Kokarin Zamanantar Da Sin Da Afrika Na Kara Karfafa
Published: 28th, June 2025 GMT
Masana da jami’ai a Nijeriya, sun yaba wa ci gaba na a-zo-a-gani da karin kuzarin da ake samu a hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijeriya, suna masu bayyana kokarin da aka yi zuwa yanzu a hadin gwiwar bangarorin biyu a tafarkin zamanantar da kansu.
Masanan sun bayyana haka ne yayin taro na biyu na bayan taron FOCAC da aka yi ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar.
Da yake jawabi, daraktan cibiyar nazarin Sheriff Ghali Ibrahim, ya ce daga Bandung a 1955 zuwa Beijing a 2024, Sin da Afrika sun ci gaba da bijirewa mulkin mallaka da danniya, yayin da Sin ta yi ta goyon bayan kasashen Afrika wajen zamanantar da kansu da samu ci gaba, ta hanyar zuba jari da bayar da tallafi da rance da sauransu.
Masu gabatar da jawabai da dama sun bayyana ci gaban da aka samu a baya-bayan nan a hadin gwiwar Sin da Nijeriya, suna masu jinjinawa hadin gwiwar abota bisa manyan tsare-tsare da shugabannin kasashen biyu suka cimma a bara. Sun kuma bukaci hukumomin Nijeriya su kyautata amfani da manufar soke haraji ta Sin, su kuma yayata damarmakin ci gaba da cimma burikan kasashen biyu na samun karin kuzari. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: a hadin gwiwar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Kefas Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi
Daga Sani Sulaiman
Gwamnan Jihar Taraba, Dr. Agbu Kefas, ya yi jimami kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis 27 ga watan Nuwamban 2025, yana da shekaru 102.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan Yada Labarai da Hulda da Jama’a, Mista Emmanuel Bello, ya sanyawa hannu.
Gwamnan ya ce rasuwar wannan babban malami babban rashi ne ga kasa, yana mai nuna cewa a wannan lokaci ne ake matuƙar bukatar irin gudummawar da yake bayarwa, duba da kalubalen da kasar ke fusfuskanta.
Ya kara da cewa marigayi Sheikh ya koyar da ilimi da zai ci gaba da jagorantar kasa kan batun zaman lafiya tsakanin addinai.
Haka kuma, Dr. Kefas ya yabawa halayen Sheikh Bauchi, wanda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tawali’u, jin kai, da haƙuri.
Saboda haka, Gwamna Agbu Kefas ya yi kira ga jama’a da su yi koyi da jagorancin wannan fitaccen malami.
Ya ce al’ummar kasa za su ci gaba da bin tsarin ladabi da tarbiyyar da marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya koyar.
A wani bangaren, Dr. Kefas ya ja hankalin ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da addininsu ba.
Ya jaddada muhimmancin jurewa da girmama ra’ayin juna maimakon nacewa a kan namu ra’ayin, tare da tabbatar da aniyarsa ta ci gaba da hidima ga dukkan ‘yan Jihar Taraba bisa adalci ba tare da la’akari da addini ko kabilarsu ba.