rubuta wa ɗaya daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar SPD da ke mulki a Jamus, ta ce rashin ɗaukar matakin na iya bada damar gudanar da wasu sabbin laifuffuka a Gaza, tare da watsi da irin tarihin da aka koya a shekarun baya. A ranar 22 ga watan Yuli, biyu daga cikin jiga jigan kawancen jam’iyyun dake jagorancin Jamus, sun bukaci ƙasar da ta shiga cikin ƙasashen duniya da ke ƙawance domin gaggauta kawo ƙarshen yaƙin Gaza...
A jawabin da Shugaban Jami’ar ABU, Farfesa Adamu Ahmed, ya yi ta bakin mataimakinsa, Farfesa Sanusi Rafindadi, ya yaba da yadda taron ke taimakawa wajen wayar da kai game da wannan cuta mai hatsari. Ya kuma gode wa Hajiya Fatima bisa amsa gayyatar jagorantar taron. Shugabar Sashen Kula da Mata, Farfesa Rahanatu Lawal, ta jaddada buƙatar haɗin kan kowa da kowa wajen yaƙi da cutar. Ta ce mata ba za su iya wannan yaƙi su kaɗai ba, dole ne maza su ba su goyon baya. Daga cikin waɗanda suka gabatar da jawabi akwai Dakta Aminat Jimoh daga Asibitin Koyarwa na ABU. Ta buƙaci mata da su riƙa duba kansu akai-akai, musamman idan suna da tarihin ciwon a cikin danginsu. Ta...
Shugaban Kasa Bola Tinubu, ya taya daliban nan ’yan mata ‘yan asalin jihar Yobe su uku da suka lashe gasar harshen Turanci da aka yi a birnin Landan na Burtaniya. A farkon makon nan ne dai Nafisa Abdullahi Aminu da Rukayya Muhammad Fema da kuma Hadiza Kashim Kalli suka zama zakaru a gasar TeenEagle ta 2025 da aka yi a birnin na Landan. Ambaliya ta lalata kauyuka 3 a Sakkwato Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 A cikin wata sanarwa daga bakin kakakinsa, Bayo Onanuga, ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce nasarar ’yan matan abin alfahari ce ga Najeriya. Tinubu ya kuma yaba wa makarantun da daliban suke karatu, inda ya ce nasarar daliban wata...
Akalla magidanta 50 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kauyuka uku na karamar hukumar Tangaza da ke jihar Sakkwato, sakamakon wani mamakon ruwan sama da aka tafka a yankunan. Ambaliyar da ta mamaye kauyukan na Tangaza ne da suka hada da Gidan Madi da Baidi da Madarare, kuma ta haifar da rushewar gidaje da lalacewar gonaki da rijiyoyi da sauran su. Yadda ’yan bindiga suka sace Zamfarawa 150 a cikin kwana 4 Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas Mutanen da lamarin ya shafa sun ce suna bukatar agajin gaggawa na abinci da magani da tsaftataccen ruwan sha. Shugaban karamar hukumar ta Tangaza, Isah Salihu Kalenjeni, ya jagoranci wata tawaga...
Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada kudurinta na farfado da harkar ilimi ta hanyar gyara makarantun da suka lalace wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata. Da yake jawabi yayin wata ziyarar duba makarantu a Makarantar Sakandare ta Murtala Muhammad da ke ƙaramar hukumar Tarauni, Kwamishinan Ilimi, Dr. Ali Haruna Makoda, ya bayyana halin da wasu makarantu ke ciki a matsayin alamar rushewar tsarin ilimi. Kwamishinan ya nuna damuwa game da yadda ake amfani da harabar makarantu ba bisa ka’ida ba, musamman yadda wasu mazauna yankunan suka mayar da harabar Makarantar Murtala Muhammad wajen zubar da shara. Ya tabbatar da cewa za a ɗauki matakin gaggawa don dakile lalacewar muhalli da kuma tabbatar da amintaccen wuri don karatu. ...
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Zamfara, CP Ibrahim Balarabe Maikaba, ya kawata jami’ai 390 da aka daga matsayinsu zuwa sabon mukami a rundunar. An gudanar da bikin kawata jami’an ne a Hedikwatar Rundunar ‘Yan Sanda da ke Gusau, babban birnin jihar. A cewar sanarwar da mai magana da yawun ‘yan sanda, DSP Yazid Abubakar, ya fitar, Kwamishinan ‘Yan Sanda ya taya sabbin jami’an murna tare da bukatar su tabbatar da cancantarsu da mukaman da aka ba su, ta hanyar rubanya kishin aiki, ladabi da kwarewa a ayyukansu. Ya jaddada bukatar jami’an da su dage wajen yin aiki da jajircewa da kuma bayar da ingantaccen tsaro ga al’ummar Jihar Zamfara da Najeriya gaba ɗaya. Daga cikin waɗanda suka sami...
Iran ba zata taba amincewa wata hukuma ko wata kungiyar kasa da kasa ta kusanci cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban kwamitin tsaron kasa da kuma al-amuran harkokin waje a majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a ranar Litinin da ta gabata. Ya kuma musanta zancen da wasu suke yadawa na cewa masu sanya ido a ayyukan makamashin nukliya daga hukumar IAEA sun dawo suna ayyukansu a fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ebrahim Azizi shugaban kwamitin ya kara da cewa an tsara cewa wata tawaga daga hukumar IAEA zata kawo ziyarar aiki nan Tehran don tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar kan abubuwan da suka shafi sayasar hukumar IAEA...
Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini yana fadar haka a wani wani taro na tunawa da daya daga cikin shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kallafawa kasar. Ya kara da cewa duniya ta sauya sabada nasarar sannan musamman a fagen diblomasiyya da kuma kafofin yada labarai a duniya, wanda ya bar tasiri mai kyau ga kasar. Labarin ya kara da cewa, akalla kasha 60 % na mutanen duniya...
Ya ce malamin bai fi Sheikh Ahmad Gumi ba, wanda ya gaza yin zaman sulhu da Turji. Guyawa, wanda ya daɗe yana taimaka wa jami’an tsaro da bayanai, ya ce ba a taɓa yin sulhu da mutum yayin da yake ci wa jama’a zarafi ba. Ya ce: “Za a iya cewa mutum ya yi sulhu alhali yana ci gaba da karɓar haraji daga hannun manoma da tilasta musu noma? Ko kuma yana kashe mutane da ƙond motar jami’an tsaro?” Guyawa ya ƙara da cewa Turji da sauran ‘yan ta’adda kamar Kachalla Choma da Kachalla Haru suna da makamai da kwamandoji da yawa, kuma babu wani abu da ke nuna sun ajiye makamansu. Ya ce malamin da ya faɗi cewa Turji...
‘Yansanda a kasar Iran sun bada labarin cewa suna amfani da jiragen leken asiri da wasu kayakin masu aiki da lantarki na zamani don tabbatar da lafiyar masu tattalin 40 zuwa wurare masu tsarki a kasar Iraki. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Brigadier General Ahmad Ali Goodarzi shugaban yansanda a nan kasar Iran ya bayyana cewa, yansandan kasar suna aiki tare da rana wajen kyautata ayyukan tsaro a dukkan kofofi shiga Iraki daga Iran guda 6 saboda tabbatar da tsaron masu zuwa 40 na Imam Hussain (a). Ya ce: Yansa a kan iyakokin kasar suna sanya kula da musamman a kofofin shiga kasar Iraki, wadanda suke da cinkoson mutane. Tare da amfani da jiragen marasa matuka...
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cikakken goyon bayan rundunar ‘yan sanda ga Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano wajen tabbatar da kiyaye dabi’u da yakar munanan halaye a cikin al’umma. CP Bakori ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar wayar da kai da Sakatare na Hukumar, Abba El-Mustapha, ya kai tare da tawagarsa zuwa hedikwatar rundunar ‘yan sandan Kano. A yayin ganawar, CP Bakori ya yaba da jagorancin hukumar, musamman kokarin da El-Mustapha ke yi wajen tsara harkokin masana’antar Kannywood da kuma kare tarbiyya ta hanyar sa ido mai tsauri. Ya tabbatar da ci gaba da hadin gwiwa tsakanin rundunar da hukumar, musamman wajen dakile cin zarafi da amfani da kafafen sada zumunta...
Mataimakin shugaban kasar Iran Muhamad Reza Aref ya bayyana cewa kasar Iran tana goyon bayan dukkan shirin zaman lafiya a yankin musamman tsakanin kasashen Armenia da kuma Azarzaijan. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Aref yana fadar haka a lokacin ganawarsa da shugaban kasar Armenia Vahagn Khashaturyan a kasar Tukeministan ake ake gudanar da taron kasashen wadanda basa kan bakin ruwa a duniya a ranar Litinin. Majalisar dinkin duniya ce ta take shrya wannan taron don ci gaban irin wadannan kasashe a duniya karo na 3TH. Aref yace yana fatan zaman zafiya ta dore a cikin kasashen yankin don amfanin kowa. Daga karshe mataimakin shugaban kasan Iran ya bayyana cewa Iran tana goyon bayan kasar Armenia ta...
Iran ba zata taba amincewa wata hukuma ko wata kungiyar kasa da kasa ta kusanci cibiyoyin makamashin nukliya na kasar Iran ba. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto shugaban kwamitin tsaron kasa da kuma al-amuran harkokin waje a majalisar dokokin kasar Iran yana fadar haka a ranar Litinin da ta gabata. Ya kuma musanta zancen da wasu suke yadawa na cewa masu sanya ido a ayyukan makamashin nukliya daga hukumar IAEA sun dawo suna ayyukansu a fordo, Natanz da kuma Esfahan. Ebrahim Azizi shugaban kwamitin ya kara da cewa an tsara cewa wata tawaga daga hukumar IAEA zata kawo ziyarar aiki nan Tehran don tattaunawa da jami’an gwamnatin kasar kan abubuwan da suka shafi sayasar hukumar IAEA...
’Yan bindiga sun sace mutum 150 a mabanbantan hare-haren da suka kai kauyuka daban-daban na jihar Zamfara a cikin kwana hudu. Kakakin Gwamnatin jihar ta Zamfara, Mahmud Mohammed Dantawasa ne ya tabbatar da hakan ga BBC. Sai dai duk da yake bai bayyana hakikanin adadin mutanen da aka sace ba, amma ya ce gwamnatinsu na iya kokarinta wajen ganin ta ceto su. Duk wanda ya haka rijiyar burtsatse a Lekki ruwan masai yake sha – Gwamnatin Legas ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’ Haka na zuwa ne a daidai lokacin da malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunna, ya ce kwamitin zaman lafiyar da yake jagoranta ya sami nasarar kulla yarjejeniyar zaman...
A dai dai lokacinda ake yaki na kwanaki 12 tsakanin Iran da HKI da Amurka, daga ranar 13-24 na watan Yunin da ya gabata, cibiyoyin yakin yanar gizo na kasar Iran sun gwada karfinsu da kuma kwarewansu a wannan fagen fama. Kanfanin dillancin labarai na Tasnim na kuma kasar Iran ya nakalto sharhin wasu kafafen yada labarai na kasashen yamma dangane da shi. Makarantar Midle East Institute ya dubi wannan al-amarin a cikin wabi bayani da ya fitar. Inda yake cewa cibiyoyin yakin yanar gizo na Iran sun shagaltu a wannan lokacin da kare cibiyoyin kasar Iran, amma ta kuma ya aiki da kare kasar taga makiya musamman masu taimakawa HKI a wannan yakin. Kuma da hakan ta kare wurare...
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali Namadi, ya ajiye aikinsa bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karɓi rahoton kwamitin bincike da ke duba rawar da ya taka a batun ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Wannan matakin na murabus ana kallonsa a matsayin wani muhimmin cigaba da ke nuna jajircewar gwamnatin jihar wajen kare gaskiya, bayyana ta da kuma ɗaukar nauyin ayyukanta a bainar jama’a. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, Kwamishinan ya bayyana cewa ya yanke shawarar murabus ne duba da muhimmancin al’amuran da suka shafi jama’a da kuma halin da ake ciki. Ya ce: “A matsayina na ɗaya daga cikin...
Babbar Kotun Shari’a ta Minna a Jihar Neja ta bayar da wani umarnin na wucin gadi game da gidan rediyon Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd, inda ta hana Gwamnatin Jihar ɗaukar duk wata matsaya da za ta dakatar da ayyukan gidan rediyon. Mai Shari’a Mohammed Mohammed ne ya yanke hukuncin bisa ƙorafin gaggawa (motion ex-parte) da Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd da Daraktan gudanarwarta, Mohammed Shuaibu Badeggi, suka gabatar a kotun da ke Minna. A cikin ƙorafin, lauyoyin masu ƙara sun jingina hujjoji da sassa daban-daban na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), da kuma Dokar Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC Act). Hukuncin kotun ya hana wadanda ake ƙara, ciki har...
Gwamnatin jihar Legas ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar duk wanda yake haka rijiyar burtsatse a unguwar masu hannu da shuni ta Lekki da ke jihar, ruwan masai yake sha. Babban Sakatare a ofishin da ke kula da magudanun ruwa da tsaftar ruwan sha a jihar, Mahmood Adegbite ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki kan samar da ruwan sha a jihar a kwanakin baya. DAGA LARABA: Me Ke Sa Matasa Zama Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa A Kafafen Sadarwa Na Zamani? ‘Za a yi ambaliyar kwana 5 a jihohi 19 na Najeriya’ Mahmood ya kuma ce gurbataccen ruwan sha a unguwar zai iya haifar da barazanar lafiya matukar ba a bi hanyoyin da suka dace wajen...
Ta sake kafa tarihi bayan da jaridar National Concord mallakar MKO Abiola ta naɗa ta a matsayin editan jaridar ta farko, inda A shekarar 1986, aka ɗaga darajarta zuwa matsayin Manajan Darakta kuma Babban Edita mace ta farko da ta riƙe wannan matsayi a tarihin jaridun Nijeriya. Ta auri MKO Abiola a shekarar 1981, kuma ta tsaya tsayin daka tare da shi wajen gwagwarmayar siyasarsa da rikicin da ya biyo bayan zaɓen 12 ga watan Yuni, inda ta bayar da gagarumar gudunmawa a fagen jarida, tare da shafe kusan shekaru 30 tana jan ragamar kafafen yaɗa labarai a Nijeriya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wasu matasa sun zabi tallata ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta na zamani ta yadda bai kamata ba a wasu lokutan. Tallata ‘yan siyasa da matasan suke yi kan haifar da hatsaniya, ko kiyayya, a intanet ko ma a zahiri a tsakanin su. NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu matasa suka zabi zama “sojojin baka” ko “karnukan farautar” ‘yan siyasa a kafafen sada zumunta. Domin sauke shirin, latsa nan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp