Dukkaninsu sun je ne domin girmama marigayi Dantata tare da halartar jana’izarsa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Barau

এছাড়াও পড়ুন:

An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina

Gwamnatin Saudiyya ta amince a yi jana’iza tare da binne gawar attajirin ɗan kasuwar nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata.

Babban sakataren marigayin, Mustapha Abdullahi Junaid ya ce shirye-shirye sun kammala domin gudanar da jana’iza tare da binne gawar marigayin a garin Madina.

A wani saƙo da Mustapha ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa, “AlhamdulilLah an samu amincewar (hukumomi).

“Za a ɗauki Aminu Alhassan Ɗantata daga Abu Dhabi zuwa Madina. Za a yi jana’iza gobe da safe in sha Allah.”

Aminiya ta ruwaito cewa a safiyar jiya Asabar ce dai attajirin ɗan kasuwar ya rasu a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Amma iyalansa suka jinkirta binne shi domin a cewarsu, suna so ne su cika masa burinsa na binne gawarsa a garin na Madina, birnin Ma’aiki (S.A.W).

An dai gudanar masa da sallar gawa da ba ta kusa wata sallar ga’ib a Jihar Kano, wadda Sheikh Ibrahim Khalil ya jagoranta.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sai bayan Magariba za a yi wa Dantata jana’iza a Madina
  • Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Saudiyya Don Halartar Jana’izar Ɗantata
  • HOTUNA: Yadda Sarki da Gwamnonin Kano da Jigawa suka sauka a Madina domin jana’izar Dantata
  • HOTUNA: Yadda Sarki da Gwamnan Kano suka sauka a Madina domin jana’izar Dantata
  • Yau za a yi Jana’izar Aminu Dantata a Madina
  • Jana’izar Aminu Ɗantata: Abba da Sarki Sanusi sun tafi Saudiyya
  • Gwamna Yusuf Ya Jagoranci Tawagar Kano Zuwa Jana’izar Marigayi Aminu Dantata A Madina
  • An samu amincewar yi wa Dantata jana’iza a Madina
  • HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Aminu Ɗantata a Kano