2025-06-29@19:56:58 GMT
إجمالي نتائج البحث: 43

«taron sauraron jin ra»:

    Idi ya kuma yi nazari kan matakin da bangaren kiwon dabbobin kasar yake, inda yawan Shanu suka kai miliyan 20.9, Tumaki miliyan 49.1, Awakai miliyan 88.2, Kajin gidan gona kuma miliyan  258.5. Kazalika, Maiha ya jaddada muhimmancin hadakar ta zuba hannun jari a fannin na kiwon dabbobin, wanda ya sanar da cewa; hakan zai taimaka matuka gaya wajen dakile yaduwar cututtukan da ke yi wa dabbobin illa. A nasa jawabin, Babban Shugaban Kamfanin Ricardo Lacerda ya bayyana cewa; kasar Brazil na shirin samar da wuraren kiwon dabbobi na zamani kimanin guda 200,000 a wasu daga cikin jihohin wannan kasa, musamman don kara samar da isasshen naman Shanu. Ya kara da cewa, kasar za kuma ta tabbatar da kokarin kara habaka...
    Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lallai zai kara rura wutar rikici a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila.   Sai dai ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai da cewa “abin takaici ne” sannan ya ce Iran ta tanadi “dukkan zabin kare ‘yancinta”, yana mai jaddada cewa Amurka za ta fuskanci “tsauraran sakamako”.   Araghchi ya kara da cewa, Amurka ta keta kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.   Bugu da kari, wani dan Majalisar kasar Iran, ya kara da cewa, “babu wani mummunan lahani...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa, kasar Iran ta shiga yaki, kuma don haka dole sai an sami sauyi a rayuwar mutane ba. Fatima Muhajirani ta bayyana cewa daga yau ramukan layin dogo a cikin birnin Tehran wuraren mafaka da muyewa ne na mutanen da suke birnin har’ila yau za’a bude masallatai da makarantu don su zama wuraren samun mafaka. A wani bangare fatimeh Muhajirani ta bayyana cewa an rufe sararin samaniyar kasar Iran, don haka babu jirgi wanda zai tashi a ciki ko wajen kasar har zuwa abinda hali yayi ta kuma kara da cewa a halin yanzu jirgin kasa zai zama hanyarb tafiya mafi sauki a wannan haling a mutane. Tace mahajjan Iran zasu dawo ta hanya...
    A yau Asabar ne kasar Sin ta yi nasarar harba tauraron dan Adam na lura da yanayin bala’u a doron kasa, wanda ake sa ran zai rika samar da bayanai ga kasar Sin dangane da aukuwar bala’u daga indallahi, ta aikewa da sakwanni tsakanin sararin samaniya zuwa doron duniya. An harba tauraron dan Adam din mai suna Zhangheng 1-02, ta amfani da rokar Long March-2D, daga tashar harba kumbuna ta Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin, da karfe 4 saura mintuna 4 agogon Beijing, ya kuma shiga da’irarsa ba tare da wata matsala ba, kamar dai yadda hukumar kula da binciken sararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA ta tabbatar. Kazalika, CNSA ta ce, wannan aiki muhimmin mataki ne...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta harbo jiragen saman yaki kirar F-35 Iran ta zama kasa ta farko a duniya da ta yi nasarar harbo jiragen yaki kirar F-35, bayan da ta yi nasarar auna wasu jiragen saman yakin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kirar F-35 guda biyu, kuma ta barar da su kasa. Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi amfani da wadannan jirage masu tsananin ci gaban zamani wajen kai hare-haren wuce gona gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da safiyar ranar Juma’a, wanda hare-haren suka yi sanadiyyar shahadar wasu manyan jami’an sojan Iran da masana kimiyyar nukiliya da fararen hula da suka hada da mata da kananan yara. Ma’aikatar hulda...
    Wani babban jami’in sojan Iran ya ce an kai hare-hare a kalla wurare 150 a farmakin ramuwar gayya kan gwamnatin Isra’ila, ciki har da wasu sansanonin soji masu matukar muhimmanci. Da yake zantawa da gidan talabijin na kasar da sanyin safiyar Asabar, Birgediya Janar Ahmad Vahidi, babban mai ba da shawara ga babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya ce, rundunar ta IRGC ta yi nasarar aiwatar da shirinta na Operation True Promise III. A cewar kwamandan na IRGC, an kuma kai hari kan ma’aikatar harkokin soji da cibiyoyin soji da masana’antu a lokacin da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke daukar fansa. Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su sun hada da Manjo Janar Mohammad...
    Abdulazeez pleaded not guilty to the two-count charge. Abdulazeez ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da su biyu. Bayan rokon da ta yi, lauyan ICPC, Hamza Sani, ya bukaci kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 13 ga watan Yuni, 2025, domin masu gabatar da kara su gabatar da shaidu. Sai dai daga baya kotun ta ba da ranar sannan ta dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yunin 2025 domin sauraron karar. Lauyan wanda ake tuhuma ya nemi a ba shi belin, wanda ICPC ba ta yi adawa da shi ba. Mai shari’a Iheabunke ya bayar da belinta a kan kudi naira miliyan 10, tare da mutane biyu da za su tsaya mata. Ya ce dole ne...
    Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta bayyana cewa jerin wuraren da zata kaiwa hare hare a HKI a duk wani yakin da zata taso tsakanin kasshen biyu, suna hannu. Daga ciki har da ciboyoyin Nukliyar kasar wadanda ta boye su. Tashar talabjin ta Presstv a nann Tehran ta nakalto majalisar ta na fadar haka a jiya Litinin, ta kuma kara da cewa ta kara samun bayanai masu muhimmanci a wannan fagen, bayan bayanan leken asirin da ta samu a cikin yan kwanakin da sukka gabata. Labarin ya kara da cewa a halin yanzu sojojin JMI suna cikin shiri fiye da na ko wani lokaci, don maida martani ga makiya. Tace a halin yanzu jerin wuraren da sojojin Iran zasu...
    Wani kamfanin kera kayakin aikin likita mai zaman kansa a nan Tehran ya gabatar da wata na’ura mai aikin tiyata wanda kuma aka dora masa kayan aiki na zamani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an gabatara da wannan na’urar a kasuwar baje kolin kayakin aikin likita karo na 26TH wanda ke gudana a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa samar da kayalin aikin likita wadanda suke tafiya da zamani, ya zama dole ne bayanda aka haka sayarwa kasar Iran irinsu daga waje. Wannan hanin ya sa a dole daga cikin gida kwararru suka fara samar da kayakin aikin likita na zamani, don wadatar da asbitocin kasar daga sayan na waje, har ma tana...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake yi kutse cikin garin Al-Qunaitra na kasar Siriya tare da kafa wurin bincike lamarin da ya fusata al’ummar yankin Sojojin mamayar Isra’ila da suka sake yin Kutse cikin yankunan kasar Siriya sun gudanar da sintiri a yankunan tare da kafa shingen binciken ababan hawa tsakanin Khan Arnabeh da kauyen Jaba da ke lardin Quneitra. Sintirin ya kunshi yahudawan sahayoniyya goma masu magana da harshen Larabci na ka’ida kuma suna sintirin ne a motoci kirar Hummer. A cewar kungiyar kare hakkin bil’adama ta Siriya, sojojin mamayar Isra’ila biyu kuma sun kutsa kai a tsakanin garuruwan Jaba da Khan Arnabeh, kusa da tsohon wurin binciken ababan hawa na Al-Saqri. Sun samu rakiyar motocin sojoji dauke masu rakiya...
    Likitocin Iran sun yi bikin murnar nasarar da ta samu na dasa na’urar dawo da ji da inganta shi ga masu matsalar kurmantaka da raunin ji a lardin Khuzestan na kasar Ƙaunar sana’a, dagewa, da sadaukarwa sune sirrin nasarar kowane aiki da hidimar jin kai. Waɗannan kalaman ne Farfesa Nadir Al-Saki ya fara bude jawabinsa a yayin bikin nasarar da aka yi na aikin tiyatar dashen na’urar magance matsalar Rashin ji da rauninsa sau 1,500 a lardin Khuzestan dake kudu maso yammacin ƙasar. Wadannan tiyata sun bayyana kwarewar aikin likita da basirar likitoci a lardin, wajen maido da ji da magana ga wadanda suka rasa jin tun da fari. Bikin dai ya samu halartar likitoci da ma’aikatan jinya da yara...
    Kasar Faransa ta ce daga ranar daya ga watan Yuli mai zuwa ta haramta shan sigari a wuraren taruwar jama’a. Kasar ta ce wuraren da haramcin ya shafa sun hada da makarantu da tashoshin mota ko na jirgi, wuraren shakatawa, wuraren wasanni ko kasuwanni saboda kada yara kanana su gani. Yadda ambaliyar Neja ta ci mutum 12 ’yan gida daya NAHCON ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin 2025 Ministar Lafiya da Iyali na kasar, Catherine Vautrin ce ta bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ta ce, “Dole a daina shan sigari a wuraren da yara suke. “’Yancin shan sigari ya kare ne a inda ’yancin yara na shakar tsaftatacciyar iska ya fara,” kamar yadda ministar ta shaida wa jaridar Ouest-France...
    Jaridar “Maariv” ta buga labarin da yake cewa; Tattauanwa a tsakanin “Isra’ila” da kasashen Afirka akan yadda za su bayar da dama ga mutanen Gaza da su yi hijira zuwa can, ta yi isa sosai.  Rahoton jaridar na jiya Juma’a ya ci gaba da cewa; Tattaunawar ana yinta akarkashin damar da za a bai wa Mutanen Gaza  su yi hijira cikin zabin kansu, zuwa wasu kasashen na Afirka, kuma Amurka tana cikin wadanda ake tattaunawar da ita da wadannan kasashen na Afirka. Haka nan kuma jaridar ta ‘yan sahayoniya ta ce, kasashen da ake tattaunawa da su, sun nuna amincewarsu a matakin na farko ka karbar bakuncin mutanen Gaza. Tattaunawar dai ta kunshi yadda za a gina matsugunan Falasdinawan da...
    MDD ta bayyana cewa; Da akwai damuwa mai zurfi akan halin da ‘yan Hijirar Sudan suke ciki a gabashin kasar Chadi saboda rashin masu bayar da kudaden taimakon kula da su. Ma’aikatan MDD a fagen ayyukan ceto sun ce ana samun kwararar ‘yan hijira daga Sudan zuwa gabashin kasar ta Chadi, da kuma ‘yan kasar ta Chadi da suke komawa gida. Tun da yaki ya barke a Sudan zuwa yanzu an yi rijistar kwararar ‘yan Sudan masu yawa. A cikin wata daya kadai ‘yan Sudan  su dubu 55, sai kuma ‘yan asalin Chadi da su ka koma gida zuwa Jahar Inidy da yankin Fira, a gabashin kasar, da su kuma sun kai dubu 39. Sanarwar ta MDD ta ci gaba...
    Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta soki yunkurin da Amurka ke yi na hana kasashen duniya amfani da sashen harhada na’urorin laturoni na Chips kirar kasar Sin. Wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar a Larabar nan, ta kira yunkurin na Amurka da cin zali daga bangare guda, da baiwa kasuwa kariya, matakin da tabbas zai illata tsarin ayyukan masana’antun kira da rarraba sassan semiconductor na duniya.   Kazalika, kakakin ma’aikatar ya ce a baya bayan nan sashen lura da harkokin cinikayya na Amurka ya fitar da wasu bayanai, ta fakewa da batun wai ana keta dokokin Amurka na fitar da hajoji, da nufin haramtawa sassan kasa da kasa amfani da sassan na’urorin Chips masu kunshe da manyan fasahohin sarrafa bayanai...
    Iran ta yi Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan sansanonin ‘yan gudun hijirar a Jabalia da Khan Younis na Falasdinu. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Esmail Baghai ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren na Isra’ila, yana mai cewa hakan ya saba wa dokokin kasa da kasa. A yayin da yake bayyana goyon bayansa ga al’ummar Falastinu da ake zalunta, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kakkausar suka kan mummunan hare-haren da gwamnatin sahyoniyawan ta kai kan matsugunan ‘yan gudun hijira da kuma sansanonin ‘yan gudun hijira a Jabalia da Khan Younis, wanda ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama wadanda ba su ji ba ba su gani ba, da suka hada da kananan...
    Gwamnatin Amurka da kuma kasar Ukraine daga karshe sun rattaba hannu kan yarjeniyar hakar ma’adinai masu karanci na kasar Ukraine, don bawa kasar damar biyan basussukan da Amurka ta ke binta sanadiyyar yakin da take fafatawa da kasar Rasha fiye da shekaru 3 da suka gabata. Jaridar ‘The Nation” ta kasar Amurka ta kara dacewa yawan kudaden da Amurka ta tallafawa Ukraine a yakin dai ya kai dalar Amurka biliyon $175, kuma wannan ita ce hanya tilo wacce Ukraine zata iya biyan wadannan basussuka. Labarin ya kara da cewa a jiya Laraba ce kasashen biyu suka rattaba hannu a kan yarjeniyar. Wannan na faruwa ne al-hali ana ci gaba da yaki tsakanin Rasha da Ukraine. Wannan yarjeniyar dai ta tabbatarwa...
    Dabbobi sama da miliyan guda ne ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar Babura da ke jihar Jigawa. Shugaban karamar hukumar Babura, Alhaji Hamisu Muhammad Garu, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da aikin rigakafin dabbobi na bana. A cewarsa, fiye da tumaki da awaki miliyan daya da shanu dubu ashirin ake sa ran za a yi wa rigakafi a fadin karamar hukumar. Ya jaddada cewa karamar hukumar na da cikakken shiri da kudurin tallafawa sauyin noma na Gwamna Umar Namadi, domin inganta rayuwa da tattalin arzikin al’ummar jihar. Shugaban ya jaddada muhimmancin masu kiwon dabbobi su bada hadin kai yayin aikin rigakafin domin tabbatar da lafiyar dabbobinsu. Alhaji Hamisu Garu ya kuma nuna jin...
    Aljeriya sun kori fiye da bakin haure 1,100 zuwa Nijar a rana guda, al’amarin da ba a taba ganin irinsa ba. Bakin hauren da hukumomin Aljeriyar suka bayyana da basa bisa ka’ida, an kora su a cikin hamadar sahara a ranar Asabar din da ta gabata, Inda sukayi tattaki zuwa kan iyakar kasar Nijar, kasar da dubban bakin haure ke bi domin zuwa Libya da Aljeriya domin isa Turai. Wannan dai shi ne karo na farko da aka kori bakin haure da dama daga kasar Aljeriya a lokaci guda. A cewar kungiyar ‘Alarme Phone Sahara’ ta Nijar da ke taimakawa bakin haure a cikin hamada, an kori mutane 1,140 a lokaci guda, adadin da ba a taba ganin irinsa ba....
    Shugaba Vladimir Putin a yau Asabar ya umarci sojojin Rasha da su tsagaita buɗe wuta a Ukraine a wanan ranar ta Ista da kuma gobe Lahadi. Putin ya kuma yi kira ga Kyiv da ta yi hakan, yayin da ake ganin tattaunawar tsagaita buɗe wuta ta ci tura. Kada Kanawa su bari rigingimun siyasa su hana su zaman lafiya — Shettima Shin Mataimakin Gwamnan Bauchi ya ‘mari’ Ministan Tinubu? Haka kuma, Rasha da Ukraine sun yi musayar fursunonin yaƙi na sama da mutum 500 — kuma mafi girma tun bayan fara yaƙi a tsakanin kasashen biyu. Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskiy, ya ce ƙasarsa ta karɓi sojoji fursunonin yaƙi akalla 277 waɗanda ke tsare a gidajen yarin Rasha, kamar yadda ya...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke neman kawo karshen yakin Gaza bayan sun rattaba hannu kan wasu takardu da ke nuna bukatar hakan. A bayan nan dai fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra’ila, ciki har da janar-janar, suka sanya hannu kan wata takardar neman gwamnatin Isra’ila ta mayar da hankali kan dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ko da hakan zai kai ga dakatar da yaƙin da ake yi a yankin Falasdinawa. Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno A cewar Jaridar Maariv a ranar Litinin, sojoji 1,525...
    Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a yau Laraba . Ya kuma kara da cewa, a wannan karon sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, kan wasu wurare masu muhimmanci a birnin Yaffa (tel’aviv). Haka ma sun cilla wasu makaman kan jirgin yaki mai daukar jiragen sama na Amurka wato USS Harry Truman dake arewacin tekun red Sea. Kafin haka dai jiragen Amurka...
    Jagoran ‘yan adawar Isra’ila Yair Lapid ya yi kira da a gudanar da zanga-zangar gama-gari idan Firaministan kasar Benjamin Netanyahu ya ki bin hukuncin da kotun kolin kasar ta yanke na dakatar da matakin da gwamnatinsa  na korar shugaban hukumar tsaron cikin gida ta Shin Bet.  Yair Lapid ya shaidawa dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv cewa “Idan har gwamnatin 7 ga watan Oktoba ta yanke shawarar kin yin biyayya ga hukuncin kotun, to za ta zama haramtacciyar gwamnati a wannan rana.” “Dole ne tattalin arzikin kasar ya tsaya cik, majalisa ta shiga yajin aiki, kotu ta shiga yajin aiki, hukumomi su shiga yajin aikin, ba jami’o’i kadai ba, har da makarantu.” Inji shi. A ranar Juma’a ne Kotun kolin...
    Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gabaci da kuma kudancin kasar Lebanon wanda yak eta yarjeniyar zaman lafiyan da HKI ta cimma da kungiyar Hizbullah mai lamba 1701 ta shekara ta 2006. Tashar talabijin ta Presstv anan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Lebanon na cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan bayan kauyen taraya a gundumar ba’alabak, cikin lardin Ba’alabak Hermel, da kuma kan garin Shaara kusa da garin Jenta a dai dai kasar tsaunuka da ke yankin. A kudancin kasar Lebanon kuma jiragen yakin HKI sun jefa makamai masu linzami har guda 4 a kan yakunan Jibaa da Snaya Kafafen yada labaran HKI sun tabbatar da wannan labarin sun kuma nakalto sojojin kasar suna...
    A ranar Juma’a ce Amurka ta bai wa Jakadan Afirka ta Kudu, Ebrahim Rasool, wa’adin sa’o’i 72 ya tattara komatsai ya fice daga ƙasar. Hakan na ƙunshe cikin wata ’yar taƙaitacciyar sanarwa da mai magana da yawun ma’iakatar harkokin wajen Amurka, Chrispin Phiri ta fitar. Trump ya dakatar da kafar watsa labarai ta VOA Mahaifiyar Sarkin Gwoza ta rasu Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya zargi Ebrahim Rasool da kasancewa “ɗan siyasar wariyar launin fata mai ƙyamar Amurka,” lamarin da ya ƙara rura wutar rikicin diflomasiyya da ya kunno kai tsakanin Washington da Pretoria. A cikin watan Fabarairun da ya gabata ne Shugaba Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social cewa Amurka...
    A wani bangare na daban kuwa, dole ne ’yan siyasar Turai su yi tunani cewa, jama’arsu sun dauki irin wannan mataki ne ba ma kawai bisa bukatunsu na sayayya ba, har ma ya kasance mataki ne na nuna adawa da babakeren Amurka, da bukatunsu na dogaro da kansu a bangaren manyan tsare-tsare. Huldar Amurka da Turai ta wannan fuskar ta yi hannun riga da ainihin ma’anar zumunci, inda lamarin ya yi rauni matuka, kuma tabbas matukar Turai ba ta nemi dogaro da kanta ba, za ta yi asara daga barazana da kalubalen da Amurka take haifarwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    Rahotanni daga kasar Syria na cewa wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta shiga birnin Jableh da ke yankin Latakia na kasar Siriya a karon farko a daren jiya Lahadi, kamar yadda wata majiya ta kasar ta shaida wa Al Mayadeen. Tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya sun  zagaya a unguwannin Jableh, inda suka duba shaguna da gidajen jama’a da aka wawushe da kuma wadanda aka kona. Wannan dai na zuwa ne bayan wani tashin hankali da ya barke a yammacin kasar ta Syria, inda aka ga wasu dauke da makamai masu alaka da ma’aikatar tsaron sabuwar gwamnatin kasar ta Syria da kuma dakarun tsaron cikin gida a cikin faifan bidiyo suna aikata munanan laifukan yaki da suka hada da kisan  fararen...
    Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga. Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta. Kuma akwai turaren kanti kamar...
    Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya. Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan, da kuma lokacin da ya kamata a yi Magana da su, ko kuma lokacin da ya kamata a zare musu takobi.” Dukkanin wadannan bayanan suna cikin al’kur’ani mai girma. Ayatullah Sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron karatun alkur’ani mai girma, a jiya Lahadi da dare, ya yi ishara da cutukan ruhi da su ka addabi bil’adama a wannan  zamanin da...
      Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa har yanzu ana iya biyan kudin kujeran aikin Hajji ta hannun hukumar.   Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta shafin sada zumunta na hukumar.   Ya yi kira ga wadanda har yanzu suke da bukatar zuwa Hajji su tuntubi jami’an hukumar a dukkan kananan hukumomi ashirin da uku na jihar ko su ziyarci hedikwatar hukumar dake kan titin Katsina, a cikin garin Kaduna.   Alhaji Yunusa Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa mutum dubu uku da dari hudu da sittin (3,460) ne suka biya kudin Hajji ta hannun hukumar.   Ya kuma kara da cewa kudin Hajji ya kama naira...
    Helikwaftan farko da aka haɗa a Najeriya ya kusa kammaluwa, kuma shirye-shiryen gwajin tashinsa sun yi nisa. Hukumar NASENI, mai kula da binciken inganta aikin injiniya da kimiyya da ƙere-ƙere ce ta bayyana haka. Ta sanar da wannan nasara ce a yayin wani taron kwararru da ta gudanar a Kaduna ranar Laraba. Manajan Ayyuka a Cibiyar Binciken Kera Jirage na NASENI da ke Kaduna, Injiniya Kareem Aduagba, ya bayyana cewa Ya ci gaba da cewa, “yanzu mun kai matakin ƙarshe kuma nan gaba kaɗan za mu yi gwajin tashin helikwaftan farko ƙirar Najeriya.” Boko Haram ta ƙona wuraren ibada da gidaje a Adamawa NAJERIYA A YAU: Halin da jama’a za su shiga idan Kamfanin Kaduna Electric ya ƙi sauraren ma’aikatansa...
    A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev. Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin. Sannan aka gudanar da taro na farko tsakanin Amurka da Rasha a birnin riyad na kasar Saudiya ba tare da an gayyaci Zelesky ba haka ma, babu wani Jami’in tarayyar Turai da aka gayyata. Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki...
    Ya ce, motocin da aka kwato sun hada da wata farar mota kirar Howo, wacce aka sace daga Riruwai, karamar hukumar Doguwa, Kano, a ranar 17 ga watan Janairu, 2025, aka kuma gano ta a Lokoja, jihar Kogi.   Akwai wata bakar mota kirar Honda Accord 2013, wacce aka sace daga Abuja ranar 18 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a filin jirgin sama na Kano.   Bugu da kari, akwai wata farar mota kirar Mercedes Benz GLK wacce aka sace a hanyar Magwan Kano a ranar 27 ga watan Janairu, 2025, aka gano ta a Hotoro Quarters Kano da wata jar Toyota Corolla LE da aka sace a Abuja a ranar 30 ga Janairu, 2025, aka gano ta...
    Majalisar Wakilai ta sanya Laraba, 26 ga watan Fabrairu, a matsayin ranar da za ta buɗe zauren sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin dokokin haraji. Kakakin Majalisar, Abbas Tajudeen wanda ya bayyana hakan a ranar Talata, ya ce za a gudanar da sauraron ra’ayin jama’ar a zauren majalisar na wucin-gadi. Abba ya sanya hannu kan dokar kafa rundunar tsaro ta Kano Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi Ya bayyana cewa, kwamitin majalisar kan harkokin kuɗi ne zai jagoranci zaman sauraron ra’ayin jama’ar haɗi da wasu ƙusoshin majalisar na wasu kwamitocin. Aminiya ta ruwaito cewa, a makon jiya ne ƙudirin kafa dokokin harajin guda huɗu da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa majalisar suka tsallake karatu na...
    Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi furuci da cewa: Nan da wasu ‘yan makonni za a fara tilastawa Falasdinawa mazauna Gaza fara yin gudun hijira Ministan kudin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Bezalel Smotrich ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana tuntubar Amurka domin tattaunawa kan aiwatar da shirin shugaban Amurka Donald Trump na tsugunar da mazauna Zirin Gaza a wasu kasashe. A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta 12 ta haramtacciyar kasar Isra’ila Smotrich ya furta cewa: Za a fara aikin kwashe mutanen daga Gaza nan da makonni masu zuwa. Smotrich ya ci gaba da cewa: Mazauna Gaza ba za su samu abin da suke nema ba a Gaza nan da shekaru goma zuwa goma...
    Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu idan har Hamas ba ta sako fursunonin yahudawan sahayoniyyar Isra’ila kafin yammacin ranar Asabar ba. A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce, abin da gwamnatin mamayar Isra’ila ta kasa cimmawa ta hanyar wuce gona da iri, ba zai yi nasara ba ta hanyar aiwatar da siyasar makirci da yaudara. Sanarwar ta ce, manyan al’ummar Gaza sun tsaya tsayin daka wajen fuskantar...
    Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu da shirin na shugaban kasar Amurka akan mutanen Gaza. Ministan harkokin wajen Saudiyya Faysal Bin Farhan ya ce, Saudiyya tana da matsaya tabbatacciya da ita ce kin amincewa da duk wani shiri na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza zuwa wata kasa.” Ministan na Saudiyya ya nuna goyon bayansa ga kiran da Iran ta yi na yin taron kungiyar kasashen musulmi domin tattaunawa wannan batu....
    Gwamnatin jihar Kebbi, ta kammala shirye-shiryen gudanar da daurin auren mata dari uku a karshen watan Fabrairun wannan shekara. Da yake zantawa da manema labarai da yammacin Lahadi, shugaban babban kwamitin kuma tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar, Suleiman Muhammad Argungu, ya bayyana cewa, nasarar daurin auren da aka yi a shekarar da ta gabata, wanda gidauniyar NANAS ta uwargidan Gwamnan, Hajiya Nafisa ta shirya, ya sanya gwamnatin ta sami kwarin gwiwar daukar nauyin aurar da wasu rukunin a wannan shekarar. A cewar Shugaban kwamitin, za a aurar da mutane  600  marasa galihu ba tare da la’akari da addini, kabilanci da siyasa ba a tsarin gwamnati. Ya ce, an kafa kwamitocin tantancewa a dukkan kananan hukumomi 21 domin zabar...
    Shugaban Hukumar jin dadin Alhazai ta Nijeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da tsawaita wa’adin biyan kudin kujerar aikin hajjin 2025 zuwa ranar 10 ga Fabrairu, 2025. Karin wa’adin na zuwa ne biyo bayan koke-koke da aka kai wa hukumar na a kara wa maniyyatan da suka gaza kammala biyan kudinsu a kan lokaci. Nijeriya Na Iya Fuskantar Ƙarancin Maniyyata A Hajjin Bana EFCC Ta Gurfanar Da Manajan Darakta Kan Damfarar ₦144m A Gombe Farfesa Usman ne ya bayyana hakan a yayin wani taro da ya gudana a manhajar ‘Zoom’ a ranar Talata 4 ga watan Fabrairu, 2025, tare da masu ruwa da tsaki a shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji. Shugaban Hukumar NAHCON ya yi kira ga Sakatarorin...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
    Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa  kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka. Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu. Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga  Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.  Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20  da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can. A cikin kafafen sadarwa na...
۱