Laftanar Kanar Shikarci: Sojojin Iran Suna Cikin Shirin Ko-Ta-Kwana Fiye Da Kowane Lokaci
Published: 1st, July 2025 GMT
Kakakin sojojin Iran Laftanar kasar Abul-Fadal Shikarci ya sanar da cewa; Sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwana fiye da kowane lokaci a baya, don haka za su mayar da martani mai tsanani akan sabon wuce gona da iri na ‘yan sahayoniya.
Kakakin sojojin na Iran ya kuma ce; Dama ko kadan jamhuriyar musulunci ta Iran ba ta taba amfani da Kalmar ‘dakatar da fada ba” a mastayin zabi.
Haka nan kuma ya ce; ‘Yan sahayoniya ba wadanda za a amince da su ba ne, balle gaskatawa, ba a cikin Iran ba, balle kuma a kowane wuri a duniya.”
Shikarci ya kuma yi ishara da cewa; sojojin kasar suna cikin Shirin ko-ta-kwan fiye da kowane lokaci a baya, don haka duk wani sabon hari na wuce gona da iri daga ‘yan sahayoniya zai fuskanci mayar da martani mai tsanani.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fararen hulan Isra’ila sun kai wa sojojin ƙasarsu hari
Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da wani hari da fararen hula’yan ’yan ƙasar suka kai wa sojojinta.
An kai wa dakarun rundunar sojojin ko-ta-kwana na Isra’ila hari ne a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan.
Yahudawa ’yan share wuri zauna suka kai wa sojojin na Isra’ila harin ne a yayin da sojojin ke aiwatar da wani samamen tare da yin kame a yankin, mai suna Kafr Malek.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, “fararen hula ’yan Isra’ila sun yi wa jami’an ruwan duwatsu tare da cin zarafin sojojin ta jiki da ta baki, ciki har da kwamandan rundunar.”
Yunwa ta kashe yara 66 a Gaza ‘An kashe ’ya’yana da mijina da ’yan uwana a hanyar ɗaurin auren ɗana’ Yadda aka yi jana’izar kwamandojin Iran da Isra’ila ta kasheTa kara da cewa fararen hular sun yi ɓarna tare da lalata motocin sojoji, har ma sun yi yunkurin bige jami’an tsaro.
Rundunar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a yayin da fararen hula’yan Isra’ila ke tuƙi zuwa wani wuri da aka ayyana a matsayin wurin da sojoji suka kulle.
Sanarwar ta ce jami’an tsaro sun tarwatsa taron, kuma an kama mutum shida tare da mika su ga ’yan sandan Isra’ila don ci gaba da bincike.