JMI Ta Bukaci Kungiyar Majalisun Dokoki Ta Duniya Su Kori HKI Daga Cikinta
Published: 2nd, July 2025 GMT
Shugaban tawagar Iran a kungiyar hada kan majalisun dokokin kasashen duniya ya bukaci kungiyar ta yi tir da HKI saboda hare-haren da ta kai mata wanda ya keta dokokin kasa da kasa, ya kuma bukaci a koreta daga kungiyar.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Manoorchehr Mottaki yana fadar haka a wata wasikar da ya aikewa shugaban kungiyar majalisun dokokin ta duniya wato IPU, shugaban Tulia Ackson, ya ce abin fata shi ne kungiyar zata yi tir da HKI kan sabawa doka ta 2(4) na MDD.
Har’ila yau Mottaki ya bayyana cewa yana fatan Ackson zai sa a jingine samuwar HKI a kungiyar.
Ya ce majalisar majalisun ta tattauna dangane da hare-haren Amurka da HKI kan kasar Iran su kumka yi All..wadai da su.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban kasar Iran ya soki lamirin hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA
A wata tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron a yammacin jiya Lahadi, shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi Allah wadai da dabi’ar nuna fuska biyu daga Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya, yana mai cewa irin wannan dabi’a ta nuna fuska biyu za ta janyo rugujewa da haifar da matsaloli da dama ga tsaron yankin da ma duniya baki daya.
A yayin wannan tattaunawa, shugaba Pezeshkian ya ce, wadannan ayyuka na nuna fuska biyu sun haifar da matsaloli da dama ga harkokin tsaro na yanki da na duniya, kuma ana sa ran hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA za ta mutunta haƙƙin kasashe da guje wa ɗabi’a nuna fuska biyu a fagen ayyukanta da kuma kare haƙƙin ƙasashe membobinta.
A martanin da shugaban kasar Faransa ya nuna dangane da matakin Iran na dakatar da hadin gwiwa da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, shugaba Pezeshkian ya soki yadda babban sakataren hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ke bayar da rahotannin da ba su dace ba kan shirin makamashin nukiliyar Iran da kuma rashin yin Allah wadai da harin da aka kai kan cibiyoyin makamashin nukiliyar Iran, wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa.