Majalisar dokokin tsibirin Corsica a yankin Mediterranean, wacce ta kasance jiha ce a kasar Faransa, ta amince da kasar Falasdinunu a matsayin cikakken kasa mai zaman kanta a MDD.

Tsirin dai tana neman samun yanci daga kasar faransa, ta amince da samuwar kasar Falasdinu da kuma yin watsi da HKI a matsayin yar mamaya.

Kissan kiyashi mai ban tsoro wanda HKI take yi a zirin Gaza ya tada hankalin mutane da dama a duniya kuma ya shara fagen amincwa da kasar Falasdinu mai zaman kanta.

Labarin ya kara da cewa Marie-Antoinette Maupertuis shugaban majalisar dokokin kasar ta Corsican ne ya gabatar da bukatar amincewa da kasar Falasdini a majalisar. Ya ce bisa wasu dokokin MDD kasar Falasdinu kasace mai zaman kanta.

Daga baya shugaban majalisar ya bayyana a shafinsa na Intaernet kan cewa tsibirin mai neman yenci daga kasar Faransa ta amince da kasar Falasdinu mai zaman kanta ta kuma yi allawadai da kissan da sojojin yahudawan Isra’ila suke yi a Gaza.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: kasar Falasdinu

এছাড়াও পড়ুন:

Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa

Daga Salihu Tsibiri

Tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana tabarbarewar tsaro da ake fuskanta, wato ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma hare-haren ’yan bindiga, a matsayin barazana ga  siyasar ƙasar nan gabanin zaɓen 2027.

Ya yi wannan tsokacin ne a jawabinsa yayin bude zaman taron musamman na yini biyu da Majalisar Wakilai ta shirya kan halin tsaro da ƙasar ke ciki.

Alhassan Ado Doguwa, wanda ya yaba da ayyukan da hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanarwa, ya ce halin da Arewa ke ciki abin takaici ne ƙwarai, la’akari da yawan mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma waɗanda ke rayuwa cikin tsananin rashin tabbas.

Tsohon shugaban ya jaddada cewa duk da cewa su ma gwamnoni suna da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a tare da gwamnatin tarayya, lokaci ya yi da za a duba batun tsaro a matsayin barazana da ba ta da alaƙa da jam’iyya, addini ko ƙabila.

Ya kara da cewa idan matsalar tsaro ta ci gaba da ta’azzara, akwai bukatar a rufe majalisa gaba ɗaya tare da ayyana dokar ta-baci, har sai an ɗauki matakin gaggawa don kare ƙasar daga halin da take ciki.

A nasa bangaren, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin ’yan sanda, Makki Abubakar Yalleman, ya bayyana tsaro a matsayin alhakin kowa, inda ya yaba wa umarnin shugaban ƙasa na janye ’yan sanda daga wasu manyan mutane domin ƙara ƙarfi a yaki da laifuka a fadin ƙasar.

Sai dai Makki Yalleman ya yi kira da a samar da isasshen kuɗi da na’urorin zamani domin inganta ƙwarin gwiwa da ƙwarewar rundunar ’yan sandan Najeriya a yakin da take yi da ta’addanci, garkuwa da mutane da kuma ’yan bindiga.

A nasa bangaren, shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda, ya danganta matsalolin tsaro da ake fuskanta ga gazawar bangarorin gwamnati uku wajen tabbatar da bin tanade-tanaden kundin tsarin mulki, musamman kan ta’addanci, garkuwa da mutane, ’yan bindiga da kuma masu yi wa gwamnati tawaye.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Zabi JMI A Cikin Majalisar Zartarwan Ta Hukumar Yaki Da Makaman Guba Ta Duniya CWC
  • An Rutsa Da Tsohon shugaban Kasar Najeriya A Guine Bissau Bayan Juyin Mulki
  • Gwamna Radda Ya Sanya Hannu Kan Kasafin 2026 Ya Zama Doka
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yabawa Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Shugaban Majalisar Koli Ta Taron Kasa Iran Ya Yawaba Pakistan Saboda Goyon Bayanta
  • Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru  Isa Chiroma Mafaka Ta Wucin Gagi
  • Abbas Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya
  • Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya