HausaTv:
2025-07-01@17:20:22 GMT

Wargajewar HKI Ba Makawa Inji Wani Janar Daga Sojojin JMI

Published: 1st, July 2025 GMT

Daya daga cikin manya manyan sojojin kasar Iran ya bayyana cewa wargajewar HKI da kuma halakar Firai ministan kasar tabbas ne babu makawa. Ya kuma gargadi makiyan JMI kan cewa duk wani kuskuren da zasu tabka sai ya sanya dukkan sansanoninsu na soje a yankin cikinbabban barazana na lalatasu.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto , Major General Yahya Rahim Safavi yana fadar haka a taron addu’a da kuma girmma marigayi Manji Janar Muhammad Baqiri babban hafsan hafsoshin kasar wanda yayi shahada a ranar Jumma’a 13 ga watan Yunin da ya gabata.

Ya kuma kara da cewa babban shaitan da kuma karamin shaitan duk zasu halaka sun kasa kaiwa ga bukatunsu a yankin kwanaki 12 da suka dorawa JMI. Janar Safawi wanda kuma ya kasance daga cikin masu bawa jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran ya kara da cewa yakin da ya gabata  ya gaggauta halaka da kuma bacewar HKI daga yankin gaban ta tsakiya.

Ya ce, tsagaita wutan da aka amince, dan sararawa ce ga makiya JMI amma su tabbatar da cewa da yardar All…yaki mafi muni yana gabansu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Darakta Janar Na Hukumar IAEA Ya Ce; Babu Tabbas Iran Na Da Shirin Mallakar Makamin Nukiliya

Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran na kera makamin nukiliya ba!

A wata hira da tashar talabijin ta Faransa LCI, Darakta Janar na hukumar kula da makamashin nukiliya ta IAEA Rafael Grossi ya bayyana cewa: Ba zai iya tabbatar da cewa Iran tana kera makamin nukiliya ba.

Grossi dai ya fuskanci tambayoyi da kalubale da dama daga mai gabatar da Shirin, kan ko Iran na daf da kera makamin nukiliya? Ya amsa a cikin halin shakku, yana mai cewa a cikin rahoton ya nisanci zargin Iran da kokwarin kera makamin nukiliya domin babu tabbas kan zargin.

Da aka tambaye shi ko Iran na kera makamin nukiliya? Grossi ya amsa da cewa: “Ba zai iya tabbatar da hakan ba, kuma zai zama rashin gaskiya idan aka ce suna shirin kera makamin nukiliya.”

Da yake amsa tambayar da mai gabatar da shirin ya yi danganr da wasu masu kallon Shirin suna kokwanton ingancin harin da aka kai kan Iran: Grossi ya kare hare-haren wuce gona da irin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka kan cibiyoyin nukiliyar Iran, da ba su kan ka’ida, yana mai cewa akwai yanayi na uku a cikin dabarun kera makamin nukiliya da ake kira “boyayyen shiri” ko “shirin da bai fito fili ba” inda har yanzu Shirin bai kai matakin kera makamin ba, amma ta mallaki dukkan karfin iko da fasahohin da ake bukata, kuma idan lokaci ya yi, za su iya mallaka. Ya kara da cewa Iraniyawa suna da fatawar haramta mallakar makamin nukiliya da sauran makaman kare dangi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Isra’ila na bincike kan harin dakarunta da ya kashe fararen hula a Gaza
  • Laftanar Kanar Shikarci: Sojojin Iran Suna Cikin Shirin Ko-Ta-Kwana Fiye Da Kowane Lokaci
  • Jarumin Matashi Ya Ragargaji  Wani Ɗan Fashi A Kano
  • Lebanon Ta Nuna Damuwarta Da Yiyuwar Yan Ta’adda Daga Siriya Su Kawo Hare-Hare Cikin Kasar
  • Iran Ta Bawo Mayakan Huthi Fasahar Kera Makamai Masu Linzami Daga Cikin Ruwa
  •  Wani Dan Bindiga Dadi Ya Kashe Ma’aikatan Kashe Gobara 2 A Amurka
  • Kalibof Ya Mayarwa Shugaban Kasar Amurka Martani Kan Mummunan Kalamansa
  • Falasdinu: Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Yammacin Kogin Jordan
  • Darakta Janar Na Hukumar IAEA Ya Ce; Babu Tabbas Iran Na Da Shirin Mallakar Makamin Nukiliya